Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Abin da ya kamata ku sani kan kayan abinci da aka sauya wa halitta
- Marubuci, Olaronke Alo & Chiamaka Enendu
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Global Disinformation Unit
- Lokacin karatu: Minti 5
Ana ci gaba da tafka muhawara a kafafen sada zumunta kan amfani da irin da aka inganta halittarsa a Najeriya, bayan bidiyon da wani mai jan ra'ayin mutane a fannin lafiya ya yi da ya karaɗe shafukan.
Miliyoyin mutane ne suka kalli bidiyon da ke da tsawon minti 14, wasu dubbai kuma suka tofa albarkacin bakinsu, wanda wani likita mai suna Dakta Chinonso Egemba ya wallafa a shafinsa ya na bayanin kimiyyar da aka yi amfani da ita wajen inganta irin, da kuma batutuwa da suka jiɓance shi.
Martanin da jama'a suka yi ta yi ya nuna cewa har yanzu batun na janyo mabanbantan ra'ayoyi a Najeriya , kuma labaran da ba na gaskiya ba kan tasirin da abinci daga irin da aka inganta ke yi kan lafiya na ci gaba da karaɗe shafukan.
Da ya ke mayar da martani bayan sukar da ya sha kan bidiyon, dakta Egemba ya shaidawa BBC cewa ya ce yana ganin mabanbantan ra'ayoyin da aka samu ba ya rasa nasaba da shati faɗin da aka daɗe ana yaɗawa.
Wasu da dama sun zarge shi da cewa an biya shi ne domin tallata abincin da aka samar daga irin da aka inganta ko kuma a bayan fage ya na yi wa wasu ƴan ƙasashen waje aiki ne, ciki har da Bill Gates, zarge-zarge da Egemba ya musanta.
'' Mutane sun daɗe da yin tunanin cewa ina yi wa Bill Gates aiki a sirrance'' in ji sa. '' To a gaskiya, ni ba na aiki da wani kamfanin samar da irin da aka inganta. Ilmantar da mutane kawai nake yi a shafina, kuma zan ci gaba da aikin ilmantar da ƴan Najeriya.''
Mene ne irin da aka inganta?
A shekarar 2016, Najeriya ta amince da soma sayar da amfanin gona da aka samu daga irin da aka inganta karo na farko wato BT Cotton. Daga baya aka amince da wasu kamar PBR Cowpea da TELA Maize domin maganace matsalar ƙarancin abinci. Amma a faɗin duniya, an soma amfani da su tun shekarun 1990.
An bayyana tsarin samar da tsirrai ta hanyar inganta su da sauya halittunsu ta hanyar da sauyin ba zai yiwu ba hakanan - ana yin hakan ne ta hanyar haɗa aure inda ake ɗauko irin wani tsiro a gwama shi da wani.
Ana haka ne domin taimakawa manoma samar da shuka da ke iya jurewa abubuwa kamar cutuka da fari fiye da waɗanda ba a inganta ba.
Masu binciken kimiyya na nemo ƙwayoyin haliitar da ke da wata ɗabi'ar da ake buƙata - kamar iya jurewa fari- sai su kwaikwayi kwayar halittar su sanya ta cikin wata.
Dalilan da ya sa Najeriya ke shuka irin da aka inganta
Najeriya ta amince da sayarwa da kuma cin amfanin gona da aka samar daga irin da aka inganta kamar masara da wake, saboda rage matsalar ƙwari masu cinye amfanin gona da kuma kawo ƙarshen matsalar ƙarancin abinci wanda ke da nasaba da yanayi mara kyau, in ji Dakta Yemisi Asagbra, darakta janar na hukumar samar da tsirrai ta hanyar inganta halittunsu na Najeriya.
Dokar hukumar ta ce wajibi ne a rubuta a jikin amfanin gona cewa an samar dashi ne daga irin da aka inganta domin bai wa mutane damar zaɓi.
Hukumomin lafiya, ciki har da hukumar lafiya ta duniya WHO ta ce binciken baya bayan nan ya nuna cewa babu wata shaida da ke nuna abincin da aka samar daga irin da aka inganta ba su da wata barazana ga lafiyar alumma.''
Sai dai har yanzu akwai kokwanto da rashin tabbas kan fasahar da aka yi amfani da ita wajen inganta irin, wanda ya kai ga har mutane na yada labarai marasa tushe game da hakan.
