Da gaske an saki Sunday Igboho mai rajin kare ƙabilar Yarbawa?

Mai rajin kare ƙabilar Yarbawa, Sunday Igboho

Asalin hoton, FACEBOOK/SUNDAY ADEYEMO IGBOHO FOUNDATION

Bayanan hoto, Mai rajin kare ƙabilar Yarbawa, Sunday Igboho

Mai rajin kare ƙabilar Yarbawa a Najeriya, Oloye Sunday Adeyemo, wanda aka fi sani da Sunday Igboho ya samu ƴancin barin ƙasar Benin bayan kwashe shekara biyu ana tsare da shi.

A ranar Lahadi ne labarin samun ƴancin Igboho ya bayyana bayan ya walla wani saƙo a shafinsa na instagram yana gode wa tsohon shugaban Najeriya, Olusegun Obasanjo da kuma wasu fitattun ƴan Najeriyar.

Lauyan Sunday Igboho a Najeriya, Yomi Aliyu (SAN) ya tabbatar wa BBC da batun sakin ɗan rajin kare ƙabilar ta Yarbawa, wanda ke kan hanyarsa ta zuwa Jamus domin haɗuwa da iyalansa.

A wata tattaunawa da BBC, Yomi Aliyu ya ce babu abin da zai hana Sunday Igboho dawowa Najeriya tunda gwamnatin Benin ta sake shi, kasancewar ba ya da wata harƙalla da gwamnatin Najeriya.

Ya ce “Idan har Benin za ta sake shi kan cewa bai mata wani laifi ba, zai iya shiga Najeriya. Zai iya shiga Najeriya idan ya ga dama.”

An kama Sunday Igboho ne a 2021 bayan da jami’an hukumar DSS na Najeriya suka kai samame a gidansa bisa zargin shi da yaɗa aƙidar ƴan aware.

Me Sunday Igboho ya ce?

Kauce wa Instagram
Ya kamata a bar bayanan Instagram?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da Instagram suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta Instagram da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

Karshen labarin da aka sa a Instagram

A shafinsa na Instagram, Sunday Igboho ya wallafa wani bidiyo ne yana godiya ga wasu mutane a ‘wannan rana mia muhimmanci.’

Bai faɗi takamaiman abin da ya faru a ranar da ya kira mai muhimmanci ba, kuma bai bayyana cewa ko zai bar ƙasar Benin zuwa Jamus ko kuma zai koma Najeriya ba.

Cikin waɗanda ya gode mawa a akwai shugaban ƙasar Benin, Patrice Tallon da al’ummar Yarbawa, kamar Farfesa Wole Soyinka, da sarakunan Yarbawa da kuma masu goyon bayansa waɗanda ke goyon bayan ƴantar da ƙasar Yarbawa.

Ina Sunday Igboho yake a yanzu?

..

Yomi Aliyu ya tabbatar wa BBC cewa a ranar Lahadi Sunday Igboho yana Benin, sai dai ana sa ran zai kama hanya zuwa Jamus.

Hukumomi a Benin sun kama Igboho ne a filin jiragen sama na Benin sa’ilin da yake kan hanyarsa ta zuwa Jamus.

Yanzu kimanin shekara biyu ke nan bayan da hukumomi suka tsare Sunday Igboho tun bayan kama shi a daidai lokacion da yake yunƙurin tserewa bayan da jami’an tsaron Najeriya suke neman shi.