Hanyar ƴan ci-rani mafi hatsari da hankalin duniya bai kai gare ta ba

- Marubuci, Priya Sippy
- Lokacin karatu: Minti 5
Mohammed Abdullahi Mohamud, mai shekara 35, na tuna bulaguro mai cike da hatsari da ya yi cikin ƙaramin jirgin ruwa daga Djibouti zuwa Yemen lokacin yana matashi mai jini a jika.
Kamar sauran matasa irinsa, ya ƙudiri aniyar barin ƙasarsa Somaliya domin nema wa kansa rayuwa mai inganci a ƙasashen waje.
Bulaguro daga Afirka zuwa Yemen na ɗaya daga cikin hanyoyin da ƴancirani suka fi bi a duniya, sai dai da alama har yanzu hankalin duniya bai kai gareta ba.
Haka kuma hanyar ta kasance cikin mafiya hatsari, kamar yadda Mohammed ya fuskanta.
"Minti 30 da fara tafiyar, jirgin ruwan da muke ciki ya fara tangal-tangal," in ji shi.
"Masu fasa ƙwaurin mutane ƴan Yemen suka fara magana cikin harshen Larabci, suna cewa za su hantsular da mutane cikin teku. Ba a jima ba suka tura wasu ƴan Ethiopian bakwai cikin teku."
Duk da hatsarin da bulaguron ke tattare da shi, dubban matasa ƴancirani ne ke yinsa a kowace shekara.
Ƙungiyar MMC, mai kula da zirga-zirgar ƴancirani a duniya ta yi ƙiyasin cewa kusan mutum 100,000 ne daga Afirka ke isa Yemen a kowace shekara, inda mafi yawansu ke zuwa daga ƙasashen gabashin Afirka, musamman Ethiopia da Somaliya da Djibouti.
A cikin jirgin da Mohammed ya hau, akwai ƴan Ethiopia 47 sai ƴan Somaliya biyar da masu safarar mutane ƴan Yeman su biyu.
"Yanayi na tashin hankali da ɗimuwa," in ji shi.
"Ruwa na shigowa cikin jirgin. Mun riƙa amfani da hannayenmu wajen kwashe ruwan daga cikin jirgin. Ba mu san ko hakan zai taimakemu ba,'' in ji shi.
Tun 2014 Yeman ta fara faɗawa yaƙin basasa, lamarin da ya sa ƴanciranin ƙasar da dama ke tuɗaɗa zuwa Saudiyya inda ake da buƙatar ayyukan leburanci.
A yayin da tattalin arziki ya kasance dalilin ƙaurar jama'a, hukumar kula da ƴancirani da duniya (IOM), ta ce ƙaruwar ƴancirani daga ƙasar Ethiopia musamman yankunan Amhara da Oromia, na faruwa ne sakamakon yawaitar rikice-rikice, da tashin hankalu da kuma muzgunawa.
Bulaguro ta Djibouti ko Somalia

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Akwai tagwayen hanyoyin da ƴancirani ke bi a yankin tekun Aden.
Ko dai su bi ta Obock a Djibouti zuwa Lahij, wani gari da ke kudu maso yammacin Yemen, ko kuma su bi ta Bossaso a Somalia zuwa Shabwah, gaɓar ruwan kudu maso gabashin Yemen.
Amma shi Mohammed ya bi ta duka hanyoyi.
Bulaguronsa daga Djibouti zuwa Lahij ya ɗauki tsawon sa'a biyar.
A 2014, bayan ya koma Somaliya, ya kuma koma Yemen inda ya bi da Bosaso.
"A wannan karon ban tsorata sosai ba saboda tafiya da ta gabata da na bi da Djibouti. Amma dai ta iyu ta fi tsayi, ta ɗauke mu kwana guda kafin mu isa Yemen,'' in ji shi.
A cewar ƙungiyar IOM, Djibouti ce zango na farko ga masu son zuwa Yemen. Ƴanciranin Ethiopia kimanin 106,000 ne suka shiga ƙasar a 2023.
Isa wurin da ake ya da zango a Djibouti na da matuƙar hatsari, kuma yakan ɗauki makonni. Ga waɗanda ke zuwa daga yankin Amhara na Ethiopia, zuwa Oback bai fi kilomita 400 ba.
Yayin da wasu ƴan ciranin ke hawa ƙananan motoci da na bas-bas, da dama kan tafi da ƙafarsu, inda suke ratsa sahara cikin tsananin zafi. Yanayin zafi kan kai maki 50 a ma'aunin salciyos musamman a lokacin bazara.
A lokacin da suka isa gaɓar teku, mutanen kan biya masu safarar mutane kudi kimanin dala 300 domin ƙetarawa da su tekun Aden.
Ayla Bonfiglio, shugabar ƙungiyar MMC a yankin ta ce safarar mutane ya zama babbar sana'a.
"Idan muka lissa dala 300 sau kimanin 100,000, adadin ƴanciranin da ke ƙetarawa a kowace shekara, muna maganar wajen dala miliyan 30.''
Cikin shekara 10 da suka gabatam hukumar IOM ta yi ƙiyasin cewa ƴan cirani 1,400 ne suka mutu sakamakon nutsewa a ruwa. Amma Bonfiglio ta yi imamin cewa wannan adadi ka iya zarta harka.
"Mutane da dama na ɗaukar hanyar gabashi a matsayin mafi hatsari a nahiyar,'' in ji shi.
"Duk wani ƙetare teku da ya saɓa ƙa'ida yana ƙunshe da amfani da jirage marasa inganci wajen ƙetarar da jama'a,'' in ji ta.
Ƴancirani kan fuskanci cin zarafi da uƙuba

