Ko Hamas za ta amince ta bar Gaza?

A Hamas member holding a gun
Ko Hamas za ta amince ta bar Gaza?
    • Marubuci, Paul Adams
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Diplomatic correspondent
    • Aiko rahoto daga, Jerusalem
    • Marubuci, Rushdi Abualouf
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Gaza correspondent
  • Lokacin karatu: Minti 9

Ta yaya ƙungiyar da ta mulki Gaza tsawon kusan shekara 20, tana yi wa kusan Falasɗinawa miliyan biyu mulkin kama-karya da fafatawa da Isra'ila a lokuta daban-daban, a rana ɗaya za ta ajiye makami da miƙa ragamar mulkin yankin?

Daga irin munanan hotuna da ke fitowa daga Gaza tun bayan tsagaita wuta a ranar 10 ga watan Oktoba, da alama Hamas na ci gaba da aiwatar da ƙudurinta na nuna ƙarfi a Gaza.

Jami'anta sanye da takunkuman fuska sun mamaye kan tituna, suna duka da kuma hukunta abokan hamayyarsu.

Wasu kuma da aka bayyana a matsayin masu bai wa maƙiya haɗin kai ana harbinsu a ƙafafu da kuma jibgar su da manyan kulake.

Wasu daga cikin waɗanda Hamas ke far mawa tana musu hukunci sun kasance cikin ƙungiyoyin da suka riƙa yin wawaso da karkatar da kayan agaji, wadanda ake zargi da tsananta mummunan halin da mutane suka faɗa ciki, in ji wani mutumin da BBC ta tattauna da shi.

Majalisar Dinkin Duniya a baya ta zargi wasu ƙungiyoyi da sace kayan agaji da aka shigar Gaza.

Wannan ba shi ne abin da shugaban Amurka Donald Trump yake son gani ba a cikin yarjejeniyarsa ta zaman lafiya a Gaza, mai ƙunshe da ƙudurori 20, wadda ta ƙunshi cewa Hamas za ta miƙa makamanta, ta amince da shirin yin afuwa, mayaƙanta su fice daga Gaza sannan su miƙa ragamar tsaron yankin ga dakarun tabbatar da zaman lafiya ta ƙasa da ƙasa da za a kafa.

 A Hamas militant waves his party's flag

Asalin hoton, AFP via Getty Images

Bayanan hoto, Shirin tsagaita wuta ya fara aiki a ranar Juma'a 10 ga watan Oktoba​ - Hamas da Isra'ila sun zargi juna da saɓa yarjejeniyar

A nasa ɓangare, da alama Shugaba Trump ya rasa wane mataki zai ɗauka game da batun cin zarafin.

A kan hanyarsa ta zuwa Isra'ila a ranar 13 ga watan Oktoba ya nuna cewa Amurka ta bai wa Hamas - wadda ƙungiya ce da Amurka da Birtaniya suka ayyana a matsayin ta ta'addanci - damar maido da doka a Gaza.

"Mun ba su dama ta wani lokaci," kamar yadda ya shaida wa ƴanjarida a cikin jirgin shugaban Amurka na Airforce One.

Kwana uku bayan haka sai ya tsaurara kalamansa. "Idan Hamas ta ci gaba da kashe mutane a Gaza, wanda hakan ba shi a cikin yarjejeniyar," kamar yadda ya rubuta a shafinsa na sada zumunta, "zai zamanto babu wata makawa face mu je mu kashe su."

To yanzu mene ne matsayin Hamas idan aka lura da abin da ke faruwa a Gaza?

Sannan kuma, idan aka yi la'akari da yaƙin da aka gwabza na shekara biyu, tabbas hakan ya jefa mutanen yankin cikin uƙuba da wahala, da kashe-kashen jagororinta, shin akwai wani abu da ya rage wa Hamas a nan gaba?

'Taɓarɓarewar doka da oda'

Al'ummar Gaza, waɗanda suka jigata tare da shiga cikin tashin hankali sanadiyyar yaƙin na shekara biyu, wanda ma'aikatar lafiya ta Hamas ta ce ya haifar da kashe mutum 68,000 a Gaza - wannan mataki da aka ɗauka daga ƙarshe ba abu ne mai sauƙi ba, sai dai kuma bai zo da mamaki ba.

