Yadda ake cin zarafi da kashe ƴan Ghana a jiragen ruwan China

Asalin hoton, Bright Tsai Kweku
Idan ana magana kan cin zarafi da cin hanci da rashawa a kan jiragen ruwa na kamun kifi mallakin ƴan China da ake aiki da su a Ghana, to babu abin da Bright Tsai Kweku bai gani ba.
Ya kasance mai yi wa wasu mutanen China aiki a matsayin masunci inda suka mayar da shi tamkar "bawa", a cewar sa.
Mr Kweku ya ce "suna daukar shi, su tsarta masu yawu, su kuma haure su da kafa.
"Na fuskanci hakan nima in ji Mr Kweku ya yi aiki a mastayin mai kula da kayan aiki da matukan jirgi.
Ya ce an tursasa masa yin aiki har na tsawon kwana uku ba tare da bacci ba, an hana shi abinci, sannan an tilasta masa shan ruwa mara tsafta.
Makomar wasu daga cikin abokansa masunta, ya fi nasa muni, a cewar sa.
Mr. Kweku ya ce daya daga cikin abokan aikinsa ya taba kamuwa da cutar amai da gudawa a kan jirgin ƴan China, amma masu jirgin suka ki dawo da shi gabar teku domin a duba lafiyar sa.
Ya kuma sake ganin wani wanda ya yi wata mummunar konewa a kan jirgin, bayan da wata gobara ta tashi a jirgin.
Wani kuma abokin aikin farfelar jirgin ce ta kama shi.
Dukkan su babu wanda ya rayu, kuma ba a biya iyalansu diya ba, a cewar sa.
Wadannan kadan ne daga cikin misalai na irin zarge-zargen da ake yadawa na
cin zarafi da wariyar masuntan China ke aikatawa a teku, a gabar ƙasar Ghana.

Asalin hoton, EJF
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Kungiyar rajin tabbatar da adalci kan harkokin muhalli ta EJF da ke Birtaniya ta ce aƙalla kashi 90 cikin dari na kamfanonin da ke kamun kifi a Ghana mallakin ƴan ƙasar China ne, a ƙarkashin dokar mallakar jirgin ruwa ta Ghana.
Akwai dai adadin mai yawa na wadannan jiragen ruwa da ake zarginsu da aikata laifuka, a cewar EJF.
Wani rahoton EJF na bincike ya ce haramtattu ne, da ba a san da zaman su ba, kuma suna aiki ba bisa ƙai'da ba, da take haƙƙin dan Adam da kamfanin kamun kifi na China a Ghana ke yi.
Kamfanin da ke kula da kamfanin kamun kifin na China DWF na daya daga cikin manyan kamfanoni kamun kifi a duniya.
Dukkan ma'aikatan jirgin 36 da EJF ta yi hira da su an tilasta masu yin aiki na sama da awa 14 a rana, ba tare da samun abinci a kan kari ba.
Kashi 94% ba su samu magani yadda ya kamata ba, ko an zage su.
Kashi 86% sun koka kan rashin wajen zama mai inganci.
Kashi 81% an ci zarafin su.
Kashi 75% sun samu munanan raunuka a kan teku.
A wani martani, ofishin jakadancin China ya ce suna "kamun kifi cikin mutuci".
"Mukan yi aiki da sauran ƙasashen duniya domin kawo karshen haramtattun ayyuka, da kamun kifi ba bisa ka'ida ba da ake yi, kuma mun yi ƙoƙari sosai domin yaƙi da kamun kifin ba bisa ƙa'ida ba, a cewar ofishin yaɗa labarai na jakadancin, kamar yadda ya sanar da BBC.
Ɗaya daga cikin mummunan bala'in da ya shafi jirgin ruwan China a kan ruwa a Ghana ya faru ne wata takwas da suka gabata.
A ranar 6 ga watan Mayu, jirgin ruwan MV Comfort na biyu ya nutse a cikin ruwa sakamkon iska mai karfi.
An ceto mutum 14, 11 kuma sun ɓata, ko sun mutu, ciki har da wanda ke sanya ido a kan wadanda ke cikin jirgin.
An gano matuƙin jirgin dan ƙasar China.
Ɗaya daga cikin wadanda suka rayu, da ya bukaci mu sakaya sunansa, kuma za mu kira shi da Micheal, ya tuno irin abin da ya faru a wannan ranar.
Ya ce duk da cewa a lokacin da abin ke gab da faruwa ƙarfin da iskar na ƙara munana, ɗaya daga cikin 'yan China ya umurci masu kamun kifin, inda ya ce su tura daya daga cikin su ya janyo abin da ake ajiye kifin da ƙarfi.
Kwalekwalen na ɗauke da kifi mai yawa, wanda hakan ya sa ya kwace, ya kuma juye.

