Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Me ya sa ƴan Najeriya ke son fita zanga-zanga, duk da kamen da ake yi?
- Marubuci, Yusuf Akinpelu
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News Lagos
- Aiko rahoto daga, Lagos
- Lokacin karatu: Minti 6
Khalid Aminu na shirin zuwa wani gidan rediyo a Kaduna, domin halartar wani shiri a lokacin da wasu jami'an tsaro na sirri sanye da kayan gida su uku suka shiga cikin ɗakin otel ɗin da yake, inda suka tafi da shi domin amsa tambayoyi.
Ya ce an tsare shi na tsawon sa'a shida kuma an yi masa tambayoyi kan gangamin da yake jagoranta na wayar da kan jama'a don fita zanga-zanga ranar 1 ga watan Agusta.
Sai da lauyansa ya shiga lamarin kafin aka sake shi, in ji shi.
"Zan halarci zanga-zangar duk da abin da ya faru," kamar yadda ya shaida wa BBC.
Banda shi, an kuma tsare wani mai amfani da shafin TikTok da ke zama a Kano, Junaidu Abdullahi (wanda aka fi sani da Abusalma) na tsawon kwanaki shida bayan ya wallafa wani bidiyo - wanda daga baya ya goge - inda yake kira ga mutane su yi watsi da duk wanda ke son hana su fita zanga-zangar.
Shi ma an sake shi bayan yi masa gargaɗi, a cewar lauyansa.
"Ba kama mutane masu sukar gwamnati ya kamata hukumomin Najeriya su riƙa yi ba, a wannan lokaci da miliyoyin mutane ke daf da faɗawa cikin yunwa, rashin abinci mai gina jiki da kuma matsanancin talauci," in ji ƙungiyar Amnesty International a wani martani da ta mayar kan kama Abusalma.
Masu fafutika irinsu Aminu, na ta gangamin tara mutane domin fita zanga-zangar wadda aka yi wa laƙabi da "Kawo ƙarshen rashin kyakkyawan shugabanci a Najeriya", inda suke kira ga gwamnati ta samar da ilimi kyauta, kawo ƙarshen rashin tsaro, ayyana dokar-ta-ɓaci kan hauhawar farashi, da kuma bayyana albashin ƴan majalisa.
Shugaba Bola Tinubu ya buƙaci matasan kada su shiga zanga-zangar, inda ya ce waɗanda ba sa son zaman lafiyar ƙasar ne suka shirya ta.
Shugaba Tinubu dai ya lashe zaɓen 2023 ne bayan samun kashi 37 na ƙuri'un da aka kaɗa, wanda kuma shi ne mafi kankanta da wani shugaban ƙas ya lashe zaɓe a tarihin ƙasar.
Har yanzu bai samu karɓuwa daga wajen mutane da dama ba, bayan ayyana cire tallafin man fetur da na lantarki.
Ga kuma faɗuwar darajar naira da hauhawar farashin kayan abinci da na tafiye-tafiye.
Mista Tinubu ya ce gwamnatinsa ta ɓullo da sauye-sauyen tattalin arziki domin janyo hankalin masu zuba jari daga ƙetare domin inganta tattalin arzikin ƙasar.
To sai dai hakan ya ƙara jefa miliyoyin mutane cikin talauci da kunci.
Rashin tsaro, musamman a yankin arewacin ƙasar, ya ɗaiɗaita manoma da dama da kuma janyo tashin farashin kayan abinci.
Farashin kayan abinci irin shinkafa da wake da tumatiri da dankali da kuma doya ya tashi da kashi 250 tsakanin watan Mayun 2023 zuwa Yunin 2024, a cewar alkaluman da hukumar ƙididdiga ta ƙasar ta fitar.
Wannan abu ya yi matukar harzuƙan 'yan ƙasar da dama.
Shugaba Tinubu ya buƙaci a ba shi ƙarin lokaci domin ya shimfiɗa shirye-shiryen gwamnatinsa.
Ya kuma amince da sabon albashi mafi ƙanƙanta na naira 70,000, inda yanzu ake jiran ya saka hannu a kai bayan majalisa ta amince da shi.
Ƴan majalisar wakilai sun kuma amince su rage albashinsu har na tsawon wata shida.
Gwamnatin Najeriyar ta kuma sanar da raba tan-tan na hatsi zuwa jihohi.
Haka kuma ya ƙaddamar da bai wa ɗalibai bashin karatu da dakatar da harajin da ake biya kan wasu abinci da ake shigowa da su da kuma alƙawarta motocin bas-bas masu amfani da iskar gas da za su ɗauki mutane domin rage musu raɗadin janye tallafin mai.
Sai dai a daidai lokacin da hauhawar farashi ya tashi zuwa kashi 34 a watan Yuni, wanda rabon a ga haka tun shekara 28 da suka shuɗe, wasu ƴan Najeriya na jin cewa hakan bai wadatar ba wajen shawo matsin tattalin arziki da ake ciki.
Sun ce ƴan siyasa ba sa sadaukarwa yadda ya kamata.