Daga cikin mutanen Gaza da wakilin BBC ya tattauna da su - waɗanda wasu daga cikinsu ma'aikatan agaji ne, da lauyoyi da kuma wani tsohon mai bai wa shugaban Hamas shawara - kowannensu na da ra'ayi da ya sha bamban game da ko Hamas za ta amince ta miƙa ragamar ikon Gaza.

Da kuma ko yanzu ne lokacin da ya dace a samu hakan.

Palestinians gather to celebrate following the announcement of a ceasefire agreement

Asalin hoton, Anadolu via Getty Images

Bayanan hoto, Falasdinawa na murna sanadiyyar cimma yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza

"Shekara biyu ke nan na wargajewar doka da oda," in ji ma'aikaciyar agaji Hanya Aljamal wadda ke zaune a birnin Beir al-Balah, a tsakiyar Zirin Gaza. "Muna bukatar a samu wanda zai karɓi ragama.

"Duk da rashin cancantar Hamas na mulkin Gaza, gara su a kan ƙungiyoyin ƴan daba."

Dr Ahmad Yousef, wanda tsohon mashawarci ne ga Ismail Haniyeh, tsohon shugaban ɓangaren siyasa na Hamas, na da ra'ayin cewa ana buƙatar hukuma mai ƙarfi a yanzu.

"Matuƙar akwai mutanen da ke ƙoƙarin ci gaba da ɗaukar doka a hannunsu, muna buƙatar mutanen da za su tsorata su tare da korar su," in ji Dr Yousef, wanda ke jagorantar wata ƙungiyar ƙwararru a Gaza, kuma har yanzu yake da kusanci da shugabannin Hamas.

A shot of Hanya Aljamal
Bayanan hoto, 'Duk da rashin cancantar Hamas na mulkin Gaza, gara su a kan ƙungiyoyin ƴan daba,' in ji Hanya Aljamal

"Abin zai ɗauki lokaci. Ba lokaci mai tsawo ba. Nan da wata ɗaya za mu karɓi baƙuncin ƴansanda da sojoji daga Turkiyya da Masar," kamar yadda ya ci gaba da bayana, yana nufin dakarun tabbatar da zaman lafiya da za a samar a Gaza, kamar yadda yake ƙunshe a cikin yarjejeniyar zaman lafiya.

Ana sa ran rundunar za ta ƙunshi dakaru daga Masar da Turkiyya.

"Wannan ne lokacin da za su ajiye bindigoginsu."

Sauran ƴan Gaza na shakku, da ɗari-ɗari. Wasu na da yaƙinin cewa da wahala Hamas ta saki iko da kuma ajiye makamanta.

Moumen al-Natour, wani lauya mazaunin Gaza wanda Hamas ta sha ɗaurewa a gidan yari, na daga cikin masu wannan ra'ayi.

Members of Hamas line up

Asalin hoton, AFP via Getty Images

Bayanan hoto, Falasdinawa da dama na ganin cewa da wahala Hamas ta ajiye makamanta da miƙa iko

Tun a cikin watan Yuli ya shiga ɓuya, bayan da wasu mutane sanye da takunkuman fuska suka je gidansa da ke Birnin Gaza, tare da buƙatarsa da ya je asibitin al-Shifa domin amsa tambayoyi, kamar yadda ya bayyana.

"Hamas [na aike wa duniya] saƙo da kuma Donald Trump...cewa ba za su saki mulki ba kuma ba za su ajiye makamansu ba.

"Idan na shiga hannun Hamas a yanzu, za su kashe ni a kan titi ta hanyar harbi da bindiga kuma su ɗauki bidiyon hakan," kamar yadda ya bayyana a cikin ɗaya daga cikin bidiyoyin da ya turo mana daga maɓoyarsa a Gaza da bai bayyana ba.

Bangon da ke bayansa na cike da ramukan harsasai.

Moumen al-Natour
Bayanan hoto, Moumen al-Natour, lauya da ke Gaza ya ce idan ya shiga hannun Hamas a yanzu za su kashe shi

"Ƴan daba ne, ba gwamnati ba," kamar yadda ya bayyana Hamas.

