Tsibirin da aka fi girmama likitocin gargajiya saboda cire aljanu da karya sihiri

Asalin hoton, Simon Urwin
- Marubuci, Simon Urwin
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Travel
- Lokacin karatu: Minti 4
Tsibirin Siquijor na musamman ne - ba a Philippines ba kawai, har ma a nahiyar Arewa maso gabashin Asiya, wanda aka sani da tsafi, da maganin gargajiya tun shekaru aru-aru.
Siquijor da ke tsakiyar yankin Visayas, na jan hankalin matafiya 'yan Philippines da dama, ciki har da mazauna ƙasashen ƙetare da ke zuwa don gane wa idonsu da kuma samun magani.
An kafa wurin tun a ƙarni na 16, inda ake bai wa maziyarta jiƙe-jiƙe, waɗanda aka yi imanin suna sukan warkar cutuka (duk tsananinsu). An yi imanin abubuwa uku ne ke jawo cutukan da ake iya warkarwa a wurin.
"Abu na farko shi ne fusatattun aljanu a duniya," a cewar ɗanjagoran wurin Luis Nathaniel Borongan. "Aljanu na kewaye da mu, a wuraren zubar ruwa, da dazuka, da koguna. Idan muka matsa musu za su iya saka mana cuta a matsayin ramuwa, ko ma su halaka mu."
Abu na biyu kuma, in ji Borongan, maita ce ke haddasa shi. "Akwai na'uka da dama, kamar asiri, da jifan mutum da wata cuta."
Na ukun kuma wanda shi ne mafi sauƙi, shi ne "abin da ke faruwa haka kawai", kamar mura da sauransu, waɗanda akan warkar da su da zarar an ziyarci masu wurin.
An yi imani sosai da maganin gargajiyar tsibirin - ta yadda Siquijor ya fara jawo hankalin mutane daga nesa da ƙasar ta Philippines.
Da zarar sun isa yankin, matafiya kawai sai su nemi direban tasi, "nan take za su nuna maka wurin," in ji Borongan.

Asalin hoton, Simon Urwin
Tsibirin da ake girmama likitocin gargajiya
Mazauna tsibirin Siquijor kan je wurin malaman gargajiya fiye da yadda suke zuwa asibiti. "A lokuta da dama malaman kan yi nasara a inda likitoci suka gaza," a cewar Borongan.
Suna yawan bai wa mutane magungunan gargajiya. "Sukan haɗa magunguna daga ganye iri-iri kusan 300 da aka shuka a tsibirin. Harhaɗa magunguna daga ganye na daga cikin abin da ya sa mazauna tsibirin ke ƙara amincewa da maganin tsawon shekaru."
A daɗe ana yi...
'Yan yawon duniya na Sifaniya Juan Aguirre da Esteban Rodriguez ne Turawan farko da suka je Siquijor a 1565. Bayan sun hango tsibirin daga nesa da tunanin wuta ce, sai suka ba shi sunan Isla de Fuego (Tsibirin Wuta).
"Wutar na tashi ne daga bishiyoyin molave," in ji Borongan. "Wannan abu da ke faruwa haka kawai (wanda yanzu ya yi ƙaranci), ƙila shi ne abin da ya sa Siquijor ya shahara da tsafi, da kuma dalilin da ya sa wasu maƙwabta ke fargabar zuwa nan ɗin."

Asalin hoton, Simon Urwin
Wurin da ake haɗa addinin shamanism da ɗariƙar Katolika suka gauraya
Ƙasar Philippines ta koma bin ɗariƙar katolika a 1521 a hukumance, amma 'yan mishan ba su je tsibirin ba har sai shekarun 1700, ƙila saboda jita-jitar tafi. "Amma tuni mazauna wurin suka tsumi da al'adu yadda 'yan mishan ba su iya sauya hakan ba," kamar yadda Borongan ya faɗa.
"Amma daga baya, addinan biyu sun dunƙule: masu maganain sun fahimci cewa baiwarsu ta zo ne daga abin da suke kira Allah; sai suka koma amfani da alamun addini."
Magungunan soyayya, da sha'awa, da nasara
Ana iya sayen magungunan gargajiya hatta a gefen titin tsibirin da pesos 100. Daya daga cikin mafiya shahara shi ne maganin soyayya, wanda aka haɗa da ganye 20.
"Yana alamta kiran mutum," in ji Lilia Alom, wata mai haɗa magani tsawon shekara 30. "Yana sa a ji kamar 'zo wajena', ko da zimmar soyayya ko kuma sa'a kawai."
Amma Alam ta ce maganin ba shi jawo mutum ya so wani har abada.

Asalin hoton, Simon Urwin
Saduwa da iyaye da kakanni
Tigi ɗaya ne daga cikin abubuwan da ake yi wajen magance cutukan da shaiɗanun wata gawa ke haddasawa.
Mai magani Pascal Ogoc kan yi amfani da sanda wajen tsarkake gawar mutum - "sandar za ta lanƙwashe ko kuma ta ƙara girma idan aka kira sunan mutum da ƙarfi," in ji shi - kafin ya sadu da kakanninsa.
"Suna yawan ce min ba su jin daɗi saboda ana yawan mantawa da su," a cewar Ogoc.
Maganin mai sauƙi ne: mutumin da abin ya shafa zai ba da abin sadaka ga malamin sai a yi masa addu'a a madadin wanda ya rasun don a warkar da su.
Cire aljanu da warware sihiri
Ruhelio Lugatiman ɗaya ne daga cikin waɗanda suka rage a bolo-bolo. Akan cika kwalaba da ruwa, da tsinke da kuma wani dutse na sihiri. Sai a hura ruwa yayin da ake zagaya kwalabar a kan maras lafiyar; dutsen zai karya sihiri da cire aljanun.
Lugatiman ya ce ya ga abubuwa da yawa kamar fara (da aka turo wa wani) da kuma allura da ake cire wa mutane lokacin addu'ar. Za a ci gaba da yin hakan har sai ruwan ya dawo daidai, abin da ke nuna samun waraka.
Kai wa mutane sauƙi
Masu maganin ba su karɓar kuɗi daga wajen mutane sai dai abin sadaka. "Abu ne na kula da al'umma, ba don a samu kuɗi ba; rayuwarmu mai sauƙi ce," a cewar mai magani Juanita Torremacha.
Saboda haka ne adadin mutanen da ke zuwa suka ragu a 'yan shekarun nan. Domin sauya lamarin, sai aka koma yin bikin magani na Siquijor na shekara duk sati tun daga 2006 a wurin shaƙatawa na Mt Bandilaan National Park. Ana maraba da kowa da kowa.
"Kowa zai iya haɗa maganin da yake so don jin daɗinsa a wurin," in ji Borongan. "Muna so mu nuna cewa ba 'yan damfara ba ne, maganinmu na da tasiri sosai tsawon shekaru, kuma shi ne ya sa Siquijor ya zama daban. Ba za mu so mu rasa wannan sihirin ba."











