Ko kun san amfanin ƙuda wajen sarrafa abincin da aka zubar?

    • Marubuci, MaryLou Costa
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Technology Reporter
    • Aiko rahoto daga, Vilnius, Lithuania
  • Lokacin karatu: Minti 5

Yawancin mutane ba sa yarda ƙuda ya zo ko kusa da abincin da suke ci, kuma ganin tsutsotsi a kwandon sharar gidanka abu ne da zai sa mutum ƙyanƙyami wani ma har ya yi amai.

To amma hukumomi a wasu biranen duniya a yanzu suna amfani da tsutsar da ke girma ta zama ƙuda wajen sarrafa sharar abinci wajen mayar da ita sinadarin furotin.

A Vilnius, babban birnin Lithuania, yanzu hukumomin birnin suna amfani da tsutsa wajen sarrafa tarin sharar abincin da jama'a ke fitarwa duk shekara - wannan kuma ya ma haɗa hatta da sharar abincin da ƙananan hukumomi shida da ke maƙwabtaka da birnin.

A ƙiyasi yanzu kuɗin da birnin ya huta kashewa a kan sharar abinci har tan 12,000, ya kai yuro miliyan biyu a duk shekara, in ji shugaban kamfanin Energesman, da ke wannan aiki, Algirda Blazgys.

Yanzu dai kamfanin da ke tattara sharar abincin ya duƙufa wajen gano hanyar da zai mayar da wannan dabara hanyar samun kuɗi.

Kamfanin ya tara ƙudaje kusan miliyan shida a wani wuri na musamman inda suke saduwa a duk bayan sa'a shida.

Matar ƙuda takan saka ƙwai wajen 500 a tsawon kwanakinta na rayuwa galibi 21.

Ta wannan hanya kamfanin yake samun ƙudajen da yake amfani da su wajen sarrafa wannan sharar abinci.

Yadda tsutsotsin ke da saurin cinye sharar abinci shi ya sa suka kasance masu amfani sosai wajen kawar da tarin sharar abinci mai yawa cikin ɗan ƙanƙanin lokaci, kuma hakan ya sa tun da suna ci su ƙoshi su ma ya zama suna ɗauke da sinadarin furotin mai gina jiki inda za a iya amfani da su wajen yin abincin dabbobi ko amfani a masana'antun da ake buƙatar sinadarin na furotin - misali wajen yin fenti da gam da rigar kujeru da sauran abubuwa.

Haka kuma za a iya amfani da kashin wannan tsutsa ta ƙuda a matsayin taki.

Yanzu dai kamfanin Energesman na ci gaba da gwajin irin abubuwan da za a iya yi na tsutsar ta ƙuda har mar ya haɗa hannu da jami'a domin samar da tsutsar don gudanar da bincike.

Baya ga wannan kamfanonin su na sayen tsutsar sosai inda suke amfani da ita wajen kamun kifi.

Sai dai matsala ɗaya a kan wannan shiri ita ce dokokin kiyaye lafiya na Turai ba su yarda a yi amfani da tsutsar ƙuda da aka ciyar da sharar abinci ba wajen yin abincin ƙwarin da mutum yake ci saboda za a iya samun gurɓatar abincin.

Akwai kasashe da wurare da dama da suke amfani da wannan hanya ta amfani da tsutsar ƙuda wajen sarrafa sharar abinci, inda su kuma tsutsotsin ake amfani da su a matsayin hanyar samun sinadarin furotin.

Misali a Kenya akwai shirin da ake kira Project Mila inda ake amfani da tsutsar ƙuda wajen sarrafa tarin sharar abinci ta birnin Mombasa, sannan kuma suna sayar da kashin tsutsar a matsayin taki ga manoma.

A birnin Sydney na Australia ma kamfanin Goterra na gudanar da irin wannan aiki na gwaji, na amfani da tsutsar ƙuda wajen sarrafa sharar tarin abincin da ake fitarwa a birnin, kuma kamfanin ya fara wannan aiki ne a shekarar nan amma kuma tun shekara uku baya yake yi da wasu yankunan ƙananan hukumomi na kusa da birnin na Sydney.

Yanzu dai ba a sani ba ko nan da wani lokaci ƙananan hukumomin biranen Birtaniya za su fara sayo miliyoyin ƙudaje ta yarda za su riƙa amfani da tsutsar ƙudan wajen cinye tan miliyan 6.4 na shara da biranen ke fitarwa.

Shugaban Flybox, Larry Kotch, babban kamfanin da ke amfani da ƙwari wajen sarrafa shara a Birtaniya, yana da ƙwarin gwiwar cewa nan da ɗan lokaci za a kai ga hakan.

Ƙananan hukumomin biranen Birtaniya na da sha'awar hakan kamar yadda Mista Kotch yake gani, saboda daga watan Maris na shekara mai zuwa -2026 zai zama dole a Ingila a duk mako a riƙa tattara sharar abinci

Saboda a yanzu haka kusan ƙananan hukumomi 148 daga cikin 317 na Ingila ba sa yin haka kamar yadda kwamitin bayar da shawara kan sarrafa shara na ƙananan hukumomi ya bayyana.

To amma kuma a yanzu dokokin ma'aikatar kula da muhalli da da abinci da harkokin karkara sun hana ƙananan hukumomi amfani da tsutsar ƙuda wajen sarrafa kayan abinci.

Sai dai Mista Kotch ya ce idan dokoki za su yi aiki bisa tsari da doron kimiyya, yana ganin nan da shekara biyu Birtaniya za ta ga ƙaramar hukumarta ta farko da za ta yi mu'amulla da kamfanin da ke amfani da ƙwari wajen sarrafa shara.

Jami'in ya ce, ''abin takaicin shi ne, har kullum gwamnati za ta ce a'a ne kawai saboda kare lafiya.

To amma kusan duk wanda muka yi wa magana a ƙananan hukumomin na Birtaniya na murna sosai a kan samun sinadarin furotin na ƙwari, kuma sun fi son su yi amfani da ƙwari maimakon sababbin fasahohi.

Zaɓin da ake da shi yanzu bayan zubar da shara a ramuka shi ne na sarrafa sharar ta hanyar ruɓar da ita inda ta hakan ake samun iskar gas da ake makamashi maras gurɓata muhalli (biogas).

Sai dai Mista Kotch ya ce a yanzu kamfanonin da ake wannan aiki na ruɓar da sharar abincin ba su kai yawan da za su iya sarrafa tarin sharar da ake fitarwa daga gidaje ba.

''A fadin duniya ana fitar da sharar abinci sama da tan 1.3 a duk shekara. Kuma mun yi amanna wajen kashi 40 cikin ɗari na wannan sharar za a iya sarrafa ta ta hanyar amfani da ƙwari.'' In ji Mista Kotch.

Shugaban ya ƙara da cewa ta wannan tsari baya ga hutawa da biyan kuɗin zubar da sharar da kuma fitar da tururin sinadarin da ke ɗumama yanayi (methane), hanya ce kuma ta samar da sinadarin furotin mai amfani da kuma takin gargajiya.