Abu 5 da suka hana zango na biyu na yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza fara aiki

Asalin hoton, AFP via Getty Images
- Marubuci, By Muhannad Tutunji
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News Arabic
- Aiko rahoto daga, Jerusalem
- Lokacin karatu: Minti 5
Isra'ila da Hamas sun amince da fara ɗabbaƙa yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza da Amurka ta shirya, wanda aka yi tunanin hakan ne zai kawo ƙarshen yaƙin da ya addabi Zirin Gaza.
Kimanin wata biyu bayan shiga yarjejeniyar, har yanzu dai babu wani cigaba da aka samu.
A tsare-tsaren sabuwar yarjejeniyar, wadda Shugaban Amurka Donald Trump ya jagoranta, da Isra'ila da Hamas duk suna tsaka mai wuya.
Daga ciki akwai buƙatar Hamas ta miƙa makamanta, sannan Isra'ila za ta janye dakarunta daga Gaza, ta miƙa tsaron zirin a hannun dakarun ƙasashen duniya da za a haɗa.
Haka kuma batun mulkin Gaza na cikin abubuwan da suke kawo tsaiko a yunƙurin da ake yi na tabbatar da tsaro, da ma neman mutum na ƙarshe daga cikin Isra'ilawa da aka sace da ra yage ba a gani ba, Ran Gvili.
Ina ɗansanda Ran yake a yanzu?

Asalin hoton, Handout
Gvili, wanda ɗansandan Isra'ila ne da ya shiga hannu a lokacin da Hamas ta kai hari a ranar 7 ga Oktoba. Hamas ta ce ta yi ƙoƙarin nemasa a cikin baraguzan Gaza, amma ba ta samu nasarar ganinsa ba.
Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya nanata cewa dole Hamas ta sako dukkan waɗanda ta yi garkuwa da su - matattu da rayayyau - kafin a ɗabbaƙa yarjejeniyar.
A bara an shaida wa iyayen Gvili, Talik da Itzik cewa ɗansu ya mutu.

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
"Sun sace mana," in ji mahaifiyarsa, Talik a zantawarta da BBC. "Sun san inda suka ɓoye shi," in ji mahaifinsa Itzik.
"Kawai suna ƙoƙarin ɓoye shi ne domin su yi wasa da hankalinmu."
Sun ce sun yi amannar Hamas na ƙoƙarin ajiye ɗansu ne domin amfani da shi a nan gaba domin neman abun.
Sai dai Hamas ta shaida wa BBC cewa zargin ƙanzon kurege ne kawai, kuma Isra'ila na neman hanyoyin hana ruwa gudu ne game da tabbatar da yarjejeniyar tsagaita wutar.
Amma dai Amurka ta dage wajen an fara amfani da zagaye na biyu na yarjejeniyar, kamar yadda jaridun Haaretz da The Times of Israel suka ruwaito.
A tattaunawarsa ta BBC Arabic Gershon Baskin, tsohon mai shiga tsakani wajen ceto waɗanda aka yi garkuwa da su, musamman wajen karɓo sojan Isra'ila Gilad Shalit a 2011, ya ce, "Isra'ila ba su da zaɓi masu yawa," wajen hana daɓɓaka zagaye na biyu na yarjejeniyar.
Ya ƙara da cewa Trump ya riga ya yanke shawarar abin da yake so, kuma "zai matsa wa Netanyahu cewa babu lokacin ɓatawa."
Karɓe makaman Hamas
Daga cikin manyan abubuwan da suke gaba-gaba wajen kawo tsaiko ga yarjejeniyar akwai batun karɓe makaman Hamas.
Turkiyya dai ta dage domin shiga cikin ƙasashen duniya da za su kasance a tsakani da ake kira International Stabilisation Force wato ISF, wadda ita ce haɗakar ƙasashen da za su yi aikin karɓe makaman, kamar yadda jaridar Hayon da ake bugawa da harshen Hebrew a Isra'ila ta bayyana.
Netanyahu kuma ya nace ba za ta saɓu ba, kuma yana samun goyon bayan Amurka, kamar yadda jaridar ta bayyana a makon jiya.
Zuwa yanzu dai babu wata ƙasa da fito fili ƙarara ta bayyana aniyarta na shiga cikin haɗakar ƙasashen ISF.
Wataƙila Hamas ta amince da "jingine makamai," da kuma wataƙila miƙa su ga gwamnatin Falasɗinu, amma da wahala ta amince ta miƙa makamanta ga Isra'ila ko Amurka, in ji Gershon Baskin.
Ina dakarun Isra'ila za su koma?
Yanzu haka Isra'ila ce ke da iko da kusan kashi 53 na zirin Gaza.
A ƙarƙashin zango na farko na yarjejeniyar, Isra'ila ta amince ta janye sojojinta su koma bakin iyaka a yankin arewa da kudu da gabashin Gaza, inda ake kiran layin da aka shata da "Yellow Line."

