Yadda zanga-zangar lumana ta zama tarzoma a wasu jihohin Najeriya

Lokacin karatu: Minti 7

A yau Alhamis ne aka fara zanga-zangar gama-gari kan tsadar rayuwa da matsalar tsaro da kuma neman samun mulki nagari a fadin Najeriya.

Da farko dai zanga-zangar wadda aka shirya ta lumana ta fara wakana a jihohi da dama cikin kwanciyar hankali, amma daga bisani ta juye a wasu wuraren zuwa tashin hankali.

Ma'aikatu da hukumomin gwamnati da bankuna da sauran gine-gine na gwamnati da harkokin kasuwanci sun kasance a rufe a jihohi da dama.

Masu zanga-zangar dai sun tsara yin ta tsawon kwana 10 har sai gwamnati ta biya musu bukatunsu.

Jihar Kano

A jihar Kano zanga-zangar ta juye inda ta zama tashin hankali, kamar yadda rahotanni suka nuna cewa wasu ɓata-gari sun shiga zanga-zangar kuma suka rika fasa shaguna da kantina da ofisoshi suna kwashe kaya.

Rahotanni sun ce ɓata-garin sun rika aikata miyagun abubuwa da suka haɗa da ƙwacen waya a hannun jama'a.

Tun da farko, matasan da suka fara gangamin sun nufi gidan gwamnatin jihar ta Kano ne.

Wakilinmu ya ce wasu daga cikin gungun matasan sun fasa wani gida a kusa da fadar gwamnatin Kanon, inda suka rika kwasar taliya da man girki a jarkoki.

Kazalika wasu daga cikin matasan sun rika balle duk wani abu da suka gani na karfe da ciccire fitilu na titi masu amfani da hasken rana.

Wasu kuma sun rika farfasa kayayyakin ne, yayin da suke cinna wuta a tayoyi da suke kashe hanya da su.

Amma daga bisani jami'an tsaro sun rika bi suna kama wadanda suka kwashi kayan.

Haka kuma bayanai sun ce jami'an tsaro sun rika harbin iska tare da amfani da mota mai feshin ruwan zafi.

Wakilinmu na BBC ya tabbatar da cewa ya ga mutum wajen biyar da harsashi ya same su amma ba za i iya tabbatar da cewa ko sun rasu ba.

Wasu daga cikin matasan da suka shiga zanga-zangar sun far ma sabuwar cibiyar hukumar sadarwa ta kasar (NCC), wadda za a bude a mako mai zuwa, inda suka wawashe wasu daga cikin kayan cibiyar tare da cinna mata wuta, kamar yadda wasu rahotanni suka ce.

An ga matasan suna ta kwashe kwamfuta da kujeru da sauran na'urori da duka wasu kaya masu muhimmanci da za su iya dauka

Jihar Jigawa

A jihar Jigawa, wasu rahotanni sun nuna cewa zanga-zangar ta kazanta a wasu sasssan jihar, inda ta kai ga barnatawa da kwashe wasu kayayyaki na gwamnati.

A Dutse babban birnin jihar, bayanai sun nuna cewa an kona hedikwatar jam'iyyar APC mai mulkin jihar da ma kasar, yayin da harbin da jami'an tsaro suka yi aka ce ya samu wani matashi, sai dai babu tabbacin ko ya rasu.

A garin Shuwarin da ke wajen babban birnin na Jigawa, an samu hatsaniya kamar yadda wasu rahotanni suka ce, inda harbin da jami'an tsaro suka yi ya samu wani matashi, wasu kuma na cewa mutum biyu aka samu.

Wasu daga cikin matasan da suka shiga zanga-zangar sun kuma wawashe wata ma'ajiya ta gwamnati inda aka ajiye shinkafa.

