Me ya sa ɗalibai suka kasance sahun gaba a zanga-zangar Turkiyya?

Wani mutum riƙe da tutar Turkiyya yayin da mutane suka fita zanga-zanga a birnin Santambul.

Asalin hoton, Reuters

    • Marubuci, BBC News Turkish
    • Aiko rahoto daga, Istanbul
  • Lokacin karatu: Minti 6

Tun bayan ɓarkewar zanga-zanga sakamakon kama Magajin garin Istanbul Ekrem Imamoglu – wanda ya kasance babban abokin hamayya ga shugaba Recep Tayyip Erdogan - an tsare kusan mutum 2,000 a faɗin Turkiyya. Da yawa cikin waɗanda aka kama ɗaliban jami'a ne, waɗanda ke sahun gaba a zanga-zangar.

Duk da haramta zanga-zanga a Istanbul, birni mafi girma a ƙasar Turkiyya, ɗalibai sun bazama kan tituna tare da kauce wa umarnin hukumomi. Suna taruwa ne a wani dandali da ke birnin - Sarachane Park - inda dandazon mutane ke shafe dare suna tsaye, yayin da ƴan sanda kuma ke bin su suna kame da kuma tarwatsa su ta hanyar fesa musu hayaki mai sa hawaye.

Sai dai, jam'iyyar Imamoglu ta Republican People's Party (CHP) ta sauya tsari a baya-bayan nan, inda suka buƙaci a kawo karshen taruwar mutane a dandalin Sarachane.

Maimakon haka, sun buƙaci masu zanga-zanga su riƙa yi daga gida - ta hanyar karfafawa da kuma ɗaga tutoci ta tagoginsu. Jam'iyyar ta kuma shirya gagarumin maci a ranar Asabar. Yayin da aka haramta zanga-zanga a Istanbul, ba a hana yin maci ba.

Sai dai ɗalibai sun ce babu guda ba ja da baya.

Maimakon taruwa a dandalin Macha da ke tsakiyar birnin Santambul, da dama cikinsu sun saka takunkumin fuska domin ɓoye fuskokinsu da kuma kauce wa kame.

Sun ki a ɗauki hotunansu sannan sun buƙaci a sakaya sunayensu saboda dalilai na tsaro.

"Muna mafarkin ƙasar da za mu yi zanga-zanga ba tare da ɓoye fuskokin mu ba lokacin zanga-zanga," kamar yadda ɗaya daga cikin ɗaliban ya faɗa wa BBC.

Shugaba Erdoğan, ya kira masu zanga-zangar sanye da takunkumi da "ƴan ta'adda" a wata sanarwa ranar 26 ga watan Maris.

'Nuna bambanci a shari'a'

An tsare Imamoglu ranar 19 ga watan Maris, bayan kama shi kan zargin rashawa - a ranar da aka sanar da shi a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar CHP.

Ana sa ran gudanar da zaɓen shugaban ƙasa a Tukiyya a 2028, amma ana samun jita-jitar cewa za a iya dawo da zaɓen baya.

Masu adawa sun hakikance cewa zargin da ake yi wa Imamoglu na da alaƙa da siyasa, inda suka kira kamen da aka yi amsa da "juyin mulki" - zargin da Erdoğan ya musanta.

Ɗalibai lokacin da suka fita zanga-zanga.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Duk da haramta zanga-zanga a Istanbul, birni mafi girma a Turkiyya, ɗalibai sun bazama kan tituna tare da kauce wa umarnin hukumomi.
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Duk da cewa ɗaliban da ke zanga-zanga a dandalin Macha sun bayyana cewa ba su da alaƙa da wata jam'iyyar siyasa, wasu na rera wani take da aka fi sanin magoya bayan adawa da yin sa: "Ƴanci, doka da kuma hukunci!"

"Ka duba halin da muke ciki, " wani ɗalibi ya faɗa. "Suna tura mutane kurkuku ba tare da kai su kotu ba."

Wani ɗalibin ya nuna fushinsa kan bambanci wajen yin shari'a.

"Wannan zanga-zanga ba wai don an kama Imamoglu bane kawai - muna yin ta ne kan yadda ba a yin cikakken bincike kan waɗanda ake zargi," in ji shi.

Da dama daga cikinsu sun buƙaci a bai wa ɓangaren shari'a ƴanci.

"Muna son gwamnati ta daina iko da kotuna," wani ɗalibi ya bayyana. Gwamnati ta hakikance cewa ɓangaren shari'ar Turkiyya yana zaman kansa ne.

Baya ga batun Imamoglu, ɗaliban sun nuna ɓacin-rai wasu batutuwa da dama - ciki har da rashin kyawun tattalin arziki da kisan mata da kuma rashin tabbas kan makomarsu.

Wani abin damuwa shi ne ƙwace shaidar karatun diploma na Imamoglu, wanda hakan na nufin cewa ba shi da damar stayawa zaɓen shugaban ƙasa karkashin dokokin Turkiyya.

"Idan za su ƙwace shaidar karatunsa na diploma, me zai hana su ƙwace namu?" wani ɗalibi ya tambaya.

Duk da irin waɗannan kalubale, ba dukkan matasa ne ke son barin Turkiyya ba.

"Yawancin abokaina da muka yi karatu sun fita waje," in ji wani ɗalibi. "Amma ina son zama. Ni matashin ɗan Turkiyya ne, kuma ina son gina makomata a nan."

