Hotunan Afirka: Gangamin goyon bayan Falasɗinawa da Shugaba Tinubu a Brazil

    • Marubuci, Cecilia Macaulay
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
  • Lokacin karatu: Minti 5

Zaɓaɓɓun ƙayatattun hotunan mako daga sassan Afirka da duniya:

Masu wasa da babur a birnin na Nairobi sun cika titi a ranar Lahadi inda suke fareti domin nuna goyon bayansu ga Falasɗinawa daidai lokacin da ake yakin Isra'ila da Gaza ke ci gaba da ƙazanta.

Asalin hoton, Gerald Anderson/Anadolu/Getty Images

Bayanan hoto, Masu wasa da babur a birnin na Nairobi sun cika titi a ranar Lahadi inda suke gangamin nuna goyon bayansu ga Falasɗinawa daidai lokacin da ake yakin Isra'ila da Gaza ke ci gaba da ƙazanta.
An gudanar da biki a Brazil washegarin ranar inda Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu yake duba masu yi masa faretin ban-girma da suka tarbe shi zuwa Fadar Planalto da ke Brazilia...

Asalin hoton, Evasristo Sa/AFP/Getty Images

Bayanan hoto, An gudanar da biki a Brazil washegarin ranar Lahadi inda Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu yake duba masu yi masa faretin ban-girma da suka tarbe shi zuwa Fadar Planalto da ke Brazilia...
Shugaba Bola Tinubu da takwaransa na Brazil, Shugaba Luiz Inacio Lula da Silva sun rattaba hannu kan wasu yarjeniyoyi.

Asalin hoton, Adriano Machado/Reuters

Bayanan hoto, Tinubu da takwaransa na Brazil, Shugaba Luiz Inacio Lula da Silva sun kuma sa hannu kan wasu yarjeniyoyi.
A Ranar Juma'a ke nan waɗannan ƙwararrun masu ɗinka kaya kan jan kafet a Sun City da ke Afirka ta Kudu suke nuna kayan ƙawa a bikin bayar da kyaututtuka na zane-zane da al'adu na ƙasa.

Asalin hoton, Oupa Bopape/Gallo Images/Getty Images

Bayanan hoto, A Ranar Juma'a ke nan waɗannan ƙwararrun masu ɗinka kaya kan jan kafet a Sun City da ke Afirka ta Kudu suke nuna kayan ƙawa a bikin bayar da kyaututtuka na zane-zane da al'adu na ƙasa.
Wasu mata sanye da kaya masu ƙayatarwa a wani bikin bajekolin kaya masu ban mamaki na Afirka ta Kudu da aka yi a birnin Johannesburg ranar Alhamis.

Asalin hoton, Kim Ludbrook/EPA/Shutterstock

Bayanan hoto, Wasu mata sanye da kaya masu ƙayatarwa a wani bikin bajekolin kaya masu ban mamaki na Afirka ta Kudu da aka yi a birnin Johannesburg ranar Alhamis.
Wasu yanmata a ranar Lahadi 24 ga Agustan 2025 ke nan da suka halarci bikin Ashenda da ake yi tsawon shekaru domin tunawa da mahaifiyar Annabi Isa a Mekelle da ke arewacin ƙasar Habasha...

Asalin hoton, Girmay Gebru/BBC

Bayanan hoto, Wasu yanmata a ranar Lahadi ke nan da suka halarci bikin Ashenda da ake yi tsawon shekaru domin tunawa da mahaifiyar Annabi Isa a Mekelle da ke arewacin ƙasar Habasha...
Sun ci kwalliya domin halartar taron na tsawon yini uku inda suka sha kitso da ke nuna tsawon gashinsu.

Asalin hoton, Girmay Gebru/BBC

Bayanan hoto, Sun ci kwalliya domin halartar taron na tsawon yini uku inda suka sha kitso da ke nuna tsawon gashinsu.
A irin ranar kuma a Nairobi, babban birnin Kenya, wani mabiyin addinin Rastafari riƙe da littafin Injila a wani taron yin addu'oi.

