Matsalar tsaro: Maƙarkashiya ake yi wa Tinubu - Akpabio

Lokacin karatu: Minti 3

Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya Godswill Akpabio, ya ce matsalar tsaro da ta karara tsananta a kasar, wata makarkashiya ce ake yi wa gwamnatin Bola Ahmed Tinubu, kan sauye-sauye da gwamnatin ke yi a kasar.

Akpabio ya bayyana hakan ne ranar Talata a Abuja, a lokacin kaddamar da sabuwar hedikwatar Hukumar Harajin Kasar a Abuja.

Ya ce: ''Ina tabbatar ma, Shugaban Kasa, mako biyu bayan ka ci zaben (2027), za a daina kai harin bambamai. Mutane na daukar nauyin kai harin ne domin kawar da hankalinka daga aikin da kake yi.''

''Kana kokari sosai duk da irin makarkashiyar da ake yi wa gwamnatinka,'' in ji shi.

Mista Akpabio, ya yi ikirarin ne kasa da da sa'a 24 bayan da Tinubu ya yi wata ganawa ta sirri da babban hafsan tsaro Janar Olufemi Oluyede da wani Janar na sojin Faransa a fadar shugaban kasar a Abuja.

Wasu majiyoyi da ke da kusanci da Shugaban kasar, sun bayyana ganawar ta ranar Litinin a matsayin wani mataki na tsaurara matakan shawo kan matsalar tsaron da addabi kasar a baya-bayan nan.

Tinubu ya yi ganawar ne mako uku bayan ya sanar da cewa Faransa ta amince ta samar wa Najeriya kayan aiki na soji da bayar da horo ga jami'an tsaron kasar da ke fafatawa da masu tayar da kayar baya a yankin arewa maso gabashin kasar.

Akpabio, ya yi kalaman ne sakamakon matsalar tsaro da ta addabi sassan Najeriya, ciki har da harin da jirgin saman yaki na sojin sama na Najeriya kai ranar Asabar, wanda ya hallaka farar hula akalla 100 a kasuwar Jilli da ke jihar Borno, harin da hukumomi suka ce an kai shi bisa kuskure, da kuma matakin da Amurka ta dauka na janye ma'aikatan ofishin jakadancinta wadanda aikinsu ba na wajibi ba ne daga ofishin jakadancinta da ke Abuja.

Amurkar ta kuma shawarci 'yan kasarta da su guji zuwa Najeriya a wannan lokaci saboda matsalar ta tsaro.

Najeriya dai na fama da matsalar tsaro daban-daban, musamman a yankin arewacin kasar, matsalar da ta hada da hare-haren Boko Haram a arewa maso gabas, da matsalar barayin daji da masu satar mutane domin karbar kudin fansa a arewa-maso- da kuma arewa-maso-tsakiyar kasar.

Haka kuma Mista Akpabio, ya kare shugaban hukumar zabe ta kasar, Farfesa Joash Amupitan, a kan zargin kalaman da aka danganta da shugaban na INEC, inda ake zarginsa da nuna goyon baya ga Tinubu, a shafinsa na X, a wani lokaci a can baya.

Akpabio ya yi watsi da zargin kalaman wadanda aka bankado, inda ya ce ko kadan kalaman ba su da wata alama ta nuna cewa na nuna bangaranci ne ga Tinubu, da jam'iyyar APC mai mulki.

Shugaban na Majalisar Dattawa, ya ce an yi wa kalaman na FarfesaAmupitan, fassara ta son-kai ne. Kuma ya yi su ne kafin ya kama aiki a matsayin shugaban INEC, a lokacin yana matsayin malamin jami'a kawai.

Ya ce: ''Kalamai ne da kowa zai iya yi domin nuna goyon bayansa ga duk wanda yake so.''

Amma kuma ya jaddada cewa, dole ne masu rike da mukami na hukuma su kasance, ba masu goyon bayan wani bangare ba, da zarar an ba su wani mukami na yi wa kasa aiki.

Ya kara da cewa: "To amma a duk lokacin da kake wani mukami, dole ne ka yi tunanin kasar baki daya da dukkanin al'ummarta. Kuma abin da suke yi kenan.''