Me ya sa Taliban ta hana mata karatun aikin jinya da ungozoma?

Asalin hoton, Handout
- Marubuci, Flora Drury and Turpekai Gharanai
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
- Lokacin karatu: Minti 3
Mata da ke karatun ungozoma da aikin jinya a Afghanistan sun shaida wa BBC cewa an faɗa musu cewa kar su zo makaranta washegari - wanda ke nufin an rufe hanya ɗaya tilo da ta rage musu na ƙaro karatu a ƙasar.
Aƙalla makarantu biyar a faɗin Afghanistan ne suka tabbatar wa BBC cewa Taliban ta buƙaci su rufe makarantu har sai mama ta gani, sannan an yaɗa wasu bidiyoyi a kafafen sadarwa da ke nuna ɗalibai suna kuka a lokacin da suka samu labarin.
Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoton, BBC ba ta tabbatar da sahihancin labarin ba daga ma'aikatar lafiya ta gwamnatin Taliban.
Sai dai rufe makarantun koyon aikin ungozoman na cikin tsare-tsaren ƙungiyar na hana karatun mata, domin tun a bayan sun hana mata ƙanana zuwa sakandire da manyan makarantu tun daga Agustan 2021.
Ƙungiyar ta yi alƙawarin cewa za su ba matan dama su dawo makaranta da zarar sun shawo kan wasu matsaloli - ciki har da tabbatar da cewa jadawalin karatuttukan sun dace da "Musulunci.".
Sai dai har yanzu babu wani sauyi.
Dama hanya ɗaya da ta rage wa matan na ƙaro karatu ita ce zuwa kwalejin koyon aikin jinya da ungozoma.
Ungozoma da aikin jinya na cikin ayyukan da gwamnatin na Taliban ta ba mata dama su yi, saboda ba su amince maza su kula da mata ba, sai dai idan akwai muharraminta a kusa.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Kimanin wata uku da suka gabata, BBC ta samu shiga cikin wata makarantar koyon aikin ungozoma da ke ƙarƙashin gwamnatin Taliban, inda ta ga gomman mata da suke tsakanin shekaru 20 suna koyon karɓar haihuwa.
Matan sun kasance cikin farin cikin samun damar zuwa makaranta.
"Ƴangidanmu suna alfahari da ni," in ji wata mai suna Safia. "Na bar yarana a gida ne domin in zo nan, amma sun san ina bauta wa ƙasata ne."
Amma tun a wancan lokacin, wasu matan sun bayyana fargabar za a zo lokacin da za a hana su.
Yanzu babu tabbacin yaya makomai waɗannan matan - waɗanda aka ƙiyasta sun kai kusan 17,000 zai kasance.
Babu wata sanarwa a hukumance game da hanin, amma wasu majiyoyi daga ma'aikatar lafiyar ƙasar sun tabbatar wa BBC.
A wasu faya-fayan bidiyo da aka tura wa BBC, an ga wasu daga cikin ɗaliban suna kuka.
"Tsayawa a nan muna kuka ba zai amfane mu da komai ba," in ji wata ɗaliba a cikin wani bidiyo. "Jami'an gwamnati masu tabbatar da dokar Taliban na kusa, kuma ba na so wani abu ya same mu."
Wasu faya-fayan bidiyon da BBC ta gani akwai wasu matan suna nuna rashin jin daɗinsu - suna waƙa a lokacin da suke barin makarantar.
Wata ɗaliba a Kabul ta ce an faɗa mata ta jira har "sai mama ta gani."
"Duk da cewa mun zo ƙarshen zangon karatunmu, amma ba mu fara jarabawa ba," in ji ta a zantawarta da BBC.
Wata ɗaliba ta ce, "kawai cewa aka yi mu kwashe jakunkunanmu mu fice daga ajujuwanmu."
"Sun kuma faɗa mana cewa kar mu tsaya a harabar makarantar domin ƴan Taliban za su iya shigowa a kowane lokaci, kuma komai zai iya faruwa. Lamarin ya jefa kowa cikin tsoro," in ji ta.
"A wajen wasu daga cikinmu, zuwa makaranta ya buɗe mana wani sabon babi a rayuwa bayan wani dogon lokaci ba tare da aikin yi ba, ga damuwa da zaman kaɗaici a gida."
Yanzu ana sauraron ganin abin da wannan matakin ke nufi: a bara, Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce Afghanistan na buƙatar ƙarin unguzoma 18,000.
Afghanistan na cikin ƙasashen da ake yawan samun mace-macen mata wajen haihuwa a bara, kamar yadda hukumar lafiya ta duniya WHO ta bayyana, inda wani rahoton bara ya nuna cewa aƙalla mata 620 ne suke mutuwa a cikin haihuwa 100,000.











