'Abin da ya sa muka yi wawason abinci'

'Abin da ya sa muka yi wawason abinci'

Dubban Falasɗinawa ne suka ɓalle wani rumbun ajiyar abincin tallafi na Majalisar Dinkin Duniya a Gaza a ranar Asabar, yayin da Isra'ila ke ci gaba da luguden wuta.

MDD ta yi gargaɗin cewa za a samu rashin bin doka da oda idan ba a tsagaita wuta domin shigar da kayan agaji ba.