Masoyan da aka yi wa 'kisan gilla' saboda bambancin addini

- Marubuci, Abhishek Dey
- Lokacin karatu: Minti 7
Kisan gilla kan auren masu bambancin addini da aka yi wa wasu masoya da kuma kama ƴan'uwar budurwar da ƴansanda suka yi kan zargin hannu a lamarin ya girgiza al'ummar wani ƙauye a jihar Uttar Pradesh, inda al'ummar suka daɗe suna rayuwa cikin lumana.
An tsinci gawar Kajal - mai shekara 19 a duniya wadda ke bin addinin Hindu da ta saurayinta Mohammad Arman mai shekara 27 wanda Musulmi ne, a wani wuri da aka turbuɗe su kusa da gaɓar rafi a ƙauyen Umri, ranar 21 ga watan Janairu.
Ƴansanda sun ce an kashe su ne ta hanyar duka da cebur, kwana biyu kafin gano gawarwakin nasu, kuma ana zargin cewa ƴan'uwan Kajal, maza, su uku ne ke da hannu, kuma tuni an kama su.
Yanzu haka suna hannun hukumomi kuma ba su ce komai ba tukuna game da lamarin.
Wannan kisa da aka yi wa masoyan ta bar al'ummar ƙauyen Umri cikin kaɗuwa, wanda ke da nisan kilomita 182 daga birnin Delhi, babban birnin ƙasar.
Ƙauyen na ƙunshe da kimanin gidaje 400 - wadanda wasunsu Musulmai ne wasu kuma mabiya addinin Hindu.
Da dama daga cikin al'ummar ƙauyen sun shaida wa BBC cewar sun daɗe suna zaune cikin lumana da kwanciyar hankali da juna duk da bambancin addini.
Mataimakin sufetan ƴansanda na yankin ya shaida wa BBC cewa suna da yaƙinin cewa irin kisan nan ne na "kare mutuncin iyali" - inda dangi ko al'ummar ƙauye kan ɗauki mataki a kan mace a matsayin hukunci idan suka auri wanda ba addininsu ɗaya ba.
Hukumar tattara alƙalumar laifuka ta Indiya ta fara tattara alƙaluman irin wannan kisa ne a shekarar 2014, shekarar da ta ce an yi irin haka sau 18. Amma alƙalumanta na baya-bayan nan sun nuna cewa an samu irin wannan kisa sau 38 a shekarar 2023.
Sai dai masu hanƙoro sun ce adadin ya zarta haka sosai - ya kai ɗaruruwa - sai dai akan bayyana wasu a matsayin kisan kai.
Ƙauyen Umri na a wani yanki ne na jihar Uttah Pradesh wanda ya yi suna wajen kamfanonin ƙarafa.
Yanki ne na karkara inda ake bin tsari na al'ada wajen tarbiyya da tafiyar da rayuwa.
Wani mazaunin ƙauyen Mahipal Saini ya ce lamarin da ya faru da Kajal da mijinta shi ne irin wannan kisa na farko a ƙauyen.
Wasu mazauna ƙauyen sun ce tun asali Kajal da Arman sun kasance maƙwafta ne, kuma mutane ne wadanda ba su cika son hayaniya ba, saboda haka ba su da abokai ko ƙawaye da yawa.

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Kajal malama ce a wata makaranta da ke Umri, yayin da shi kuma Arman ya koma ƙauyen ne kimanin wata biyar da suka gabata bayan kwashe shekara huɗu a ƙasar Saudiyya inda ya yi aiki a matsayin mai sayar da abinci.
Ƴan'uwansa sun ce ya koma gida ne ganin cewa ba ya samun wasu kuɗaɗen a zo a gani a can Saudiyya, kuma tun bayan komawarsa ya riƙa aiki ne da wani kamfanin fasa dutse.
Babu cikakken bayani kan yadda ma'auratan suka fara soyayya, to amma ƴansanda sun ce "mutanen biyu sun kasance masu kusanci da juna sosai."
Sun ce ana zargin cewa an kashe ma'auratan ne a daren ranar 18 ko 19 ga watan Janairu, a gidan su Kajal, lokacin da Arman ya je wurin Arman. A lokacin ne yayyinta maza Rajaram da Satish da kuma Rinku Saini suka gudanar da aika-aikar.
Mahaifinsu Ganpat Saini ya shaida wa BBC cewa shi da matarsa ba sa gida a lokacin da matasan suka kashe Kajal da Arman
Ya ce sun kasance a wata bukka a gonarsu inda suke zuwa domin gadin dabbobinsu, inda ya fada cikin alhinin ƴarsa.
Yayan Arman, Farman Ali ya ce ɗan'uwansa Arman ya bar gida ne bayan cin abincin dare a ranar 18 ga watan Janairu, inda ya ce zai sayo wa iyayensu magani idan zai dawo gida.
Ya zuwa safiya, a lokacin da iyalansa suka ga bai dawo ba, kuma aka gaza samun shi a waya, sai hankalin iyalinsa ya tashi, kuma suka kai rahoto wurin ƴansanda. Wannan ne ya sa aka fara bincike domin gano shi a ƙauyen.
Ƴansanda sun kuma ce ƴan'uwan Kajal sun so su yaudari hukumomi ta hanyar kai rahoton ɓacewar ƴar'uwarsu a ranar 20 ga watan Janairu, inda suka zargi Arman da ɓoye ta.
Ƴansanda sun ce bayan da suka yi wa ɓangarorin biyu tambayoyi, sai suka gane cewa akwai rashin gaskiya a bayanin ƴan'uwan Kajal.
Bayan ƙara zurfafa bincike ne sai suka samu shaidun da suka kai su har zuwa inda aka binne mutanen biyu.
Ganpat Saini ya ce a lokacin da suka koma gida, shi da matarsa a ranar 19 ga watan Janairu, ba su iske ƴarsu a gida ba. Ya ce ba su san cewa an kashe ta ba ne har sai da aka gano gawarwakin.
Sai dai bai bayar da amsa ba lokacin da aka tambaye shi ko shi, ko wani a cikin iyalinsa ya san cewa Kajal da Arman suna soyayya.
A ɓangare ɗaya iyalin Arman sun ce ba su san cewa yana soyayya da Kajal ba.
"Bai taɓa faɗa mana komai ba," in ji yayansa Farman Ali. "Bayan rashin sanin inda yake na tsawon kwana ɗaya, sai wasu abokansa suka shaida mana cewa ai yana yawan zuwa wurin Kajal a tsawon watanni biyu da suka gabata."
Mazauna ƙauyen sun ce a kodayaushe aka samu saɓani, ana warware lamarin ne tare da taimakon shugabannin ƙauyen. "In da iyalin Kajal sun yi tunani mai zurfi, da dattawan ƙauyen sun warware matsalar," in ji wani mazaunin ƙauyen mai suna Mahipal Saini.