Suna kuma son gwamnati ta rage yawan jami'anta da kuma irin maƙudan kuɗaɗe da ake kashewa wajen biyansu, da kuma sayen motocin alfarma da jirage na manyan jami'an gwamnati, ciki har da batun sayen jirgi wa ofishin shugaban ƙasa.
Har ila yau, mutane da dama na ganin ba a yi abin da ya kamata ba wajen magance batun cin hanci da rashawa.
Sun ce dakatarwar da aka yi wa ministar ma'aikatar jin ƙai, saboda zargin karkatar da wasu kuɗaɗe bai wadatar ba.
Aminu ya faɗa wa BBC cewa yana tara mutane a fili da kuma kafafen sada zumunta domin wayar musu da kai na fitowa zanga-zanga da kuma yin magana kan batun "rashin kyawun shugabanci a ƙasar da kuma wasu tsare-tsaren gwamnati da suke ganin ba su dace ba. Kowa na ji a jikinsa."
Aminu, mai shekara 38 wanda Injiniya ne, ya ce ƴan Najeriya na jin har yanzu ba a yi musu abin da ya kamata ba na tsawon lokaci da suka yi ta tsammani, kuma hakan ne ya sa mutane suke son fitowa kan tituna domin nuna fushinsu.
Hukumomi sun ce suna fargaba zanga-zangar za ta iya rikiɗewa zuwa tarzoma.
Sifeton ƴan sandan Najeriya ya yi gargaɗi kan yin zanga-zanga irin ta Kenya, inda ya ce ƴan Najeriya na ganin abin da ke faruwa a Kenya, na yadda matasan ƙasar suka fito kan tituna da yin kira ga shugaba William Ruto da ya sauka, abin da ya janyo ya dakatar da dokar ƙarin kuɗin haraji da kuma korar ɗaukacin muƙarrabansa.
"Wasu gungun mutane, waɗanda suka haɗa da masu ƙarfin faɗa a ji, na ta yin tsare-tsare wajen tara masu niyyar yin zanga-zanga domin su ta da tarzoma a ƙasa da nufin kwaikwayar irin zanga-zangar Kenya," in ji Mista Egbetokun.
Shekara huɗu da suka wuce ne, aka yi wata gagarumar zanga-zangar a Najeriya domin adawa da cin zalin ƴan sanda waɗanda aka zarga da kisan mutane.
Zanga-zangar ta EndSars ta cimma manufarta na ganin an soke jami'an ƴansandan na SARS, sai dai an fuskanci tashin hankali inda aka kashe ɗaruruwan masu zanga-zanga.
Zuwa yanzu, zanga-zangar da ake shirin yi ba ta da wani jagora a fili, inda aka yi imanin cewa sun yi haka ne domin kauce wa kame daga wajen hukumomi da kuma tattaunawa ta bayan fage.
Sai dai Aminu ya ce duk da cewa babu masu jagorantar zanga-zangar, amma akwai masu tara mutane.
"Akwai shirye-shirye da ake yi wajen ganin an shafa wa zanga-zangar da muke shirin yi kashin kaji," in ji shi. "Wannan ne ya sa muke kira ga dukkan ƴan Najeriya da su fito domin a yi da su."
Omoyele Sowore, wanda tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa, shi ma yana ta gangamin tara mutane domin fitowa zanga-zangar, inda yake ta raba fostoci domin kowa ya shirya.
Wasu jami'ai a fadar shugaban ƙasa sun zargi ƴan siyasar adawa irinsu Mista Sowore da ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar Labour, Peter Obi na cusa wa mutane ra'ayin fita zanga-zanga ta hanyar mara musu baya, zargin da Labour ta musanta.
A gefe guda, ministan yaɗa labarai, Mohammed Idris ya yi ƙoƙarin kwantar da hankalin mutane a daidai lokacin da hankula ke ƙara tashi, inda ya ce waɗanda ke kiran a yi zanga-zanga "ƴan uwanmu ne".
"Wannan batu ne na ƴan Najeriya kuma dukkanmu na kallon wannan batu da idon basira, muna fatan za a samu zaman lafiya mai ɗorewa," in ji ministan.
Jerin zanga-zanga da aka yi a baya kamar EndSars ta rikiɗe zuwa tarzoma bayan artabu da masu zanga-zanga suka yi da jami'an tsaro.
Har yanzu ana tuna tashin hankalin da aka shiga lokacin zanga-zangar EndSars gabanin wadda za a yi ranar 1 ga watan Agusta.
Akwai mutanen da ba za su fito ba musamman idan suka tuna da tashin hankali da aka fuskanta a 2020.
Akwai kuma ƙungiyoyi, kamar ƙungiyar ɗalibai ta Najeriya (NANS), wadda ta soki zanga-zangar da ake shirin yi.
Mista Tinubu ya ce shi ma ya taɓa jagorantar zanga-zanga a lokacin da yake ɓangaren adawa - sai dai ta lumana ce.
A mako mai zuwa ne, za a ga yadda batun zai kasance a wajen Tinubu, ba wai a matsayinsa na shugaban Najeriya ba, har ma ga kasancewarsa shugaban ƙungiyar Ecowas.