Zanga-zanga mai zaman kanta

Duk da cewa jam'iyyar adawa ta CHP ta kawo karshen zanga-zanga ta tsawon dare a dandalin Sarachane, har yanzu ba a kai ga kammala zanga-zangar baki-ɗaya ba.

Jam'iyyar ta sha alwashin ci gaba da fautuka ta hanyar maci a wasu wurare daban, sai dai ɗalibai da dama sun jajirce wajen ci gaba da zama kan tituna.

"Ba mu je dandalin Saraçhane don Imamoglu kaɗai ba, mun je don dimokraɗiyya," a cewar wani ɗalibi, inda ya ce zanga-zangar za ta ci gaba da wakana. "Akwai wurare da dama a ƙasar nan da za mu yi zanga-zanga."

Wani ɗalibi ya yi watsi da buƙatar jam'iyyar CHP ta sauya tsare-tsare, inda ya ce zanga-zangar mai zaman kanta ce.

"Abin da jagororin CHP suka faɗa bai dame mu ba," in ji shi. "Za mu iya yanke shawara a tsakanin mu, a matsayin masu zaman kansu da kuma sauya al'amura. Ba mu buƙatar jagorancin jam'iyyar siyasa."

Ɗalibai ƴan jami'a na zanga-zanga.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Ɗalibai da ke zanga-zanga sanye da takunkumi domin kauce wa bayyana fuskokinsu ko kame

Ɗalibai sun sha alwashin kawo cikas ga harkokin rayuwar yau da kullun ta hanyar zanga-zanga kan tituna da kaurace wa abubuwan inganta tattalin arziƙi, domin a ji buƙatunsu.

Wani ɗalibi ya lura cewa hakan yana da mahimmanci domin zai tilastawa jama'a su "san abin da ke faruwa".

Ya ƙara da cewa kafafen yaɗa labarai da gwamnati ke kula da su sun hana ƴan ƙasar ganin gaskiyar abin da ya sa ake zanga-zangar.

"Sai gwamnati ta tantance labarai kafin ku same su a kafafen yaɗa labarai. Amma idan kun ga abin da ke faruwa a kan tituna, za ku ga gaskiya - sau nawaƴan sanda suka yi amfani da karfi, kuma ko da gaske masu zanga-zangar na yin abin da bai dace ba."

Hukumar da ke kula da kafafen yaɗa labarai a Turkiyya RTUK, ta ƙara kaimi wajen murkushe rahotannin zanga-zangar. A farkon wannan makon, ta gargaɗi kafafen yaɗa labarai masu alaƙa da 'yan adawa da masu zaman kansu kan cewa za a haramta masu watsa shirye-shirye na dogon lokaci.

A ranar alhamis, RTUK ta dakatar da tashar talabijin ta 'yan adawa Sozcu na tsawon kwanaki goma, bisa zargin tada zaune tsaye. Hukumar ta yi gargaɗin cewa, idan tashar ta sake yin wani "laifi" bayan wa'adin dakatarwar ya kare, za a soke lasisinsa.

Sanarwar ta zo ne a daidai lokacin da BBC ta ce Turkiyya ta kori ɗaya daga cikin 'yan jaridarta, Mark Lowen, wanda ke aiko da rahotanni kan zanga-zangar, bisa dalilin cewa aikinsa na barazana ga zaman lafiyar jama'a.

An ɗauke Lowen daga otal ɗinsa na Istanbul ranar Laraba a wani abin da shugabar ɓangaren yaɗa labarai na BBC Deborah Turness ta kira "lamari mai matukar tayar da hankali".

Zanga-zangar gama-gari

Ɗalibai sun taru a gaban jami'ar Istanbul yayin zanga-zanga.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Ɗalibai sun yi alwashin kawo cikas ga harkokin rayuwar yau da kullum ta hanyar zanga-zanga kan tituna

Ɗaliban jami'a sun ɗau alwashin kin halartar ajuzuwa har sai an saki dukkan masu zanga-zanga da aka kama. Bayan nuna fushi kan abin da suka kira naɗe-naɗen masu goyon bayan gwamnati a faɗin wasu jami'o'in ƙasar, suna kuma yin kira na sake dawo da wasu hakkoki da ɗalibai ke da su.

"Ba za mu koma ba har sai an saki dukkan waɗanda aka tsare sannan an ɗage matsin lamba kan jami'o'i," a cewar wani ɗalibi, inda ya yi kiran gudanar da zanga-zangar gama-gari.

"Yayin da muka dakatar da zuwa ajuzuwa, muna kira ga dukkan ma'aikata da kuma ƙungiyoyi da su zo a shiga zanga-zangar da su. Muna so mu ga an yi zanga-zanga a faɗin ƙasa. Za mu tsayar da al'amura cak," in ji shi.

Wani ɗalibi ya nuna ɓacin rai kan tsarin siyasa.

"Yanzu mun gano cewa ba za mu yi nasara kan komai ba da zaɓe kaɗai. Kaɗa kuri'a ba zai sauya al'amura ba - shi ya sa za mu fita kan tituna," a cewar ta.

Duk da turjiyarta, ta nuna buƙatar son gudanar da zanga-zangar lumana.

"Za mu ci gaba da kasancewa muryar al'umma, kuma za mu ci gaba da yin zanga-zanga cikin lumana," in ji ta.