Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yadda Rasha ta yi wa Faransa yankan baya kan nukiliya a Nijar
- Marubuci, Paul Melly
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, West Africa analyst
- Lokacin karatu: Minti 5
Ƙasar Rasha ta yi watsi da yiwuwar gina tashar makamashin nukiliya a Nijar - mai ɗimbin arzikin Uranium - ƙasa ce mai faɗin ƙasa, da ke yankin sahara, wadda ke shigo da mafi yawan wutar lantarkinta.
Wataƙila ta ga cewa ba shi da amfani kuma ba mai yiwuwa ba ne, amma manufar ita ce yunƙurin Moscow na neman wata fa'ida ta siyasa a kan ƙasashen yammacin Turai.
Nijar na da daɗaɗɗen tarihin fitar da ƙarafa zuwa Faransa domin sake inganta su, to amma a yanzu wannan tarihi ya sauya yayain da ƙasar da sojoji ke jagoranta ta yanke hulɗa da tsohuwar uwargijiyar tata.
A watan Yuni ne ƙasar ta mayar da aikin haƙar ma'adinin uranium da ƙungiyar Orano ta ƙasar Faransa ke gudanarwa zuwa na ƙasa, lamarin da ya share wa Rasha hanyar damar zama babbar sabwar ƙawar Nijar.
Ana magana ne game da samar da wutar lantarki da aikace-aikacen likitanci, tare da mai da hankali kan horar da ƙwararru ƙarƙashin yarjejeniyar haɗin gwiwa da aka rattaɓa wa hannu tsakanin kamfanin Rasha Rosatom da hukumomin Nijar.
Idan da aikin ya tabbata zai kasance aikin makamashin nukiliya na farko a Yammacin Afirka.
Bayan tattaunawa ta farko, ba a san ko ta yaya za a samu ci gaba a wannan hanya ba. Amma da wannan mataki, Moscow ta nuna cewa ta fahimci halin da Nijar ke ciki.
A tsawon sama da shekara 50, Orano, wanda kafin 2018 ake kira Areva – shi ne kamfanin da ya rika hakar Uranium, domin samar da nukiliya wanda ke da matukar muhimmanci wajen samar da makamashin kasar Faransa.
Kamfanin mallakin gwamnatin Faransa a yanzu na samun mafi yawan ma'adinai daga Canada da Kazakhstan kuma ya yi hasashen samun ƙari daga Mongolia da Uzbekistan.
Amma dangantakar Nijar ta kasance mai mahimmanci kuma tana da nauyi ta fuskar siyasa.
Amma duk da haka Faransa ta ƙi bai wa Nijar fasahar makamashin nukiliyar, duk da samar mata da makamashin da ƙasar ke yi.
Ita kuwa Nijar dole ne ta dogara sosai kan samar da makamashin kwal da kuma shigo da wutar lantarki daga Najeriya.
To amma yanzu, saɓanin da aka samu tsakanin sojojin mulkin Nijar da faransa ya bai wa Rasha damar samun kyakkyawar fata a ƙasar, na yiwuwar kafa tashar makamashin nukiliya, wani abu da kamfanin Areva/Orano ya kasa yi cikin shekaru masu yawa.
"Ba haƙar ma'adinin uranimun ne kawai burinmu ba. Dole mu samar da wani tsari da zai kawo ci gaba da kuma samar makamashin nukiliya na zaman lafiya,'' a cewar ministan makamashin Rasha Sergei Tsivilev a lokacin da ya ziyarci Nijar ranar 28 ga watan Yuli.
A zahiri, ba duka ba ne wannan. Akwai fa'idar tattalin arziki ga ƙasar Rasha kuma wani ɓangare ne na yunƙurin kawar da tasirin ƙasashen yamma daga yankin Sahel.
Rasha ka iya samun damar gina mahaka a Imouraren, ɗaya daga cikin wurare masu arzikin uranium a duniya.
