Everton ta yi wa Liverpool fancale a Goodison Park

Liverpool ta ci karo da koma baya a shirin lashe Premier League na bana, bayan da Everton ta doke ta 2-0 a Goodison Park ranar Laraba.

A minti na 27 da fara wasan hamayya Jarrad Branthwaite ya zura kwallo, sannan Dominic Calvert-Lewin ya ci na biyu a zagaye na biyu.

Rabonda Everton ta doke Liverpool 2-0 a Goodison Park a babbar gasar tamaula ta Ingila tun ranar 17 ga watan Oktoban 2010/11.

Wannan shi ne wasan farko da Everton ta yi nasara a kan Jurgen Kloop a Goodison Park a karawa ta 19, bayan da ta ci 2-0 a Anfield a 2021.

Da wannan sakamakon Liverpool ta ci karo da koma baya, inda Arsenal ta ba ta tazarar maki uku a rige-rigen lashe Premier da suke yi har da Manchester City a bana.

Ita kuwa Everton mai maki 33 tana ta 16 a kasan teburi da tazarar maki bakwai tsakani da Nottingham Forest ta 17.

Ranar Alhamis Manchester City mai kwantan wasa biyu, mai maki 73 za ta je gidan Brighton, domin karawa a tsakaninsu.

Ranar 27 ga watan Afirilu Liverpool za ta je gidan West Ham, domin buga wasan mako na 35 a Premier League.

Ranar Asabar 21 ga watan Afirilu Liverpool, wadda aka fitar da ita a FA Cup da Europa League a bana ta je ta doke Fulham 3-1 a wasan mako na 34 a babbar gasar tamaula ta Ingila.

Ita kuwa Everton za ta karbi bakuncin Brentford ranar Asabar 27 ga watan Afirilu, bayan da ta doke Nottingham Forest 2-0 a makon jiya.

Sakamakon kwantan wasannin da aka buga ranar Laraba:

  • Wolverhampton 1-1 Bournemouth
  • Crystal Palace 2-0 Newcastle United
  • Everton 2-0 Liverpool
  • Manchester United 4-2 Sheffield United