Michael da wasu mutum tara suka yi kokari suka maƙale a wani diram ɗin mai na tsawon awa 24, kafin daga bisani masunta su gano su.
Ya ce "dare ne mai tsoratarwa." " Ba mu yi tunanin za mu rayu ba, ko akasin haka ba."
Michael bai gama wartsakewa daga hadarin ba, ya ce har yanzu masu kula da jirgin mallakin kamfanin Boatcom na Ghana ba su biya shi wata diyya ba har yanzu.
Ya ce "Ban ji dadi ba ko kadan, kamfanin sai uzuri yake ta ba mu. Wani lokacin nakan ji ciwo a rai na, ina bukatar kulawar likita a yanzu, amma ba ni da kudi."
Kojo Ampratwum, shi ne shugaban kamfanin Boatcom, ya shaida wa BBC cewar kamfaninsa ya aika da rahotonsa ga kamfanin inshora, yana kuma jiran ya ji daga gare su.
Sai dai gano wanda ke da mallakin MV Comfort 2 da ke gudanar da harkokinsa a Ghana abu ne mai sarƙaƙiya.
Hakkin mallakar jiragen ruwa mallakin kasashen waje da ke aiki a ƙarƙashin Ghana, haramtacce ne, amma sai wasu daga cikin kamfanonin China kan bi ta wasu hanyoyi domin samun wasu kamfanonin na Ghana su shige masu gaba.
Sai dai a wani bincike, EJF ta ce kamfanin kamun kifi na China na Dalian Mengxin, shi ne ke da hakkin mallakar MV Comfort 2, kuma yana ɗaya daga cikin jiragensu na Meng Xin.
Haka kuma shi ma Meng Xin, an alaƙanta shi da kasancewa daya daga cikin wadanda ake kokawa a kan su, kan irin ayyukan suke aiwatarwa a kan ruwan da ke gaɓar Ghana, musamman game da ɓatar mai sanya ido kan masunta Emmanuel Essien.

Asalin hoton, James Essien
Tun 2018, ta samar da mai sanya ido kan masu kamun kifi, akan dukkan wani jirgin kamun kifi da ke harkokinsa a kan ruwan Ghana.
Aikin su shi ne tattara bayanai kan dukkan harkokin kifi da aka yi, da kai rahoton dukkan wasu haramtattun kamun kifi da aka samu kan teku.
Essien ya samawar da kan sa suna, saboda yadda ya jajirce wajen sa ido, amma hakan ya janyo masa matsala.
Ya taɓa faɗa da wani ɗan China, da ya taɓa hana shi ci gaba da daukar bidiyon ma'aikatan jirgin, da ke jefa kifi ta haramtacciyar hanya, cikin ruwa, a cewar ɗan uwansa James Essien
Rahoton Emmanuel na ƙarshe ga hukumar kula da harkokin kamun kifi shi ne a ranar 24 ga Yunin 2019.
A rahoton, da ya bai wa BBC, ya zayyana irin haramcin da ke faruwa a harkokin kamun kifi a kasar: "na roƙi 'yan sanda da sun ƙara zurfafa bincike kan lamarin.
James ya ce dan uwan nasa ya ci abinci tare da su, da sauran ma'aikatan jirgin, kafin su koma dakunan su don yin bacci.
Washegari suka neme shi ko sama ko ƙasa.
Sama da shekara uku, har yanzu iyalansu ba su samu amsa ba.
Wani rahoton 'yan sanda ya gano "babu wata alamar rikici ko wani abu mai kama da cin zarafi."Ina son gaskiya ta fito, kamar yadda James ya sanar wa BBC cikin kuka.
Sai dai mun kasa samun kamfanin kamun kifi na Meng XIN don jin ɓangarensa kan zargin.

Ɓatan Essien na ɗaya daga cikin batutuwa masu yawa da ke jefa tsoro ga masu sanya idanu kan harkokin kamun kifi a Ghana.
Masu sanya ido a Ghana da suka yi magana da BBC sun ce akwai ɗabi'ar tsoro, da cin hanci da wariya da ke tilasta musu karɓar cin hanci da rashawa, don ɓoye, irin haramci da cin zarfin da ake yi a jirgin China.
Mafi akasarin abokan aiki na karɓar kuɗi, a cewar wani mai sanya ido, wanda ya nemi a sakaya sunan sa, za mu kira shi da Daniel.
"Ana ba su cin hanci, kuma suna karɓar kuɗi daga hannun ’yan China, inda suke mika wa ma'aikata rahoton da babu gaskiya a cikin sa.
"Idan ka ki karɓar cin hanci, za ka koma gida da yunwa," a cewar wani mai sa ido kan masunta da ake kira Samuel." Mafi akasarin masu sanya ido na karɓar cin hanci.
"Abin da muke yi kenan wajen kula da iyalansu. "Wasu na cike da tsoro su fadi gaskiyar abin da ke faruwa."A wasu lokutan abin da suke yi shi ne suna jifan masu sa idon da ruwa, don ya taɓa faruwa a baya, a cewar Sameul.
"Saboda tsoro, bama sanar da irin wadannan lamura gaba gaɗi."

Asalin hoton, EJF

Asalin hoton, EJF
Steve Trent, shine shugaba kuma wanda ya samar da ƙungiyar EJF, ya ce adadin China na kaso mai yawa na mallakar kamfanin jiragen ruwa na kamun kifi masu yawa matsala ne a Yammacin Afirka, inda ake zargin su da yi wa dokokin karan tsaye.
Amma a Ghana, matsalar "ta daban ce" a cewar sa.
"Yan China sun saka dan uwansa dan china ya kula da jiragensu don ya bai wa 'yan Ghana umarni, kuma dan China da aka bai wa jagorancin shi ne ke cin zarafin, in ji Mr Trent.
Yayin da babu wani ci gaba wajen haramta kamun kifi a Ghana, Mr Trent ya ce akwai bukatar a ƙara ruɓanya ƙoƙari.










