Sarkin da ya yi minti 20 a kan mulki da firaministan da ya yi awa ɗaya

Ajiye aiki da Firaministar Birtaniya Liz Truss ta yi na nufin cewa ƙasar ta yi firaministoci har ɓiyar cikin shekara shida. Tabbas hakan zai iya zama wani tarihi da ƙasar ta kafa a ɗuniya.

Al'ummar ƙasar Argentina ma za su iya tuna irin haka lokacin da suka taɓa samun shugabanni biyar cikin mako ɓiyu.

Murabus din da Liz Truss ta yi bayan zama firaminista ta tsawon kwana 45 - shi ne irinsa na farko a tarihin siyasar Birtaniya, idan kuma aka kwatanta hakan da sauran shugabanni a duniya da suka shafe lokaci kankani a mulki.

Shugaban gwamnatin 'yan Nazi na dare ɗaya

Za a ci gaba da tuna Joseph Goebbels a matsayin ministan farfaganda na ƙasar Jamus lokacin mulkin 'yan Nazi a shekarun 1933-1945. Sai dai mutane kalilan ne suka san cewa ya taɓa rike muƙamin shugaban gwamnati - amma na kwana ɗaya.

Hakan ya faru ne a ranar 30 ga watan Afrilun 1945, lokacin da Adolf Hitler ya kashe kansa a wani gida na karkashin ƙasa a birnin Berlin a kwanakin karshe na ƴakin ɗuniya na ɓiyu a Turai.

A matsayinsa na babban mai muƙami na biyu bayan Adolf Hitler, Goebells ya zama shugaba, sai dai shi da matarsa sun kashe kansu bayan ciyar da 'ya'yansu shida guba.

Wata ɗaya a faɗar White House

William Henry Harrison ya kasance shugaban Amurka na farko da ya mutu kan karagar mulki a shekarun 1773-1841 wanda kuma ya yi mulki a cikin kankanin lokaci.

Tsohon jami'in na soja ya kwanta rashin lafiya sakamakon kamuwa da cutar sanyin hakarkari - wato Pneumonia - kwanaki 32 da hawansa mulki, inda ya gamu da ajalinsa yana da shekara 68.

Samun shugabanni biyar cikin mako ɓiyu a Argentina

Argentina ta shiga wani rudani a watan Disamban 2001, inda ta shiga rikici na komaɗar tattalin arzikin da ya janyo gagarumar zanga-zanga kan tituna a fadin ƙasar wanda kuma ya haddasa mutuwar mutum 25.

Rikicin na siyasa ya sanya shugaba Fernando de La Rua yin muraɓus a ranar 20 ga watan Disamba.

Abin da ya biyo baya shi ne taɓarɓarewar harkokin siyasa, inda shugaban masu rinjaye na majalisar dattawa, Ramon Puerta, ya maye gurbin De La Rua a matsayin shugaban ƙasa duk da cewa kujerar mataimakin shugaban kasa ma babu wanda yake kanta saboda murabus din da ya yi.

Kwana biyu da faruwar hakan, Puerta ya ɓar kujerar bayan da majalisa ta zaɓi Adolfo Rodriguez Saa domin zama shugaba.

Sai dai, shi ma Saa ya ajiye muƙamin bayan mako ɗaya ɓayan da shirinsa na farfado da tattalin arziki ya gamu da tasgaro.

A hukuncin doƙa ya ƙamata Puerta ya dawo mulki, amma sai yaki hakan, inda ya yi muraɓus a matsayinsa na shugaban majalisar dattawa.

Daga ɓisani, jagoran mataimaka na majalisar, Eduardo Camano, ya zama shugaban kasa. Sai dai, kwana uku da hawansa mulki, sai ya yi muraɓus domin bai wa wani sabon shugaba Eduardo Duhalde da aka zaɓa wuri wanda ya yi mulki har zuwa lokacin da aka gudanar da zabukan 2003.