Masu janyo ra'ayoyin alumma a shafukan sada zumunta a Najeriya na yaɗa labarai da ke yaudarar mutane kan amincin cin abincin da aka inganta su, ciki har da ikirarin cewa suna janyo cutar daji.
A cewar cibiyar bincike kan cutar daji ta Birtaniya, babu wata shaida da ke nuna cin abincin da aka inganta na janyo cutar daji.
A gefe guda kuma, wani tsohon bidiyo da ake yaɗa wa akai-akai a shafukan X da Whatsapp a Najeriya na nuna yadda shugaban Rasha Vladimir Putin ya haramta abincin da aka inganta kuma ya ayyana duk wanda ke shuka shi a matsayin ''ɗan ta'adda".
Akawai dokoki masu ƙarfi da ke taƙaita yadda ake amfani da fasahar inganta iri da kuma shuka shi a Rasha, sai dai ba a haramta su ba. Misali, ƙasar ta amince da yin shuka da irin da aka inganta domin yin binciken kimiyya.
Bidiyo ya kuma nuna cewa cin abincin da aka samar daga irin da aka inganta na iya lalata ƙwayar halittar ɗan Adam (DNA).
'' Daga dukkanin binciken da na yi, ba bu shaidar cewa GMO na sauya DNA na mutumin da ya ci,'' a cewar Dakta Olumide Adebesin malami a jam'iar Legas da ke koyar da ilimin ƙwayar hallitar ɗan Adam da gado.
Ita ma Farfesa Cathie Martin, wata mai bincike kan shuka da kwayoyin halitta a Birtaniya, ta musanta cewa irin da aka inganta yana hana waɗanda ba a inganta ba tsirowa. " Ban taba ganin haka ba, a matsayina na manomiya, na shuga irin da aka inganta da kuma waɗanda ba a ingatanta ba a ƙasar noma ɗaya.''
A Bill Gates agenda?
Muhawarar da ake yi a kan intanet ya kuma mayar da hankali kan tasirin amfani da irin da aka inganta ke yi kan noma, da kuma ikirarin cewa ana tilastawa manoma amfani da irin, wanda ke ƙara fargabar da ake yi kan ce hukumomi za su kakaba musu irin.
Ajisefinni Ayodeji, wani ƙaramin manomi ne kuma shugaban ƙungiyar manoma ta jihar Kwara, ya ce manoma na fargabar cewa yin amfani da irin zai rage wa Najeriya dogaro da kai a fannin abinci da kuma danne manona.
Ya ce yana ƙasashen wajen ne ke tilasta musu amfani da irin da aka inganta kuma baya ganin ma'aikatan noma na da kwarewar da ake buƙata domin amfani da irin da aka inganta yadda ya kamata.
Wasu na ikirarin cewa sanya abinci daga irin da aka inganta cikin tsarin abincin na Najeriya, na daga cikin wani shiri da kamfanonin ƙasashen duniya ke yi musamman ma Bill Gates, wani ɗan kasuwa da ke Amurka, domin ƙwace ragamar fannin noma a ƙasar.
Gidauniyar Bill and Melinda Gates ta tallafa wajen yin bincike a fannin noma a Najeiya, ciki har da samar da irin da aka inganta wato TELA Maize wanda aka ƙirƙira kuma aka samar a cibiyar bincike kan noma na jam'iar Ahmadu Bello da ke Zaria.
Kabir Ibrahim, shugaban kungiyar manoma ta Najeriya (AFAN), ya goyi bayan amfani da irin da aka inganta, inda ya ce yawancin bayanai da ke tayar da hankali bayanai ne da aka samu daga labarai na ƙarya da ake yaɗawa.
Ya kuma ce babu wani manomi da ake tilastawa shuka irin da aka inganta.
Mista Ibrahim ya kuma ce kamfanonin cikin gida na raba irin da aka inganta, ya na musanta zargin cewa kamfanonin ƙasashen waje ne kawai ke raba wa, ya ce su a yanzu ma ƙari suke so.
Duk da ce-ce-ku-cen, Dakta Egemba ya ce ya ji daɗin yadda bidiyon ya tayar da muhawara ya kuma taimakawa mutane samun ilimin da zai taimaka musu ɗaukar matakin da ya dace.