Asalin hoton, Getty Images
Ba tsallake tekun ne kawai ke da hatsari ba.
Bonfiglio ta ce ƴanciranin kan fuskanci uƙuba a hannun masu safara da masu fasa-ƙwaurin mutane.
"A shekarar da ta gabata mun gudanar da bincke kan ƴancirani 350, kuma kusan dukansu sun gaya mana cewa sun faɗa tarkon masu fasa-kwaurin mutane,'' in ji ta.
"Da dama sun ce waɗanda suka yi fasa-ƙwaurinsu sun gallaza musu, ta hayar duka, da sacewa k ƙwace guzurinsu,'' in ji ta.
Ta kuma ce ƴanciranin Afirka na faɗawa hatsarin uƙuba, ko da sun isa inda suke son zuwa, mafi yawanci a Saudiyya, amma a karon farko suna fuskantar hatsarin rikicin Yemen.
"Rikicin Yemen ne hatsari mafi girma a bulaguron namu,'' in ji Mohammed.
Ya tuna tafiyar ƙafa da ya yi ta kwana 11 daga Yemen zuwa Saudiyya bayan yaƙi ya ɓarke. Ya tsallake ƙasar da abinci da ruwa ɗan ƙalilan.
"Daya daga cikin matan da muke tafiyar da su ta mutu sakamakon yunwa da ƙishirwa a kan hanya,'' in ji ta.
Ƙasar Saudiyya ta yi yunƙurin dakatar da ƴancirani daga shiga ƙasar. A 2023, ƙungiyar kare haƙƙin bil'adama ta Humar Right Watch (HRW) ta bayar da rahoton cewa jami'an tsaron kan iyaka sukan kashe ɗaruruwan ƴan Ethiopia da masu neman mafaka da ke ƙoƙarin shiga ƙasar daga kan iyakar Yemen.
Ƙungiyar HRW ta ƙiyasta cewa kusan ƴan Ethiopia 750,000 ne yanzu haka ke Saudiyya, inda dama ke ayyukan gida da leburanci.
"Aiki ne mai ƙunshe da uƙuba, ta yadda ƴanciranin ba su da wani ƴanci,'' in ji Bonfiglio.
"Suna fuskantar kamawa da tsarewa idan an kama su.''
"Yawanci sukan zauna a ƙarƙashin ƙasa saboda rashin halasta zamansu a Saudiyya.''
Akan mayar da ƴanciranin da hukumomin Saudiyya suka kama zuwa ƙasashensu.
Bayan kwashe shekara biyar yana aiki a Saudiyya, an mayar da Mohammed gida a 2021.
A can gida Mogadishu, yanzu Mohammed na sana'ar acaɓa domin kula da matarsa da ƴaƴansa biyar.
Ya ce duk da bai ji daɗin komawa Somaliya ba, ba zai shawarci wani ya jefa rayuwarsa cikin hatsari kamar yadda ya yi ba.
"Shawara ita ce kowa ya yi iamni da ƙasarsa ya kuma yi haƙuri, saboda irin bulaguron nan ba shi da amfani,'' in ji shi.