Shirin Faransa na gina mahaƙar a wurin ya gamu da cikas bayan da aka samu raguwar buƙatar ma'adinin a duniya, bayan hatsarin Fukushima na Japan a 2011.
Kodayake an ƙudiri aniyar farfaɗo da shirin a tsakiyar 2023, to amma kwatsam, sai sojoji suka ƙwace mulkin ƙasar, tare da soke lasisin Orano.
Wannan mataki ya bai wa Rasha damar samun muhimmin matsayi a fanin samar da makamashin uranium a duniya, wani sinadari mai matuƙar muhimmaci a duniya, inda take fatan samar da tashar makamashin nukiliya da zai taimaka wajen rage makamashin da ke gurɓuta muhalli.
Kuma za su iya saya da yawa a farashi mai kyau, gabaɗaya ko wani ɓangare na tan 1,400 na uranium da aka sarrafa da ke jiran fitarwa daga ma'adinan Sominak da Orano ke sarrafawa a Arlit da ƙasar ta kama a watan Yuni.
Hannayen jari sun fara janyewa ne bayan ƙungiyar ƙasashen Yammacin Afirka ta Ecowas ta ƙaƙaba wa jamhuriyar Nijar takunkumin kasuwanci bayan hamɓarar da Mohamed Bazoum shugaban farar hular ƙasar a watan Yulin 2023.
Amma ko bayan dɗage takunkumin sabuwar gwamnatin soji ta hana Orano ci gaba da jigilar kayayyaki.
A wani mataki na daban, China ta nuna alamun sayen wasu daga cikin ma'adinan da aka inganta.
Da fari jhukumomin Nijar sun fara tuntuɓar Iran kan cinikayyar ma'adinin kafin Amurka ta gargaɗe ta game da hakan.
Damar da Rasha ta samu ita ce yadda Nijar ta ɓata da Faransa, lamarin da ya ba ta damar samun nutsuwar kasancewa babbar ƙawar Nijar da nufin samun dama dkan ma'adinin na Nijar
Sauran ƙawayen Nijar makwabta da ke arƙashin mulkin Soji, kamar Mali da Burkina Faso sun ƙulla alaƙar kasywanci da Rasha don fitar da babban ma'adinin ƙasashen wato zinare.
Sabbin dokokin haƙar ma'adinai sun tilasta wa masu zuba jari daga ƙetare su riƙa ware wa ƴan ƙasa manyan ayyuka a kamfanoninsu tare da tabbatar ana sarrafa mafi yawan ma'adinan a cikin ƙasa, lamarin da zai ƙara wa ƙasashen kudin shiga da samar da ƙarin ayyuka.
Ƙasar Mali har ma ta taɓa tsare shugabannin kamfanin haƙar zinare na Canada tsawon watanni saboda rigima kan biyan haraji.
Haka ita Nijar a yanzu na ɗaukar matakai masu tsauri kan masu haƙar ma'adinan ƴan ƙasashen waje.
Rufewa da kuma mayar da ayyukan Orano na ƙasa ya kasance mai tattare da nuna ƙyama ga juna, inda gwamnati da kamfanin ke zargin juna da kawo cikas.
Daraktan kamfanin a ƙasar, Ibrahim Courmo, ya kasance tsare a gidan yari ba tare da an tuhume shi ba tun watan Mayu.
Kuma ga dukkan alamu gwamnatin mulkin sojin da ke mulki a yau ta ƙuduri aniyar kawo ƙarshen zamanin da Faransa ta ɗauka tana haƙo uranium a Nijar, inda wani jami'in ya shaida wa jaridar Paris Le Monde cewa, Orano ya kasance ''yana cusa kanta da albarkatun ƙasarmu''.
Wanene zai iya faɗin ƙudirin Moscow game da haɗin gwiwar kimiyyar nukiliya da watakila ma samar da wutar lantarki za su taɓa kasancewa a zahiri?
Sai dai wani abu da ya bayyana a fili shi ne a Nijar ludayin Rasha ce kekan dawo a fagen siyasa da mulkin ƙasar.