"Ba na son su ci gaba da kasancewa a Gaza... Ba na son su ci gaba da riƙe hgwamnati, kuma ba na son su ci gaba da riƙe harkar tsaro. Ba na son na ga suna yaɗa ƙidojinsu a masallatai, ko a kan tituna ko kuma a makarantu."

'Har yanzu Hamas ce ke da ƙarfi Gaza'

Mista al-Natour na da nasa tsarin da yake son ya gani a Gaza.

Yana ganin cewa ƙungiyoyin da a yanzu Hamas ke azabtarwa, za a iya haɗe a wani sabon tsarin tabbatar da tsaro.

To sai dai manufofinsu da ke karo da juna da kuma wasu munanan abubuwan da wasunsu suka aikata a baya, da zargin wasu daga cikinsu da alaƙa da rundunar sojin Isra'ila, abu ne mai matuƙar matsala.

"Gaskiyar lamari shi ne - kuma wani lokaci wani abu ne da ke da wahala ga Isra'ila ta amince hakan na faruwa - shi ne har yanzu Hamas na nan da ƙarfinta a Gaza." In ji Dr Michael Milshtein, tsohon shugaban sashen lamurran Falasɗinawa a hukumar tattara bayanan sirri ta Isra'ila.

"Dogaro da kungiyoyin da ba su da tabbas, kamar ƴan daba, waɗanda akasarinsu masu aikata laifi ne wadanda ke da alaƙa da ƙungiyar ISIS, kuma akasarinsu suna da hannu a hare-haren ta'addanci kan Isra'ila - a ce ana ganin su ne madadi a kan Hamas, wannan mafarki ne kawai."

Dr Michael Milshtein smiles at the camera
Bayanan hoto, Har yanzu Hamas ce ke da ƙarfia Gaza, in ji Dr Michael Milshtein, tsohon shugaban sashen lamurran Falasɗinawa a hukumar tattara bayanan sirri ta Isra'ila

Jami'an Hamas sun ce a shirye ƙungiyar take ta miƙa iko da jagorancin Gaza. Yarjejeniyar da Trump ya samar, wadda Hamas ta ce za tagoyi baya, ta ƙunshi "kafa gwamnatin riƙon-ƙwarya ta ƙwararru Falasɗinawa wadanda ba su da alaƙa da siyasa."

To amma ko da a shirye ƙungiyar take ta ja baya daga fagen mulki - wani abu da Falasɗinwa da kuma Isra'ilawa da ma ke shakku - matakin shawao kan mayaƙanta masu tsattsauran ra'ayi su ajiye makamansu zai zamo abu mai matuƙar muhimmanici, ga ƙungiyar, wadda tun gabanin harin watan Oktoban 2023, ƙarfinta ya dogara sosai kan ɓangaren mayaƙanta.

Yadda Hamas ta yi ƙarfi a Gaza

Taswirar inda Gaza take, da kuma Masar da Isra'ila a gefe da gefe
Bayanan hoto, Taswirar inda Gaza take, da kuma Masar da Isra'ila a gefe da gefe
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Domin amsa wannan tambaya mai sarƙaƙiya, kan me zai faru da Hamas nan gaba, zai yi kyau a yi waiwaye domin ganin yadda ƙungiyar ta samu irin ƙarfin da take da shi.

Daga lokacin da ta samo asali a shekarun 1980, daga wani ɓangare na ƙungiyar Muslim Brotherhood da ke Masar, zuwa ga yadda ta zama abokiyar hamayyar ƙungiyar ƴanta yankin Falasɗinawa ta PLO, Hamas ta rikiɗe zuwa ƙungiyar ƴan tawaye wadda ta yi sanadin asarar Isra'ilawa fararen hula.

Da farko Isra'ila ta taimaka wa Hamas a asirce, inda ta riƙa kallon ta a matsayin makamin da za ta yi amfani da shi wajen ƙalubalantar ƙungiyoyin PLO da Fatah, wadda a lokacin ke ƙarƙashin jagorancin Yasser Arafat.

Sai dai a lokacin da Hamas ta ƙaddamar da hare-haren ƙunar-baƙin-wake kan Isra'ilawa a shekarun 1990 da 2000, Isra'ila ta mayar da martani ta hanyar kashe manyan jami'an ƙungiyar.

