Mai wanke-wanken da ta zama mataimakiyar shugaban kasa

Francia Marquez na murmushi a wani gangamin yakin neman zabe

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Francia Marquez ita ce mace bakar fata ta farko da aka zaba a matsayin mataimakiyar shugabar kasa

Sakamakon zaben shugaban kasar Kolombiya na 2022 ya kasance na ban mamaki saboda dalilai da dama - tsohon dan gwagwarmaya Gustavo Petro ya zama shugaban kasa na farko mai ra’ayin kawo sauyi kuma abokiyar takararsa ita ma ta kafa tarihi.

A ranar 7 ga Agusta, Francia Marquez, wadda matashiya ce kuma uwa, wacce a da ta kasance kuyanga da mai hakar zinare, ta zama mataimakiyar shugaban kasa bakar fata ta farko a Kolombiya.

Marquez, mai shekaru 40, tana da kwarjini na musamman idan aka kwatanta ta da duk magabatanta.

Da farko, ba ta cikin tsarin siyasa da zamantakewar Kolombiya.

Kolombiya kasa ce mai kabilu da al’adu daban-daban kuma a al'adance ma’aikatunta sun kasance a hannun mazajen birnin, masu arziki kuma farar fata.

Amma sabuwar mataimakiyyar shugaban kasa ba ta gamsu da ƙimar kasancewa mace baƙar fata ta farko da za ta hau karagar mulki a karon farko ba.

Yaƙi da talauci da kuma tafiya da kowa da kowa

Francia Marquez
Bayanan hoto, Marquez ta yi hira da BBC jim kadan bayan ta yi nasara a zabe

Ta shaida wa BBC a wata hira da aka yi da ita a ranar 23 ga watan Yuni cewa "Ba wai na kawo kaina ba ne don na nuna fuskata a matsayin bakar fata ko na nuna kaina a matsayin mace ko kuma kawai na nuna cewa gwamnatinmu ta kunshi kowa da kowa".

An haifi Marquez a Yolombo, wani kauye mai nisan kilomita 437 daga Bogota babban birnin kasar.

Kauyen na cikin Jihar Cauca daya daga cikin yankuna masu fama da talauci da kuma yawan kauyuka a kasar.

Haka zakalika rikicin da aka shafe tsawon shekaru 65 ana yi tsakanin gwamnati da kungiyoyin sa kai da 'yan tawaye ya shafi yankin Cauca sosai."Alal misali an yi watsi da al’ummata na tsawon lokaci," in ji ta.

"Babu ruwan sha da tsaftar muhali ko wutar lantarki.”

Yadda ta zama uwa da mai hakar ma'adinai da kuma ‘yar gwagwarmaya

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Marquez tana daya daga cikin yara 12 kuma ta yi rayuwa a shekarunta na farko ta hanyar yin aiki tare da iyayenta a wata mahakar zinare da ke bakin kogin Ovejas.

Tana da shekaru 16 ta haihu kuma ta fara aiki a matsayin ‘yar aikin gida — da ke wanke-wanke da sauran ayyuka — domin ta samu kudin kula da babban danta Carlos tare da biyan kudin karatu a Jami'a a fannin aikin noma- tana kuma da Digirin Digirgir da ta samu shekaru biyu da suka gabata a fannin aikin lauya.

Marquez ta kuma rika fafitukar kare muhali, ciki har da zanga-zangar nuna adawa da shirin karkatar da kogin Ovejas zuwa madatsar ruwan Salvajina a cikin shekarun 1990. Tana cikin wadanda suka rika gangamin da ya sa Kotun Kolin kasar ta dakatar da aikin.

Daga bisani ta jagoranci wasu da suka nuna turjiya a kan shirin gwamnatin tarayya na ba kamfanonin kasashen waje hakkin hako ma'adinai bayan ta kori bakar fata 'yan Kolombiya da suka mallaki filayen hakar ma'adinai.

A 2014 tauraruwar Marquez ta haskaka inda ta jagoranci mata da dama a wani tattaki mai nisan kilomita 350 zuwa Bogota domin neman daukar mataki matsalolin da ake fuskanta a fannin zamantakewa da muhalli da hakar ma'adinai ba bisa kai'da ba a Cauca a lokacin mulkin Shugaba Juan Manuel Santos.

