Ali Bongo da shugabannin Afirka da suka kafe a kan mulki

Asalin hoton, Getty Images
Gabon ce, ƙasa ta baya-bayan nan da sojoji suka sanar da ƙace mulki da ƙrfin tsiya.
Jagororin rundunar sojan ƙasar sun yi jawabi ta kafar talbijin ɗin gwamnati cewa sun soke sakamakon zaɓen da aka yi ranar Asabar da ta wuce, wanda aka sanar hamɓararren shugaba Ali Bongo a matsayin wanda ya yi nasara.
Hukumar zaɓen ƙasar ta ce Mista Bongo ya samu nasara da kashi ɗaya cikin uku na ƙuri'un da aka kaɗa a zaɓen da 'yan adawa suka ce an tafka maguɗi.
Juyin mulkin ya kawo ƙarshen mulkin shekara 53, da suka yi ta yi, shi da mahaifinsa a Gabon.
Bongo ya hau mulki a 2009, bayan rasuwar mahaifinsa Omar Bongo.
Haka zalika, juyin mulkin na Gabon ya zo ne bayan wasu juye-juyen mulkin da aka yi a ƙasashen Afirka irinsu Mali da Burkina Faso da Guinea da Nijar da Sudan tun daga shekara ta 2020.
A gefe guda kuma, ba Shugaba Bongo ne kaɗai ya shafe shekaru a kan mulki ba tare da sauran iyalansa.
Bari mu dubi wasu shugabannin da suka shafe tsawon lokaci a kan mulki.
Shugabannin Afirka da suka kafe a kan mulki
Teodoro Obiang Nguema Mbasogo - Equatorial Guinea

Asalin hoton, Getty Images
Shugaba Teodoro Obiang Nguema Mbasogo, mai shekara 81 a yanzu, shi ne shugaban da ya fi kowa daɗewa a kan mulki a faɗin duniya.
Ya shafe shekara 44 a kan mulki yana kuma ci gaba.
Ɗan siyasar kuma tsohon jami'in soja, shi ne shugaban Equatorial Guinea na biyu, wanda ya hau mulki tun ranar 3 ga watan Agustan 1979.
An sake zaɓen Mista Obiang bayan sanar da shi a matsayin wanda ya yi nasara da kashi 95 na ƙuri'un da aka kaɗa a Nuwamban 2022.
Ɗansa mai suna Teodoro Nguema Obiang Mangue, shi ne mataimakin shugaban ƙasa. Bayan sanar da nasararsu ya ce: "Sakamakon ya sake tabbatar da gaskiyarmu...za mu ci gaba a matsayin babbar jam'kiyya."
Shugaba Obiang na ci gaba da riƙe madafun ikon ƙasar ta tsakiyar Afirka, kuma iyalai da abokansa na riƙe da manyan muƙamai.
Paul Biya - Kamaru

Asalin hoton, ANADOLU AGENCY/GETTY IMAGES
Paul Biya ne shugaban ƙasar Kamaru, wanda ya hau mulki tun daga 1982.
An haifi Biya a ranar 13 ga watan Fabrairun 1933, kuma shi ne shugaba mafi yawan shekaru a ƙasashen Saharar Afirka.
Paul Biya ya sake cin zaɓe a karo na bakwai bayan zaɓen shugaban ƙasa da aka yi na 2018.
'Yan adawa sun nemi a shiga zagaye na biyu a zaɓen amma majalisar tsarin mulki ta yi watsi da kiran nasu.
Mista Biya ya karɓi shugabanci daga Amhamdou Ahidjo, wanda shi ne firaministan Kamru kuma shugaban ƙasar na farko.
Ya fara mulki a ranar 30 ga watan Yunin 1975, kuma za a sake yin zaɓen shugaban ƙasa a 2025.
Denis Sassou Nguesso - Jamhuriyar Kongo

Asalin hoton, AFP
Denis Sassou Nguesso ne shugaban ƙasar Congo-Brazzaville.
Ya sake ɗarewa kan mulki bayan an yi wa tsarin mulki kwaskwarima, wanda ya ba shi damar sake neman wa'adi na uku a 2016.
Mista Nguesso wanda tsohon jami'i ne a rundunar soja, ya fara mulkin ƙasar tun 1997.
Gwamnatinsa ta sauya tsarin mulki da zimmar gudanar da ƙuri'ar raba gardama a watan Oktoba, inda aka cire ƙayyade wa'adi da kuma yawan shekaru.
Denis Sassou Nguesso mai shekara 80 zai sake yin takara a karo na biyar.
Yoweri Museveni - Uganda

Asalin hoton, Getty Images
Shugaban Uganda Yoweri Museveni ya hau mulki bayan juyin mulkin da aka yi a 1986.
Shi ne shugaban Uganda na tara a tarihi. An haife shi ranar 15 ga watan Satumban 1944.
Mista Museveni mai shekara 78 ya mulki Uganda shekara 37.