Wani artabu kan ƙwace iko da mulkin Gaza da aka yi tsakanin Hamas da Fatah, ya kai ga cewa Hamas ta ƙwace iko da Zirin Gaza kacokan.

A tsawon shekaru 18 da Hamas ta kwashe tana mulkin Gaza, Isra'ila ta riƙa ƙoƙarin toshe hanyoyin shigar kayan masarufi da na soji zuwa yankin, da kuma gwabza yaki tsakanin ɓangarorin biyu a 2008 zuwa 2009 da kuma 2012 da 2014 da kuma 2021.

Yayin da Hamas ke iko da Gaza, ita kuma hukumar Falasɗinawa ta PA ke jan ragamar Gaɓar Yamma, Falasɗinawa sun kasance a rarrabe, wanda hakan ke bai wa Isra'ila damar ci gaba da ikirarin cewa ba su da takamaiman shugabancin da za ta iya tattaunawa da shi.

Isra'ila ta bi ta kowace hanya wajen hallaka shugabannin Hamas

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Isra'ila ta bi ta kowace hanya wajen hallaka shugabannin Hamas

Hamas ta gaji da yaƙi

Duk da cewar har yanzu ana fama da tashin hankali a Gaza, tsohon mai bai wa hugaban ƙungiyar shawara, Ahmed Yousef ya ce ƙungiyar ta gaji da yaƙi.

Ba tare da ambato batun 7 ga watan Oktoba kai-tsaye ba, ya bayyana yaƙin a matsayin "babban kuskure" sannan kuma "akwai buƙatar sauya salo".

Mutane zaune a cikin ɓaraguzai a Gaza

Asalin hoton, Anadolu via Getty Images

Bayanan hoto, Mutane zaune a cikin ɓaraguzai a Gaza

"Ina magana da da dama daga cikinsu kuma sun shaida min cewa ba su da niyyar ci gaba da mulkin Gaza," in ji shi.

"To amma Hamas tana da mambobi fiye da 100,000, kuma waɗannan mutane ba za su ɓace ba haka nan kawai."

Ya ce yana ganin Hamas na son ta sauya tsarinta domin ganin yadda za ta ci gaba da taka rawa a siyasance a nan gaba, lamarin da ya kwatanta da yadda ANC ta sauya daga ƙungiyar yakin sunƙuru zuwa jam'iyyar siyasa a Afirka ta Kudu.

"Idan a gobe za a shirya zaɓe," in ji shi, "ina da yaƙinin cewa Hamas za ta bayyana da wani suna na daban, tare da nuna cewa tana son zaman lafiya kuma za ta so ta taka rawa a harkar siyasa yankin.

"Tashin hankali ba zai zamo aikin kowace irin jam'iyyar siyasa ba."

Mr Milshtein na shakku

"Idan har za a samu wata gwamnati ta ƴan Gaza, tabbas Hamas za ta kasance wadda take juya al'amura ta ƙarƙashin ƙasa," in ji shi.

Akwai yiwuwar cewa Isra'ila za ta sake yin arangama da Hamas a nan gaba

Asalin hoton, Anadolu via Getty Images

Bayanan hoto, Akwai yiwuwar cewa Isra'ila za ta sake yin arangama da Hamas a nan gaba

Ya ce zai yi wahala a iya karɓe makamai: inda ya yi hasashen sake ɓarkewar wani yakin a Gaza cikin shekara biyar masu zuwa.

Sai dai Ami Aylon, tsohon shugaban hukumar tsaron Isra'ila ta Shin Bet na ganin cewa ya kamata Isra'ila ta nemi wani salon yaƙi da maƙiyanta.

"Sai dai idan mun kawar da aƙidar, in ba haka ba za su ci gaba da haɓɓaka," in ji shi.

"Hanya ɗaya tilo da za mu kawar da aƙidar ita ce samar wa mutanen Isra'ila da Falasɗinawa sbuwar alƙibla. Alƙiblar samar da ƙasashe biyu."

A halin yanzu za a iya cewa babu wannan sabuwar alƙibla, wanda ya sanya hasashen Dr Milshtein ya fi na Ami Ayalon ƙarfi.

To amma, duk yadda aka yi ƙoƙarin dankwafe Hamas, ta wata hanyar, dole ne wata rana sai Isra'ila ta sake yin arangama da Hamas a nan gaba.