Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Za mu ɗauki dakaru 10,000 don kare dazukan jihar Neja - Gwamna Bago
Gwamnan jihar Neja da ke arewacin Najeriya ya ce gwamnatinsa za ta sayi makamai domin bai wa dakarun rundunar tsaron dazukan jihar 10,000 da za ta kafa.
Gwamna Mohammed Umaru Bago ya bayyana hakan ne cikin wata hira ta musamman da BBC, yana mai cewa tuni suka fara bai wa matasan wannan runduna horo.
"Burinmu shi ne mu ɗauki matsa 1,000 daga kowace ƙaramar hukuma domin kare kanmu," in ji gwamnan. "Za mu sayi makamai sosai, abin da 'yanta'addan ke ji da shi su ma za mu ba su."
Ya ƙara da cewa gwamnatinsa za ta yi hakan ne tare da haɗin gwiwar gwamnatin tarayya domin ƙirƙirar rundunar mai suna Forest Guard, wadda za ta dinga saka ido da kuma tsare dazukan jihar masu faɗin gaske.
"Gwamnatin tarayya ta kawo tsarin da ake kira Forest Guard ta ce a tsinto matasa daga ƙananan hukumomi domin haɗa hannu wajen kare gandun dajin."
Jihar Neja na cikin wuraren da suka fi fama da hare-haren 'yanbindiga da ke kashewa da kuma kama mutane domin neman kuɗin fansa, baya ga mayaƙan ƙungiyar Boko Haram da suka ɓulla sassan jihar.
A cewar rahoton kamfanin SBM Intelligence mai sa ido kan harkokin tsaro, hare-haren 'yanbindiga sun kashe aƙalla mutum 68 a wata ukun farko na 2025.
Gwamna Bago ya ce 'yanbindigar na kwarara ne daga jihohin Zamfara da Kaduna maƙwabtan jihar.
"Mun san daga inda suke fitowa, muna iyaka da Zamfara da Kaduna da Kebbi da Katsina, da kuma ƙasar Benin. Ta nan ne kuma suke fitowa su yi mana ɓarna.
"Idan muka ajiye dakaru 10,000 babu wani ɗan'ta'adda da zai yi mana barazana. Za mu haɗa kai da 'yansanda, ba za mu jira su zo ba ma, mu ne za mu dinga kai mu su hari."
Dalilin kafa dokar yin wa'azi
Gwamnan ya taɓo batutuwa da dama, ciki har da dalilin da ya sa gwamnatinsa ta kafa dokar tantance malamai kafin su yi wa'azi.
Umaru Bago ya ce duk malamin da ba zai bi dokar ba sai dai ya bar jihar Neja.
"Muna so mu tabbatar daga inda suke, mu tantance su, mau ba su lasisi. Idan ba za su yi hakan ba to sai dai su bar mana jiharmu, babu dole," a cewarsa.
"Muna da malamai masu muguwar aƙida. Kamar ƙungiyar Ansaru, babu yadda za a yi mu bari mutum ya shigo gari ya buɗe masallaci yana zagin gwamnati, yana ƙaryata Annabi, kuma ya ce shi Musulmi ne.
"A jihar Neja dai, matuƙar mutum yana son ya yi wa'azi, dole ne sai ya nemi izini."
Da aka tambaye shi anya ba suna yin hakan ne domin murƙushe 'yan'adawar siyasa ba, sai ya ce: "Ai dimokuraɗiyya ba hauka ba ne. Addini na da ƙa'ida."
A baya-baya nan, gwamnatin Neja ta tsare wani matashi da ke iƙirarin malami ne bayan salon wa'azinsa ya jawo cecekuce saboda yadda ya dinga kafirta mutanen da ke aikata wasu ayyuka.