Firaministan Indiya na mako biyu

Tsohon firaministan Indiya, Atal Behari Vajpayee, shi ne yake rike da tarihi a matsayin shugaban da ya yi mako biyu kacal a mulki a shekarar 1996, bayan kasa samun rinjayen kuri'u na hadaka da majalisa ta kada.

Ya koma kan mulki a 1998, sai dai, watanni 13 kadai ya yi kafin a samu wata hadaka da kuma ta sanya aka soke majalisa.

Sai dai, jam'iyyarsa ta BJP ta sake samun gagarumin nasara a zabukan da aka gudanar, inda ya sake komawa mulki karo na a uku a 1999 zuwa 2004.

Tarihin mace ta farko da ta zama shugabar Saliyo

Siaka Stevens ya kasance minista da ya shafe kankantan lokaci da kuma shugaban da ya fi dadewa kan karagar mulki a tarihin ƙasar Saliyo.

An zabe shi a shekarun 1967, inda sojoji suka hambarar da kuma kama shi a wani juyin mulki da suka yi a ranar da aka rantsar da shi.

Sai dai, Stevens ya sake komawa kan mulki shekara daya bayan hambarar da shi, inda ya yi mulki daga 1971 zuwa 1985, bayan da aka kawo karshen mulkin soji.

Gwamnatinsa ta gamu da zarge-zargen take hakkin dan adam da kuma magudin zabe.

Daga baya, Ivy Matsepe-Casaburri, ta zama sauwar shugaba a ranar 24 ga watan Satumban 2008, inda ta kasance mace ta farko da ta zama shugabar kasar biyo bayan murabus din shugaba mai ci, Thabo Mbeki. Lokacin tana rike da muƙamin ministar sadarwa.

Wa'adin mulkinta ya kawo karshe bayan awanni 15, sai dai, majalisar dokokin Afirka ta Kudu ta zabi wata minista Kgalema Motlanthe domin maye gurbinta.

Shugabannin rikon ƙwarya a ƙasashen Mexico da Brazil

Alal misali idan aka kwatanta da ƙasar Argentina, yankin Latin Amurka ma ya kasance yanki da ke da shugabanni masu karancin lokaci kan mulki, inda Pedro Lascurain, ya kasance shugaba na kasa da awa daya lokacin da aka yi wani juyin mulki da cire shugaba mai ci Francisco Madero a watan Febrairun 1913.

A ƙasar Brazil ma, kakakin majalisar Carlos Luz ya karbi ragamar shugabanci a ranar 8 ga watan Nuwamban 1955, bayan da shugaba mai ci Cafe Filho ya kwanta rashin lafiya. A lokacin, Brazil ta riga da ta zaɓi sabon shugaba Juscelino Kubitschek, amma an tsara sai watan Janairun 1956 zai fara mulki.

Kwanaki uku bayan hakan, Luz ya sauka daga mulki bayan samun umurni daga ma'aikatar tsaro, wadanda suka ce shugaban na riƙo na shirin yin juyin mulki domin hana ranstar da Kubitschek.

Daga bisani, shugaban majalisar dattawa, Nereu ramos ya rike matsayin na tsawon watanni ɓiyu.

Mulkin Sarakuna

Ba a san Sarakuna da fada kan siyasa a zamanin yau kuma suna cikin kwanciyar hankali kan sauye-sauye na mulki, sai dai, hakan baya nufin cewa wa'adinsu ba zai iya jima wa.

Sarki Umberto II na Italiya ya gaji mahaifinsa Vittorio Emmanuelle, bayan ajiye sarauta da ya yi.

Wani abin takaici ga Sarkin, a wani kuri'a daga gudanar, kashi 54 na 'yan Italiya sun zabi wani mulki, inda wa'adinsa ya zo karshe bayan kwana 34.

A ranar 1 ga watan Yunin 2001, yarima mai jiran gado na lokacin ya harbe mahaifinsa da 'yan uwansa na gidan sarautar Nepal.

Bayan haka, Dipendra ya yi yunkurin kashe kansa, amma ya kasa, inda ya fadi sume. Bayan kwana uku sai rai ya yi halinsa.