Asalin hoton, Gerald Anderson/Anadolu/Getty Images

Bayanan hoto, A irin ranar kuma a Nairobi, babban birnin Kenya, wani mabiyin addinin Rastafari riƙe da littafin Injila a wani taron yin addu'oi.
A birnin Omdurman na ƙasar Sudan kuma wasu Musulmi ne suka gudanar da bikin Maulidi gabanin zagayowar ranar haihuwar Annabi Muhammad SAW a ranar Asabar 23 ga watan Agustan 2025...

Asalin hoton, AFP/Getty Images

Bayanan hoto, A birnin Omdurman na ƙasar Sudan kuma wasu Musulmi ne suka gudanar da bikin Maulidi gabanin zagayowar ranar haihuwar Annabi Muhammad SAW a ranar Asabar 23 ga watan Agustan 2025...
A dai makon ne kuma a birnin Khartoum, wani ɗan Sudan ne tsaye cikin ruwan da ya kai har gwiwoyinsa bayan wani mamakon ruwan sama daidai lokacin da ma'aikata ke ƙoƙarin yin amfani da bututu domin kwashe ruwan da ya mamaye titi. Hakan ya faru ranar Laraba 27 ga watan Agustan 2025.

Asalin hoton, Ebrahim Hamid/AFP/Getty Images

Bayanan hoto, A dai makon ne kuma a birnin Khartoum, wani ɗan Sudan ne tsaye cikin ruwan da ya kai har gwiwoyinsa bayan wani mamakon ruwan sama daidai lokacin da ma'aikata ke ƙoƙarin yin amfani da bututu domin kwashe ruwan da ya mamaye titi.
A Masar mai maƙwabtaka, waɗannan yaran suna more rayuwarsu yayin da suke wasa cikin wurin iyo na yara a Alƙahira, babban birnin ƙasar ranar Talata da aka yi zafi....

Asalin hoton, Ahmad Hasaballah/Getty Images

Bayanan hoto, A Masar mai maƙwabtaka, waɗannan yaran suna more rayuwarsu yayin da suke wasa cikin wurin iyo na yara a Alƙahira, babban birnin ƙasar ranar Talata da aka yi zafi....
A ranar Alhamis ke nan a gabashin Jamhuriyar Dimokraɗiyyar Congo inda wata mata a Kibumba ke dakon jibgegen katako a bayanta.

Asalin hoton, Jospin Mwisha/AFP/Getty Images

Bayanan hoto, A ranar Alhamis ke nan a gabashin Jamhuriyar Dimokraɗiyyar Congo inda wata mata a Kibumba ke dakon jibgegen katako a bayanta.
A irin ranar ce kuma. wani mutum ke murmushi bayan halartar bikin ƙaddamar da yakin neman zaɓen Shugaba Samia Suluhu Hassan a Dar es Salaam, babban birnin Tanzania.

Asalin hoton, Anthony Siame/EPA/Shutterstock

Bayanan hoto, A irin ranar ce kuma, wani mutum ke murmushi bayan halartar bikin ƙaddamar da yakin neman zaɓen Shugaba Samia Suluhu Hassan a Dar es Salaam, babban birnin Tanzania.
Ranar Talata ke nan inda Shugaban Ivory Coast Alassane Ouattara ke gaishe da ɗumbin magoya bayansa a Abidjan bayan da ya leƙo waje ta saman wata mota yayin da yake sanar da takararsa a zaɓen watan Oktoba.

Asalin hoton, Egnan Koula/EPA/Shutterstock

Bayanan hoto, Ranar Talata ke nan inda Shugaban Ivory Coast Alassane Ouattara ke gaishe da ɗumbin magoya bayansa a Abidjan bayan da ya leƙo waje ta saman wata mota yayin da yake sanar da takararsa a zaɓen watan Oktoba.
Sannan tawagar mata ƴanwasan zari ruga a Afirka ta Kudu na murnar samun nasara da ci 66 - 6 kan abokan wasansu na Brazil a gasar wasan zari ruga na mata da aka yi a Birtaniya ranar Lahadi.

Asalin hoton, Andrew Boyers/Reuters

Bayanan hoto, Sannan tawagar mata ƴanwasan zari ruga a Afirka ta Kudu na murnar samun nasara da ci 66 - 6 kan abokan wasansu na Brazil a gasar wasan zari ruga na mata da aka yi a Birtaniya ranar Lahadi.