Francia Marquez

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Tauraruwar Francia Marquez ta haskaka ne bayan ta soma fafutuka

Marquez ta kuma halarci tattaunawar zaman lafiya tsakanin gwamnatin tarayya da FARC, wadda ita ce babbar kungiyar 'yan tawayen Kolombiya.

A yayin tattaunawar, ta bayar da hujjar cewa ' bakar fata ‘yan Kolombiya sun shafe shekaru da dama suna wahala sakamakon wannan rikici.

 "Bayanai daga ma'aikatar kididdiga ta kasa sun ce mata bakar fata suna rayuwa a matsakaicin shekaru biyar kasa da sauran matan Kolombiya.

Ina tsammanin wannan it ace shaida akan yadda tsarin wariyar launin fata ya ke aiki," in ji ta a cikin hirar 23 ga Yuni.

Ta rika fuskantar barazanar mutuwa

A 2018, an ba Marquez lambar yabo ta muhalli ta Goldman, wadda aka sani da sunan "Kyautar Nobel ta Green".

Marquez na rawa a wani gangamin yakin neman zabe a Medellinabe a Mede

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Francia Marquez na rawa a wani gangamin yakin neman zabe

Sai dai kuma wannan babban matsayi ya nuna cewa nan gaba mataimakiyyar shugaban kasar za ta fuskanci barazana a kasar da ta yi kaurin suna wajen kashe masu rajin kare hakkin bil'adama.

A cikin 2021 kadai, an kashe mutane 138 daga cikinsu a Kolombiya a cewar wata kungiyar farar hula da ake kira Front Line Defenders – watau kashi daya bisa uku na kashe-kashen da aka yi wa rajista a duk duniya a wannan shekarar.

Marquez ta tsallake rijiya da baya a shekarar 2019, lokacin da wasu 'yan bindiga suka kai hari wani taron da ta halarta a birnin Santander de Quilichao na Cauca.

Maimakon ta tsoratar da Marquez, lamarin da ya yi kamar ya sa ta himmatu wajen fafutukar ganin an yi adalci.

Ta sanar da takararta ta shugaban kasa a watan Afrilun 2021 kuma ta sami tagomashi da ya sa ta kai matsayi na biyu a zaben fitar da gwani na gammayar jam’iyyu masu ra’ayin kawo sauyi .

Wanda ya yi nasara shi ne Gustavo Petro, wanda nan take ya gayyaci Marquez don yin takara a matsayin mataimakiyyarsa.

Francia Marquez tare da Gustavo Petro

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Zababben shugaban kasar Kolombiya Gustavo Petro, tare da Francia Marquez

"Gayyatar da muke yi, watau ni da Gustavo Petro , ita ce babbar yarjejeniya kasa wadda ta kafa tushe mai karfi da fifiko don ci gaba da samar da c zaman lafiya mai dorewa da sulhu da kuma adalci na zamantakewa," in ji Marquez.

Kalubalen da ke gabansu a yanzu shi ne cika alkawuran da aka yi wa ‘yan kasar Kolombiya wadanda sun fidda rai daga tsarin zaben kasar wadanda kuma ba su da gata kamar yadda Marquez ta bayyana su a cikin jawaban yakin neman zabenta.

Ga masu lura da al’amura , cika waɗannan alkaura wani jan aiki ne mai cike da ƙalubale kamar yadda Marquez ta fuskanta har ta zama mataimakiyyar shugaban kasa.

"Ina ganin na fito fili karara dan na nuna wa alummar kasar, da jama'ata... ba za mu iya sauya matsalolin da suka faru a cikin shekaru 500 da suka gabata ba a cikin shekaru hudu kacal," in ji ta.

"(Amma) dole ne mu shirya a matsayinmu na kasa don kawo ci gaba gwargwadon iyawarmu."

Mutane kalilan ne za su yi nuna shakun cewa Marquez tana da kuzarin wannan gwagwarmaya.