Arsenal ba ta yi wa Arteta tayin sabon kwantiragi ba, Man United na son Eichhorn

Asalin hoton, Getty Images
Har yanzu Arsenal ba ta fara tattaunawa da kocinta Mikel Arteta kan sabon kwantiragi ba, yayin da dan ƙasar Sifaniyan zai rage sauran watanni 18 a kwantaraginsa daga watan janairu mai zuwa. (ESPN)
Manchester United ta bi sahun ƙungiyoyi da suka haɗa da Real Madrid da Barcelona da Paris St-Germain da Bayern Munich wajen fafutukar sayen ɗan wasan tsakiyar Jamus Kennet Eichhorn mai shekara 16, wanda Hertha Berlin ta ƙaƙabawa farashin fam miliyan 8.8 zuwa 10.5 . (Florian Plettenberg)
Everton da Fulham da West Ham, da Nottingham Forest suna sanya ido kan halin da ɗan wasan bayan Arsenal, Myles Lewis-Skelly ke ciki, bayan da kocin Ingila Thomas Tuchel ya ce ɗan wasan mai shekara 19 na buƙatar ƙara buga wasanni domin ya iya samun gurbi a tawagar ƙasar (Caught Offside)
Kocin Manchester United, Ruben Amorim, na son ya ci gaba da riƙe ɗan wasan tsakiya na Brazil Casemiro a ƙungiyar har bayan kwantiraginsa na yanzu, wanda zai ƙare a ƙarshen kakar wasa ta bana, muddin ɗan wasan mai shekara 33 ya rage albashinsa. (Talksport)
Fatan BorussiaDortmund na ci gaba da riƙe ɗan wasan baya Nico Schlotterbeck na raguwa sakamakon zawarcin Bayern Munich da Liverpool, yayin da ɗan wasan ƙasar Jamus mai shekara 25, ya nuna rashin jin dadinsa da salon wasan ƙungiyar. (Bild)
Ƙungiyoyin Premier da dama na sha'awar dawo da ɗan wasan gaban Ingila da Al-Ahli Ivan Toney, mai shekara 29, zuwa gasar ta Ingila amma albashinsa na iya kawo cikas. (Sky Sports)
Tottenham na cikin jerin ƙungiyoyin da ke zawarcin tsohon ɗan wasan Brentford Toney amma ta na ci gaba da sanya ido a kasuwa yayin da ta ke shirin sayen sabon ɗan wasan gaba a watan Janairu. (Talk).
Fulham na shirin bai wa kocinta Marco Silva sabuwar kwantiragi duk da wahala da ya fara a kakar wasa ta bana a Craven Cottage. (Ana buƙatar biyan kuɗi na I), na waje
Everton na son sayen sabon ɗan wasan gaba a kasuwar musayar ƴan wasa a watan Janairu, inda ɗan wasan gaban Manchester United Joshua Zirkzee, mai shekara 24, ke cikin jerin waɗanda za ta iya nema. (Sky Sports).
An bai wa dan wasan gaban West Ham da Jamus Niclas Fullkrug, mai shekara 32 izinin barin ƙungiyar a watan Janairu. (GiveMeSport).
Chelsea na tunanin miƙawa ɗan wasan tsakiya na Ecuador Moises Caicedo, mai shekara 24, sabon kwantaragi a matsayin ladar taka rawar gani a kakar wasa ta bana. (Sky Sports).
Tsohon kociyan Manchester United Erik ten Hag ya ki amincewa da karɓar muƙamin kocin Ajax. (NOS).