Can a karamar hukumar Birnin Kudu ma, wasu matasa sun fasa ma'ajiyar gwamnatin jihar inda suka kwashe shinkafa da taki, kamar yadda a Hadejia wasu suka kona hedikwatar karamar hukumar tare da wawashe rumbun ajiya na hukumar bayar da agajin gaggawa ta jiyar.

Abuja

A Abuja babban birnin tarayyar kasar, masu zanga-zangar sun hallara a babban filin wasa na kasa wato Moshood Abiola Stadium, kasancewar babbar kotun birnin ta umarci masu zanga-zangar da su tsaya kawai a filin a lokacin zanga-zangar kuma kada su wuce nan.

Kotun dai ta bayar da umarnin ne ranar Laraba, kasa da sa'a 24 da za a fara zanga-zangar.

Amma daga bisani matasan sun fita daga filin suka nufi filin taro na Eagle Square, lamarin da ya sa jami'an tsaro suka fara harba hayaki mai sa hawaye, sai dai lamarin bai kazanta ba.

Sai dai a yayin da suke zanga-zangar ta lumana, an kuma samu wasu masu kishiyar tasu zanga-zangar wato masu goyon bayan gwamnati.

Jami'an tsaro sun shiga tsakanin bangarorin biyu don gudun tashin hankali.

Bankuna da kasuwanni da sauran ofisoshi na gwamnati da kamfanoni da sauran 'yan kasuwa sun kasance a rufe.

Babu dai wasu rahotanni da aka samu na tashin hankali a babban birnin tarayyar.

Sai dai kuma a yankunan Nyanya, da Karu da Maraba na jihar Nasarawa mai maƙwabtaka da Abuja, an samu hatsaniya a lokacin zanga-zangar. Harkokin kasuwaci sun tsaya cik yayin da masu zanga-zangar suka datse tituna

Masu zanga-zangar da ke dauke da miyagun makamai sun ci karfin tarin jami'an tsaro da aka jibge a wuraren, inda suka datse babbar hanyar Abuja zuwa Keffi.

Rundunar 'yansanda ta Abuja ta ce an kona wani sunduki da ke zaman karamar cibiya ko ofishin jami'anta a Nyanya.

Wasu rahotanni sun ce an ga mutum biyu da harsashi ya ji wa rauni amma ba a san ko 'yansanda ne ko sojoji suka yi harbin ba.

Jihar Legas

Can a jihar Legas babbar cibiyar kasuwanci ta kasar, da safiyar Alhamis tituna sun kasance fayau - babu ababen hawa, bankuna da ofisoshi sun kasance a rufe, yayin da masu zanga-zangar ke hallara a wurare daban-daban.

Masu zanga-zangar na ihun "a kawo karshen shugabanci maras nagarta" inda wasu suka kasance dauke da alluna da kwalaye masu rubuce-rubuce na nuna adawa da tsadar rayuwa da sauran abubuwan da suke bukata gwamnati ta yi.

Dandalin Freedom Park, ne dai gwamnatin jihar ta bayar da dama masu zanga-zangar su je domin taruwa don zanga-zangar.

An jibge tawagar jami'an tsaro da aka girke a gaba da bayan daruruwan masu zanga-zangar domin hana afkuwar rikici.

Sai dai masu zanga-zangar sun bayyana cewa suna yin ta ne a lumana don kawo karshen matsin rayuwa da neman a dawo da tallafin mai da inganta tsaro da sauran garambawul da dama da suke neman gwamnati ta yi.

Akwai raisin tabbas game da zanga-zangar, abin da watakila ya shafi fitowar wasu zuwa wuraren zanga-zangar saboda gudun abin da ka je ya zo.

Jihar Borno

A jihar Borno da ke arewa maso gabashin kasar kuwa, an sanya dokar hana fita a Maiduguri babban birnin jihar ta tsawon sa'a 24, bayan da zanga-zangar ta rikide zuwa tarzoma.

