Florida: Mahukunta sun gargadi al`umma kan guguwar Idalia

An gargadi mazauna hanyar da guguwar Idalia za ta bi su tashi daga yankunan cikin gaggawa, yayin da guguwar ta tunkaro jihar Florida ta kasar Amurka.

An yi hasashen cewa za ta afkawa gabar tekun Gulf a matsayin guguwar da iska mai karfi take tafiyar kilomita 201 cikin sa`a guda da safiyar Laraba.

Cibiyar Kula da Guguwa ta Kasa (NHC) ta yi gargadin cewa Idalia na barazanar haifar da yanayin da zai cutar da al`umma da kuma illata muhalli.

Gabar bakin teku na iya fuskantar ambaliya saboda karfin guguwar.

Shugaban Hukumar Agajin gaggawa Deanne Criswell, ya bayyana cewar "mutane kalilan ne za su tsira daga hanyar da iskar za ta bi, wannan guguwa za ta yi muni idan ba mu dauke ta da muhimmanci ba''.

Gwamnan Florida Ron DeSantis, ya ce ana hasashen Idalia za ta afkawa gabar teku a Big Bend, yankin da bai taba fuskantar irin wannan guguwa ba tun a shekarun 1800.

Cibiyar Kula da Guguwa ta kasa watau NHC ta ce tun shekara tun 0851 yankin Apalacjie Bay bai sake fuskantar iska mai karfin Idalia ba.

Wani rahoto da cibiyar ta fitar ya bayyana cewar "Guguwar ta zo da salon da ba a taba ganin irinsa ba a jihar''.

Karfin guguwar ya haifar da tsawa a yankunan kudu maso yammacin Florida da suka hada da Golden Gate da Naples da kuma tsibirin Marco.

Larduna 25 cikin 67 na Florida sun fara yin kaura don komawa sabon matsuguni.

Mista DeSantis, ya bukaci mutane su gaggauta bin umarnin tashi da aka ba su domin lokaci ya na kurewa.

"Ba kwa bukatar yin tafiyar mil dari biyu don tsira, maimakon haka ku hau kan tudu''.

Yankin Tampa na Florida ya kasance mai yawan jama'a, kuma an samar da shi saboda irin wannan yanayi na tsira da rai, tuni aka rufe filin jirgin saman Tampa a ranar Talata, ana sa ran zai ci gaba da zama a rufe har sai ranar Alhamis.

Chanel Jay, wacce ta fuskanci guguwa har sau biyu ta shaida wa BBC cewar ba za ta yi ganganci da rayuwarta ba.

Itama Mary Walcott Martino, mai shekaru 79 ta shaida wa kamfanin dillanci labarai na Reuters cewar ta gama kammala tattara kayanta za ta tsere.

Gwamnatin jihar ta bude cibiyoyin tsugunar da mutane na wucin gadi bakwai a Tampa Bay.