Me ake nufi idan sunanka ya fito a jerin masu tallafa wa ta'addanci?

..

Asalin hoton, Getty Images

Wannan tambayar ce a bakunan 'yan Najeriya, tun bayan fitar da jerin sunayen wasu mutum 15 da sashen kula da bayanan sirri da suka jibanci kudade, NFIU, ta fitar a ranar Laraba.

A jerin sunayen dai gwamnatin Najeriya ta fallasa wasu mutane da kuma kamfanonin 'yan canjin da ta ce su ke daukar nauyin ayyukan ta'addanci a kasar.

Bayanai sun nuna cewa an jima ana bibiyar ayyukan mutanen 15 tare da alkawarin daukar mataki kan su.

Masana harkar tsaro a Najeriya sun bayyana makomar mutanen 15 ciki kuwa har da Malam Garba, Mamu wani mai kamfanin jarida a Kaduna.

Yaya ake alakanta mutum da ta'addanci?

Kafin dai rikicin Boko Haram, za a iya cewa Najeriya ba ta mayar da hankali kan dokokin dakile ta'addanci ba, wanda hakan ne ya sa ake yi wa abin da sashen gwamnati mi kula da bayanan sirri da suka jibanci kudade wato NFIU, kallon wani sabon al'amari.

Ayyana mutum 15 da ta'addanci dai shi ne irinsa na farko da aka yi wa wasu 'yan kasa wadanda ba sa dauke da makami ko kuma suka ja daga da gwamnati kamar 'uyan kungiyar Boko Haram da barayin daji da ma wasu kungiyoyin masu kama da wadannan.

Malam Kabiru Adamu, shugaban kamfanin da ke samar da bayanan tsaro na Beacon Consulting ya yi bayani dangane da yadda suke kallon wannan al'amari.

"Wannan dai na daya daga cikin matakan yaki da ta'addanci da ake kira da 'Counter Terrorism Strategy' da kuma dokar hana ta'addanci wato 'Terrorism Prevention and Prohibition Act', wadda ta fayyace hanyoyin da za a bi domin fallasa mutumi ko kamfani da ake tuhuma da ta'addanci." In ji Malam Kabiru.

To amm kuma masanin ya nuna dan shakku kan yadda Najeriya ke gudanar da dokokin dakile ta'addancin.

"Muna fatan wadannan hanyoyin da doka ta shimfida a kabi wajen fallasawar, domin ya kamata a ce sai an je kotu wadda ita kadaice za ta iya ayyana mutum a matsayin dan ta'adda ko kuma mai tallafawa ta'addancin.Amma da alama ba mu ga an yi hakan ba."

To sai dai Malam Kabiru ya ce duk da haka yana da kwarin gwiwa cewa akwai kyakkyawan fata kan al'amarin.

" Sai dai kawai abu daya da yake ba mu kwarin gwiwa shi ne wadannan mutanen 15 da aka ayyana muna sane da cewa an dade ana bin sawunsu tun ma a gwamnatin baya, ba wai wannan gwamnatin ce ta fara ba. Muna fatan lokacin da aka kwashe ana bibiyar su din an bi wadannan ka'idoji." In ji shugaban Beacon Consulting.

Wane zabi ya rage wa mutum 15 din?

Malam Kabiru Adamu ya ce wannan ayyana sunayen na mutum 15 da sashen NFIU ya yi ba wai na nufin shi kenan mutanen sun zama 'yan ta'adda kuma za a zartar da hukunci a kansu ba.

Ya kara da cewa ita dai gwamnati ta yi nata aiki su kuma wadanda aka ayyana din suna da "damar zuwa kotu domin kalubalantar fallasawar da aka yi musu. Wannan ba shi ba ne mataki na karshe.

To amma Idan ba su je kotun domin daukaka kara ba, to wannan ya bai wa jami'an tsaro dama da su dauki matakai daban-daban a kansu." In ji Kabiru Adamu.

'Akwai sauran runa a kaba'

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Malam Kabiru Adamu ya ce duk da matakin fallasa wadanda ake tuhuma da tallafawa ta'addanci abin a yaba ne amma kuma ya ce "har yanzu akwai sauran runa a kaba."

Ya kara da cewa " idan ka yi la'akari da yadda a cikin sunayen mutum 15 duk babu ma'aikacin banki ko guda daya to ka san akwai sauran runa a kaba kasancewar duk wani wanda yake ta'ammali da kudi a Najeriya ta hanyar banki yake yi wato da ma'aikatan banki ake yin su.

Sannan duba ga rahoton da Giaba ta fitar wato wani sashe na kungiyar ECOWAS da ke sa ido kan yadda kasashe ke bin dokokin ta'ammali da kudade masu alaka da ta'addanci tsakanin kasashe wanda ya bayar da shawarwari masu yawa wadanda kaso fiye da 70 hakki ne na gwamnati, akwai matsala.

To amma yanzu ba mu ga an hada da 'yan gwamnati ba sai dai 'yan kasa masu zaman kansu. To idan dai ana son yin abin tsakani da Allah ya kamata a kwatanta irin dokar a kan 'yan gwamnati da kuma ma'aikatan banki." In ji Malam Kabiru Adamu