Kakakin rundunar 'yansandan jihar, Nahum Kenneth Daso, shi ne ya bayyana haka a wata sanarwa, inda ya ce an yi hakan ne saboda bam da ya tashi a jiya Laraba a wani wajen shan shayi.

Sanarwar 'yansandan ta ce an dauki wannan mataki ne domin tabbatar da zaman lafiya.

Bam din wanda ya tashi kwana daya kafin zanga-zangar ta Alhamis ya yi sanadiyyar mutuwar mutum 16, a cewar 'yansanda yayin da wasu rahotanni ke cewa mutum 19 ne suka rasu.

Jihar Yobe

A jihar Yobe ma da ke yankin arewa maso gabas rahotanni sun ce tarin matasa masu zanga-zangar sun kasance dauke da kwalaye masu dauke da rubutu iri daban-daban da ke nuna bukatunsu a babban birnin jihar Damaturu.

Zanga-zangar wadda ta lumana ce da farko ta kasance lami lafiya, amma kuma wasu rahotanni sun ce an kona wasu motocin bas-bas bakwai yayin da yanayinta ya sauya a Potiskum.

Motocin suna harabar hedikwatar karamar hukumar ne kamar yadda bayanai suka nuna.

An sanya dokar hana zirga-zirga a Nguru da Gashuwa da kuma Potiskum

Jihar Oyo

Masu zanga-zanga a jihar Oyo da ke kudu maso yammaci sun bi sahun takwarorinsu a fadin kasar domin nuna damuwa kan tabarbarewar al'amura a Najeriyar.

Sun hallara a kan titin Iwo tun da safiyar Alhamis inda suke rike da allunan da ke dauke da kokensu.

A jikin allunan an yi rubutu kamar haka: "Dole mutane su yi nasara", "A kawo karshen yunwa da wahalhalu yanzu", da sauransu.

Bayan nan, akwai karin masu zanga-zangar da suka yi cincirindo a harabar jami'ar Ibadan.

Masu shirya zanga-zangar sun shaida wa yan jarida cewa za su dunguma zuwa fadar gwamnatin jihar domin mika kokensu.

Yansanda da sauran jami'an tsaro suna sintiri a wuraren da masu zanga-zangar suka yi dafifi domin tabbatar da doka da oda.

Jihar Kaduna

A jihar Kaduna jami'an tsaro sun kama mutum 25 kamar yadda rahotanni suka ce, bisa zarginsu da barnata kayayyakin gwamnati.

Matakin ya biyo bayan zanga-zangar da wasu daga cikin matasan jihar suka bi sahu kamar yadda ta kasance a kasar.

Rahotanni sun ce an sanya wuta a ginin hukumar kula da ababen hawa ta jihar, KASTELEA da kuma barnata hukumar zuba jari ta jihar KADIPA.

Jihar Bauchi

Masu zanga-zangar sun taru ne a kofar fadar Sarkin bauchi inda suka bukaci ganawa da shi, amma 'yansanda suka hana su, sai dai hakan bai sa sun hakura ba inda suka matsa a kan ganawa da Sarkin inda daga nan sai jami'an tsaron suka yi amfani da hayaki mai sa hawaye domin tarwatsa matasan.

Matasan sun kafe a kan su ci gaba da zanga-zangarsu, lamarin da ya sa 'yansanda suka toshe dukkanin hanyoyin zuwa ga gidan gwamnatin jihar.

Jihar Ribas

A Port Harcourt, babban birnin jihar Rivers, daruruwan matasa ne suka fara tattaruwa domin gudanar da zanga-zangar a mahadar, Rumuola Junction, da ke kan titin Aba inda suka fara gangamin.

Yayin da suka fara kwarara ne a birnin sauran matasa da ke wurare daban-daban suka rika shiga, yawansu ya karu sosai.

Matasan sun kasance dauke da kwalaye da ke dauke da rubutun bukatunsu ga gwamnati, suka nufi fadar gwamnatin jihar.