Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Abin da muke yi don ceto mutanen da aka sace a Kajuru - Uba Sani
Abin da muke yi don ceto mutanen da aka sace a Kajuru - Uba Sani
Gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani ya je ƙauyen na Kurmin Wali da ke jihar Kaduna, kwana uku bayan harin da aka kai, inda aka sace mutane kimanin 170.
"Ba za mu iya kwashe su daga ƙauyen ba, saboda dole ne za su ci gaba da zuwa gonakinsu...amma domin kare su a nan gaba, wajibi ne a samar da sansanin sojoji a tsakanin ƙauyen da dajin Rijana," kamar yadda gwamnan ya bayyana wa BBC.
Ya kuma ce jami'an tsaro na ci gaba da ƙoƙarin ganin sun ceto mutanen da aka sace.