Mulki ya zo ƙarshe, shekaru 70 ba tare da gajiyawa ba

Kofa ta rufe, bayan shekaru 70 tana mulki

Fuskar sarauniya cike da murmushi

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Sarauniya Elizabeth ta II

Tambari zai tsaya cak na minti biyu, masu busa sarewar masarauta za su yi shiru, za a ci gaba da tafiya da basarakiyar har zuwa kushewarta.

A yau Litinin din nan, komai zai tsaya cak babu motsin komai da zarar an kawo karshen addu'o'i a Westminster Abbey, kafin a rera taken kasa, a dauke akwatin gawar zuwa kushewar karshe da za a binne ta a Fadar Windsor, shiru zai ci gaba da yin jagora.

Shi kenan, zamanin Sarauniya ya zo karshe, komai ya tsaya kuma sauyi zai maye gurbin abin da aka baro a baya.

Zamanin mulkin shekaru 70 ya zo karshe, an rufe wannan babin. Kusan kwanaki 10 babu abin da muke yi sai batun Sarauniya, da sabon sarki, tamkar duka biyun za su ci gaba da kasancewa da mu a raye.

A yau mun kawo wannan makon mai tsawo, wannan makon mai cike da tashin hankali da damuwa.

A farkon fara sarauta, an bude babin mulkin Elizabeth tun tana karama, ta zama mai jiran gado. Lamari ne mai cike da zakwadi da jin dadi ga matashiyar sarauniyar, ta ga yadda zamani ya dinga sauyawa har zuwa zamanin fasaha.

Matashiyar da tana cikin kuruciya akai yakin duniya na biyu, ta kuma yi sadaukarwa a lokacin, tashin hankali da bakin cikin da suka biyo bayan shekarun yaki.

Komai ya yi farko yana da karshe, zamanin Elizabeth ya zo karshe, an rufe littafinta, sai dai a tarihi.

Tana nan daram-dam, a gwamman shekarun da aka dauka zamani na sauyawa, a kasa ra'ayin 'yan mazan jiya.

Sannu a hankali, za a daina ganin suna da hotonta a jikin muhimman abu kamar tambari, an daina jin muryar nan mai dadin sauraro lokacion aikawa da sakon murnar bikin Kirsimeti, babu mai sunkuyar da kai kasa a ranakun Lahadi lokacin addu'a.

Sannu a hankali, a yau Litinin an rufe dukkan kofofin.

Sun kuma bude ga Yarima Charles, da ya shafe sama da rabin shekarunsa a matsayin Yariman Wales.

Wadanda ke aiki da shi na masa kallon mutumin da ya kai kololuwar cancanta, ta fuskar nasarar da ya yi a ayyukan da ya sanya gaba, ciki har da na jin kai, ya dauki shekaru masu yawa yana ginin rayuwar da ta riske shi.

Sarauniya cike da murmushi
Bayanan hoto, Wani bangaren rayuwar Sarauniya da ba a a gani, amma ya na nan binne a fuskarta bai je ko ina ba
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Kalubalen farko da zai fara fuskanta bayan an gama zaman makokishi ne yadda zai nuna yana jin dadin aikin da yake yi, yana kuma jin dadi sarautar.

Mahaifiyarsa ta gane komai game da aikin, aikin sadaukarwa ne ga al’umma, a sama wa jama’a sassaucin rayuwa, korafin ‘yan uwa, masu dadi da marasa dadi, rayuwar dai babu yabo babu fallasa.

Za a so ganin ya taka irin rawar da ya yi a lokacinsa na Yarima mai jiran gado, sauye-sauyen da ya kawo, nauyi ne mai girma da ya hau kansa.

A yanzu kofa ta rufe a matsayin shin a Yariman Whales, a yanzu wata babba ce ta bude ta matsayin sarki mai cike da karfin iko.

Birtaniya za su so ganin jajirtaccen mutuum a matsayin mai haska musu fitilar rayuwa.

Yayin da shiru ya ziyarci duk wata kusurwa, lungu da sakon babban dakin taro na Westminster, kofa ta rufe, zamanin mulkin Sarauniya Elizabeth, ya zo karshe wadda ta yi fice da tambari a duniya, ita kuma ba duka ta sani ba.

Wannan shi ne ya kawo karshen zamanin mulkin wannan yarinya, da lokacin ta na karama babu wanda ya yi zaton za ta kawo wannan matsayi, abinda kawai aka sani shi ne yarinya Lilebet, mafi soyuwa ga kakanta.

Cikin shiri na musamman na BBC mai suna The Unseen Queen a Turance, ina dauke da hotuna da bidiyon rayuwar iyalan da ba a taba gani a waje ba.

Akwai hotunan matashiyar Gimbiya Lilibet, wasanni, tsokana, da zolaya har da rawar da take yi.

Fararen idanunta cike da fara’a.

Cike da soyayya, ga mahaifinta, sarkin da ya mutu da wuri, da mijinta Yarima Philip, wanda ya zame mata katanga kuma bango a dukkan lamuranta, ya sadaukar da komai nasa, ya yi gwamman shekaru tare da ita, bai taba kaucewa daga inda take ba har sai da wa’adi ya riske shi.

Makonnin da suka wuce, sun zama tamkar tunatarwa ga masoya, da ‘yan uwa, da abokan arziki, da makusanta, da wadanda suka san dukkan sirrinta, kan cewa duk shekarun da ta yi, babu abinda ya sauya Lilibet daga yadda take da kuruciya, dariyarta, tsokanar fada, murmushi, sadaukarwa da farin ciki.

Ta yi tsokaci akan shirin talbijin din na musamman.

"Ko da yaushe kuna fatan matasan zamani za su ji dadi da mishadantuwa," tsokacinta game da fim din iyalanta.

"Watakil su yi mamakin ganin ashe ni ma matashiya ce a wani zamani da ya shude".

Ka da wani ya yi mamaki. Saboda a watannin karshe na rayuwarta, wannan matashiyar Elizabeth din, Lilibet mai tsokanar fada da wasa da faran-faran, ta sake bayyana a tattare da dattijuwar sarauniyar, tana wasa da zolaya cikin mutane, da kallon nan na kuruciya, fito da mamalade da ake nade biredi da shi, daga cikin jakarta a lokacin bikin shekara 70 da hawa mulkinta.

A yanzu an rufe jakar. Komai ya zama tarihi. Babu abin da ya yi saura, sai dai a tuna da lokutan da suka shude.

A yau Litinin an rufe duk wata kafa, an rufe kofar zamanin mulkin Sarauniya Elizabeth ta II.