Trump ya zama shugaban Amurka na farko da aka ɗauki hotonsa a gidan yari

...

Asalin hoton, FULTON COUNTY SHERIFF'S OFFICE

Donalad Trump ya miƙa wuya ba tare da nuna turjiya ba bayan bayan tsare shi na ɗan lokaci da aka yi a jihar Georgia inda ake yi masa shari'a bisa zargin yunƙurin sauya sakamakon zaɓen jihar a 2020, wanda ana ganin shi ne a karon farko da irin haka ta faru da wani tsohon shugaban Amurka.

An tilasta wa Mista Trump biyan dala 200,000 a matsayin kuɗin beli kafin sakin sa daga gidan kason na birnin Atlanta inda aka tsare shi na ɗan lokaci domin jiran yanke masa hukunci.

Daga baya dai Trump ya bayyana shari'ar da ake ma sa a matsayin "cin amana".

Ana ganin shi ne karo na huɗu da ake tsare Trump cikin wata biyar a jere a bisa zargin sa da aikata manyan laifuka, amma kuma karon farko da jami'an 'yan sanda suka bayyana hotonsa.

Tun a watan Janairun 2021 rabon da tsohon shugaban ya wallafa wani abu a shafinsa na X da aka fi sani da Twitter a baya.

Sai wannan karon inda ya wallafa a shafin nasa cewar: "Kutse a sha'anin zaɓe. Ba gudu ba ja da baya!".

Yanzu dai shugaba Trump ya shiga sahun fitattun Amurkawa da aka tsare su ta wannan hanya, waɗanda suka hada da Elvis da Frank Sinatra da Al Capone da kuma Dakta Martin Luther King.

Magoya bayan Trump, Marsha da Cathy a wajen gidan yarin yankin Fulton

Asalin hoton, reuters

Bayanan hoto, Magoya bayan Trump, Marsha da Cathy a wajen gidan yarin yankin Fulton

Mista Trump ya daɗe ya na bayyana cewa shari’ar da ake yi masa akwai bi-ta-da-ƙullin siyasa a ciki saboda kawai ya na jagorantar jam’iyyar Republican inda zai ƙalubalanci shugaba Joe Biden na jam’iyyar Democrat a zaɓen shekara mai zuwa.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Shi ne tsohon shugaban ƙasar na farko da aka taɓa ɗaukar hotonsa a matsayin fursuna a ranar Alhamis, inda aka zarce da Mista Trump zuwa gidan yarin Fulton a cikin wata mota kuma abin da gaba ɗaya ya sha bamban da bayyanarsa a gaban kotu.

Ya ɗauki tsawon minti 20 a tsare, yayinda gomman magoya bayansa suka tattauru a harabar gidan gyara halin da aka ɗaure shi.

Bayanan da aka wallafa a shafin yanar gizo na gidan yarin sun bayar da cikakkun siffofin Trump da aka ce yana da tsawon ƙafa 6 da inci 3 da nauyin da ya kai kilogiram 97; mai gashin kai launin ruwan ƙwai da shuɗin ƙwayar ido. Sai kuma lambarsa a matsayin fursuna kamar haka: P01135809.

An gan shi jikinsa a sanyaye a cikin gidan yarin na Atlanta, wanda ya yi suna kan tsare masu aikata miyagun laifuka.

Da aka sake shi lokacin da ya ke kan hanyar komawa gida ya yi jawabi ga magoya bayansa a filin jirgin sama, inda ya ce har yanzu fa ya na da hakkin ƙalubalantar sakamakon zaɓen.

“A gani na fa an yi maguɗi a zaɓen, an sace ƙuri’a”, in ji Trump, wanda ya yi suna wajen ƙorafi a kan cika akwatunan zaɓen shekarar 2020 da ƙuri’un bogi.

“Dole in bi hakkina kullum dare da rana".

“Kamar yadda kuka sani ne, kuna da mutane da dama da kuka sanyawa ido tsawon shekaru domin aikata irin haka, ko dai Hillary Clinton da Stacey Abrams ko wasu da dama”.

A makon jiya ne aka tuhumi Mista Trump tare da wasu mutum 18 da ake zargi da hannu a ƙoƙarin sauya sakamakon zaɓen Georgia biyo bayan shan kaye da ya yi daga hannunMista Biden da ratar da ta kai ƙuri’a 12,000 a jihar.

A wata hira da Trump ya yi ta wayar tarho wadda ta fito fili, an ji shi yana matsain lamba ga babban baturen tattara sakamakon zaɓen Georgia da ya “nemo ƙuri’a 11,780” a daidai lokacin da ake tsaka da ƙirga ƙuri’un.

Daga cikin zarge-zarge 12 da ake yi ma Trump sun haɗa maguɗi da amfani da jama’a da ya kai ga karya rantsuwa domin kare ofishinsa da haɗin baki don yin yaudara da kuma bayar da bayanan ƙarya.

Sai dai ya ƙaryata duka waɗannan tuhume-tuhumen da ake yi kansa.

Rabin waɗanda ake zargii da hannu a mara wa Trump baya su ma an tsara aika su gidan gyara halin da suka haɗa da tsohon Magajin Birnin New York Rudy Giuliani da tsohon shugaban ma’aikatan fadar White House, Mark Meadows da sauran su.

Daga ciki sharuɗɗan da aka gindaya wa Trump kafin bayar da belin sa sun haɗa da daina wallafa kowane irin bayani a shafukan sada zumunta da za su iya zama barazana wajen tilasta shaidu bayar da bayanan da ba na gaskiya ba. Haka ma an nemi ya kauce wa kowace irin mu’amala da su kai tsaye, sai dai ta hanyar amfani da lauyoyinsa.

Kafin isar sa Georgia Mista Trump ya yi suka ga babbar lauyar da ta shigar da ƙarar da ake yi wato Fani Willis, wadda kuma ‘yar jam’iyyar Dimokurat ce, da ya zarga da yi masa kutungwila a yaƙin neman zaɓen sa da ya hana masa shiga fadar White House.

A cikin bayanan da ya wallafa ya zargi Mis Willis da laifin kisan kai da tayar da hankali a Atlanta, in da ya rubuta, [hakan] "ya sa mutane na fargabar fita waje sayen guntun burodi”.