Ƴan sanda sun ce sun baza jami'ai domin tabbatar da cewa ba a samu ɓarkewar rikicin addini ba. Kuma mazauna ƙauyen sun ce sannu a hankali rayuwarsu na komawa kamar yadda aka saba.
Wasu na cewa, kisan ya haifar da wani yanayi mara ɗaɗi.
"Ba mu taɓa tunanin wani abu makamancin haka zai iya faruwa a nan ba," in ji Arif Ali, wani mazaunin Umri. "Ba wai maza da mata a ƙauyen sun fara fuskantar fargabar rashin tsaro ba, amma akwai waniu yanayi mara daɗi da ya kewaye mu baki ɗaya."
Kisan da aka yi a Umri ya shiga jerin kashe-kashe irin wannan da ake zargin "kisan kare mutuncin iyali" ne da aka ruwaito daga sassan Indiya daban daban cikin tsawon shekaru da dama.
Iyalai ne ke ''haɗa'' fiye da kashi 93 cikin 100 na auren da ake yi a Indiya kuma dangi kan haɗa ma'aurata ne daga cikin kabilarsu ko kuma addini kuma ma'auratan da suka kauce wa wannan al'adar ana tilasta musu neman kariya daga ƴan sanda ko kotu.
Dokokin Indiya sun ɗauki "kisan kare mutuncin iyali" a matsayin kisan kai kuma kotuna sun sha tabbatar da cewa zaɓin abokin tarayya ta hanyar amincewa ga babba wanda ya mallaki hankalinsa yana da kariya ƙarƙashin tsarin mulkin ƙasa. A shekarar 2018, kotun ƙolin ƙasar ta umarci gwamnatocin jihohi da su kafa matsuguni a kowace gunduma domin kare mabiya addinai da ma'aurata daga cin zarafi.
Amma duk da haka ana ci gaba da samun rahotannin rikice-rikice masu nasaba da aure daga jihohin ƙasar.
Bincike ya nuna cewa yawancin Indiyawa suna adawa da aure tsakannin mabiya addinai daban, kuma dokokin da ke haifar da cece-kuce game da canza addini da ake aiwatarwa a jihohi da dama kan sa irin waɗannan ma'auratan su shiga halin tsaka-mai-wuya.
Mai shirya fina-finai Nakul Singh Sawhney, wanda ya yi wani shiri a kan batun a shekarar 2012, ya ce babu isassun bayanai kan rahotannin kisan gilla.
"Yawancin shari'o'in ba sa kai wa ga shiga bayanan hukuma sai dai idan an ambaci dalili a fili a matakin farko na rahoton ƴan sanda. Kuma a yawancin lokuta, batun kisan kare mutuncin iyali ya kan bayyana ne daga baya yayin da ake gudanar da bincike," in ji Sawhney.
Mai fafutukar kare haƙƙin bil'adama Kavita Srivastava ta ce rashin amincewa da girman abin da ake kira laifukan kare mutuncin iyali yana haifar da halin ko in kula a hukumance. "Idan har ba a ga matsalar ba, ba za a magance ta ba," in ji ta.
Yayin da mata ke ƙara tabbatar da ƴancinsu na zaɓar abokan zamansu, Srivastava ta ƙara da cewa, galibi suna fuskantar turjiya daga abin da ta bayyana a matsayin "tsarin zamantakewa mai cike da koma baya".
Umurnin kotu, in ji ta, ita kadai ba za ta iya hana aikata"laifukan kare mutuncin iyali" ba sai an yi garambawul a wasu manyan halayen zamantakewa.











