Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Abubuwan da kuke son sani kan wasan Liverpool da Chelse a Premier
Liverpool za ta karɓi bakuncin Chelsea a wasan mako na 36 a Premier League ranar Asabar a Anfield.
A wasan farko ranar 4 ga watan Oktoba da aka buga a Stamford Bridge, Chelsea ta yi nasara a kan Liverpool da cin 2-1.
A karawar Chelsea mai masauƙin baki ce ta fara cin ƙwallo ta hannun Moise Caicedo a minti na 14 da take leda daga baya Cody Gakpo ya farke wa Liverpool, sai dai daf a tashi Chelsea ta kara na biyu ta hannu Estevao.
Liverpool za ta ɗauki wasan nan da muhimmaci ganin tana mataki na huɗun teburi daga wasa 35 da cin 17 da canjaras bakwai da rashin nasara 11 da maki 58.
Kenan ƙungiyar Anfield na fatan kammala kakar nan cikin ƴan biyar ɗin farko, domin samun tikitin shiga Champions League a kakar baɗi.
Da yake Liverpool ce mai rike da kofin bara, amma ta ci karo da koma baya dun da kashe makudan kuɗi da ta sayo ƴan wasa kan fara kakar nan, kenan zuwa gasar zakarun Turai a baɗi nasara ce ga koci, Arna Slot.
Chelsea kuwa, wadda ke fuskantar matsaloli a kakar nan tana matsayi na tara daga karawa 35 da yin nasara 13 da canjaras tara aka doke ta 13 da maki 48.
Tun farko Chelsea ta sa ran samun gurbin shiga gasar zakarun Turai, sai kawai ta yi wasa shida a jere ba rae da yin nasara ba da cin ƙwallo ɗaya tal.
Haka kuma ƙungiyar Stamford Bridge ta fada ruɗani da ta kai ta kori koci, Enzo Maresca a bana ta maye gurbinshi da Liam Rosenior, shima kuma ta kore shi.
Yanzu Chelsea tana amfani da Calum McFarlane kociyan matasan ƙungiyar a matakin riƙon kwarya zuwa karshen kakar nan.
Bayanai kan Liverpool
Liverpool ta yi rashin nasara a wasa biyu a baya bayan nan da Chelsea a Premier League, adadin wanda ta sha kashi a wasa 20 da suka gabata (Nasara takwas da canjaras10). Karon karshe da ta yi rashin nasara uku a jere a hannun Chelsea shi ne tsakanin Disamba 2013 zuwa Nuwamba 2014.
Liverpool ta yi rashin nasara a wasa 11 a Premier League a wannan kakar — mafi yawa tun 2014-15 a karkashin Brendan Rodgers lokacin da aka doke ta 12. Jimilla kuma ta sha kashi 18 a dukkan fafatawa, kuma da ta fi yin rashin nasara ita ce a 2009-10 (rashin nasara 19).
Ana cin Liverpool ƙwallo biyu ko fiye da haka a wasa 16 daban-daban a Premier League a wannan kakar — ta taɓa yin wannan rashin ƙwazon a 2012-13 (wasa 17).
Babu wani ɗan wasan Liverpool da ya fi Dominik Szoboszlai yawan hannu a cin ƙwallaye a wannan kakar (Ya ci 13 ya bayar da 10 aka zura a raga). Shi ne ɗan wasan tsakiya na farko a Liverpool da wannan bajintar tun bayan Steven Gerrard a 2013-14 (Ya ci ƙwallo 14 ya bayar da 14 aka zura a raga)
Bayanai kan Chelsea
Bayan nasarar 2-1 a Stamford Bridge a watan Oktoba, Chelsea na fatan doke Liverpool gida da waje a kakar Premier League ɗaya a karon farko tun bayan 2013-14.
Chelsea ta yi nasara ɗaya daga wasa 10 a bayan nan a gidan Liverpool a Premier League (Ta yi canjaras biyar da rashin nasara huɗu), nasarar ita ce 1-0 a Maris 2021 a karkashin Thomas Tuchel.
Chelsea ta yi rashin nasara a wasa shida a jere a Premier League — sau ɗaya kacal a tarihin ta, wadda ta taba yin rashin nasara bakwai a jere a 1952.
Chelsea kan bari ƙwallo na shiga ragarta a duk wasanninta 13 a karshen wasannin Premier League, inda aka zura mata uku a wasa huɗu daga cikin biyar na karshe. Karon karshe da ta yi wasa da yawa ba tare da an zura mata ƙwallo a raga ba shi ne tsakanin Maris zuwa Agusta 1991 (Fafatawa17).
Matashin ɗan wasan mai shekaru 19, Estêvão Willian ya ci ƙwallon a wasansa na farko a Chelsea da Liverpool a watan Oktoba. Ɗan wasa matashi da ya ci Liverpool gida da waje shi ne Romelu Lukaku a 2012-13.
João Pedro shi ne kan gaba a cin ƙwallaye a Chelsea a Premier League a kakar nan mai 15 da kuma guda 20 a raga a dukkan fafatawa.