Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
'Mutum miliyan 14 na iya mutuwa nan da 2030 saboda janye tallafin Trump'
- Marubuci, Stuart Lau
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
- Lokacin karatu: Minti 2
Matakin da shugaban Amurka ya ɗauka na katse mafi yawan tallafin - da Amurka ke bai wa ƙasashe - ka iya haddasa mutuwar fiye da mutum miliyan 14 nan da 2030, kamar yadda binciken mujallar kiwon lafiya ta Lancet ya nuna.
Kashi uku cikin huɗu na waɗanda ke cikin hatsarin mutuwar ƙananan yara ne, a cewar binciken.
Ƙasashe masu ƙaramin ƙarfi da masu matsakaicin samu ne kan gaba wajen fuskantar barazanar katse tallafin.
Ana kwatanta katse tallafin da annoba ko gagarumin yaƙi,'' a cewar Davide Rasella, wanda ke cikin waɗanda suka wallafa rahoton.
A watan Maris sakataren harkokin wajen Amurka, Marco Rubio ya ce an soke fiye da kashi 80 cikin 100 na duka shirye-shirye hukumar bayar da agaji ta Amurka (USAID).
Shugaba Trump da abokansa sun ce sun gano cewa ana tafka almundahana da zamba a hukumar.
Rahoton na zuwa ne yayin da gomman shugabannin duniya ke taro a birnin Saveilla na ƙasar Sifaniya cikin makon nan domin tattauna batun katse tallafin - wanda ya fi kowane bayar da agaji a duniya.
Bayan nazarin bayanan alƙaluman tallafin hukumar a ƙasashe 133 a duniya, binciken ya ƙiyasta cewa tallafin USAID ya rage mutuwar mutum miliyan 91 a ƙasashe masu tasowa tsakanin 2001 zuwa 2021.
Sun kuma yi amfani da wani ƙiyasi wajen hasashen yadda rage tallafin da kashi 83% - adadin da gwamnatin Amurka ta sanar a farkon wannan shekara - na iya shafar adadin masu mutuwa.
Rahoton ya ce katse tallafin zai haifar da mutuwar miliyan 14 nan da shekarar 2030.
Adadin ya ƙunshi yara fiye da miliyan 4.5 ƴan ƙasa da shekara biyar, kwatankwacin mutuwar ƙananan yara 700,000 a kowace shekara.
Gwamnatin Trump - ƙarƙashin sabuwar hukumar kula da kashe kuɗaɗen gwamnati, da a baya hamshaƙin attajirin nan Elon Musk ya jagoranta - ta ƙudiri aniyar rage kashe kuɗaɗen gwamnatin tarayya.
Gwamnatin ta kuma zargi USAID da taimaka wa wasu ayyukan da ba sa cikin ayyukansa.
A yanzu haka Amurka, ta hanyar hukumar USAID - wadda ta fi kowace hukuma bayar da tallafi a duniya - na aiki a ƙasashen duniya fiye da 60, ta hanyar masu kwantiragi.
A cewar Marco Rubio, har yanzu akwai shirye-shirye kimanin 1,000 da hukumar ke gudnarwa.
A watan da ya gabata wani jami'in Majalisar Dinkin Duniya ya shaida wa BBC cewa dubban mutane na faɗawa ƙangin yunwa ''sannu a hankali''.
Ya ce a wasu sansanonin ƴangudun hijira a Kenya sun fara ganin tasirin hakan bayan samun raguwar tallafin kayan abinci zuwa maƙura.
A wani asibiti a Kakuma, da ke arewa maso yammcin Kenya, BBC ta shaida yadda wasu jarirai ke fama da alamomin yunwa sakamakon katse tallafin USAID da iyayensu ke samu.