A zagaye na biyu na yarjejeniyar dole a samu fahimtar juna kan ina za a shata layi, sannan akwai batun miƙa makamai da sake gina Gaza da ƙasashen da za su sa ido domin tabbatar da yarjejeniyar.
"Hamas ba ta so ƙarfin ya ƙare, ita kuma Isra'ila tana so ta ci gaba da kasancewa a Gaza saboda wasu dalilai na siyasa," in ji Janar Israel Ziv, tsohon hafsan sojan Isra'ila a zantawarsa da BBC.
Janar Ziv ya ce Trump ne kaɗai zai tursasa ɓangarorin biyu su amince da sharuɗan da aka gindaya domin fara amfani da yarjejeniyar ta biyu.
Mulkin Gaza bayan Hamas

Asalin hoton, AFP via Getty Images
Wani ƙalubalen shi ne yadda za a mulki Zirin Gaza bayan daɗewa a ƙarƙashin mulkin Hamas.
Duk da cewa a daftarin, an ce za a fitar da gwamnatin riƙon ƙwarya - wadda babu hannun Hamas da gwamnatin Falasɗinu a ciki - Isra'ila ta yi zargin cewa zai yi wahalar gaske ba a samu wakilan ɓangarorin biyu ba.
Wannan ya sa Isra'ila take fargabar cewa Hamas za ta ci gaba da samun ƙarfin iko a sabuwar gwamnatin, ko kuma Gaza ta sake komawa hannun gwamnatn Falasɗinu.
Ganawar Netanyahu da Trump

Asalin hoton, Getty Images
Ana sa ran Netanyahu da Trump za su daddale waɗannan batutuwa a ganawar da za su yi wannan watan a Florida.
Shugaban Amurka, wanda ya jagoranci tsara yarjejeniyar ta Gaza, ya fara shirye-shiryen assasa hukumar zaman lafiya ta Gaza a farkon shekara mai zuwa.
Ana tunanin a ganawarsu ɗin ce Netanyahu zai ƙara miƙa buƙatar a tabbatar da raba Hamas ta makamai, da hana ta shiga mulkin Gaza a nan gaba, da kuma tabbatar da barin sojojin Isra'ila a daidai tudun mun tsira, da hana tura dakarun Turkiyya zuwa Gaza, kamar yadda kafar yaɗa labaran Gaza ta nuna.
A nasa ɓangare, ana sa ran shi kuma Trump zai matsa wa Netanyahu lamba "domin daina daƙile yunƙurin fara amfani da yarjejeniyar," in ji Gerson Baskin. "Isra'ila ta fi Hamas karya alƙawarin."
Tun bayan yarjejeniyar da aka tsara a 10 ga wata zuwa ranar 15 ga Disamba, kusan Falasɗinawa 400 aka kashe, sannan an illata kusan 1,000, kamar yadda ma'aikatar lafiya ta Hamas ta ruwaito.
Waɗanda aka kashe a Gaza tun bayan harin 7 ga watan Oktoban 2023, zuwa yanzu an kashe mutum 70,665, inda mutum 171,145 suka ji rauni, kamar yadda ma'aikatar ta bayyana.






