Abin da muka sani kan hukumar agaji da ake wa zargin maƙarƙashiya a Gaza

Lokacin karatu: Minti 7

Wata ƙungiya da ake zargi da maƙarƙashiya da ke samun goyon bayan Amurka ta soma aiki a kudancin Gaza.

Wannan ƙungiyar bayar da agajin da ake kira GHF, ta fitar da sanarwar cewa akwai tarin manyan motocin dakon kaya da ke ka hanya ɗauke da kayan agaji zuwa yankunan da ke da sauƙin matsalar tsaro a yankin kudancin Gaza, inda tun a ranar Litinin da ta gabata ta soma raba kayan agajin a kusa da birnin Rafah ga dubban Falasɗinawa.

Shaidun gani da ido a Zirin Gaza sun ce kayan agajin da tuni aka soma rabawa a kusa da birnin Rafah ba su wadatar da dubban Falasɗinawan da ke wurin ba.

Sun ce mutane sun soma ƙwatar abincin daga hukumar da Amurka da Isra'ila suka ƙirƙire ta inda nan take aka soma harbin su. Sai dai ƙungiyar ta musanta haka. Ta ce ta yi ƙoƙarin raba akwatunan abinci har dubu takwas ne kafin mutane su kai ga afka ma cibiyar da ta ke aikin rabon.

Ganau ɗin sun kuma bayyana yanayin yadda ake raba kayan agajin a cibiyar na cike da "hargitsi," inda ake samun cincirinon jama'a da ke ƙoƙarin ƙwatar duk wani abin da ke ɗauke da abinci.

"Sun ba ni wata 'yar akwati da nauyinta bai fi kilo biyar ba," in ji wani da ya shiga layi har a tsawon sa'a takwas yana jiran samun tallafin, "ban san yadda zai ishe ni har da yarana ba, kamar yadda kuke ganin yawan jama'a haka".

Wani ya ce hukumar bayar da agajin na shigar da mutum 50 ne a lokaci guda a cikin cibiyar.

"Daga ƙarshe, rikici ya ɓarke - mutane suka soma tsallaka ƙofar shiga, suna kai wa juna hari, tare da yin wasoso. Lamarin dai babu daɗi gani gaskiya," in ji shi.

"Yunwa ta ci ƙarfinmu. Babu abin da muke muradin samu kamar sukari da burodi matsayin abinci.

A wurin wata mata ta kira da ƙarfi, "Mutane sun tagayyara - a shirye suke su yi kome ma, ko da kuwa zai jefa rayuwarsu a haɗari - kawai don su samu abin da za su ci su da yaransu" in ji.

An kwashe kusan wata uku Isra'ila na ci gaba da hana a shigar da kayan agaji zuwa Gaza. Ƙungiyar Hamas ta ce abin da Isra'ila ta yi na nuna ɗaya daga halayenta na hana bayar da tallafi ga Falasɗinawa.

Ko ya GHF ke tsara shigar da kayan agajin zuwa Gaza?

Ana zargin shirin na ƙungiyar ta GHF da yin wata maƙarƙashiya.

Ƙungiyar dai na amfani da 'yan kwangila Amurkawa da ke ɗauke da makamai, da ke da manufar tsallake Majalisar Ɗinkin Duniya a matsayin manyan masu samar da agajin jinƙai ga mutum miliyan 2.1 a Gaza, inda ƙwararru suka yi gargaɗin yiwuwar ƙaruwar yunwa bayan kwashe mako 11 da Isra'ila ta kwashe tana hana a shigar da abinci sai a kwanan nan.

A cikin maƙarƙashiyar da GHF ke shiryawa akwai cewa dole ne sai Falasɗinawa sun je kudancin birnin Gaza sannan ne za su amshi kayan abincin da sabulai da sauran su.

Kuma an tsara sojojin Isra'ila da 'yan kwangilar daga Amurka ne za su yi sintiri domin tsaron harabar cibiyar. Hakanan kuma idan Falasɗinawa na son kai wa ga kayan agajin dole ne sai an tantance su ta hanyar ɗaukar hoton 'yan yatsu da fuskokinsu domin a gani idan suna da alaƙa da Hamas.

Akwai tarin abubuwan da ma har yanzu ba a kai bayyana su ba.

Me ya sa Majalisar Ɗinkin Duniya da Hamas ke zargin wannan shirin?

Majalisar Ɗinkin Duniya tare da ƙungiyoyin bayar da agaji da dama sun ƙi amincewa su yi haɗin gwiwa da wannan ta GHF, wadda suka ce tsare-tsarenta sun yi hannun riga da manufofin ayukkan jinƙai, sannan ga alama suna amfani ne da "tallafin a matsayin makami".

Kakakin Majalisar Ɗinkin Duniya ya ce ayukkan GHF wani "karkatar da hakali ne daga abin da ainihi ake buƙata" inda ya buƙaci Isra'ila da ta sake buɗe dukan hanyoyin shigar da agaji.

MDD da sauran hukumomin bayar da agajin sun dage kai da fata cewa ba za su yi haɗaka da kowane shirin da ya kasa martaba gimshiƙan ayukan jinƙai.

Sun yi gargaɗin cewa tsarin da ƙirƙirarriyar hukumar ta GHF ke kai ya ware waɗanda ke da larura ta musamman kamar guragu da waɗanda suka samu rauni da ma tsofaffi, inda hakan ya ƙara jefa dubban mutane cikin haɗari da yunwa, kuma hakan ya sa ana yi wa wannan kallon wata siyasar da ake amfani da karfin soji domin cimma wata manufa, wadda kuma ƙasashen duniya ke adawa da ita.

Jan Egeland, shi ne Sakatare Janar na Ƙungiyar Bayar da Agaji ta Norway, kuma tsohon shugaban Hukumar Bayar da Agaji ta Majalisar Ɗinkin Duniya, ya bayyana wannan ƙunigiyar a matsayin ta tsarin "soji, da aka ɗauki nauyi aka siyasantar".

A ranar Litinin ya shada wa BBC cewa "waɗannan da suka ƙirƙiro ta sojoji ne -tsofaffin jami'an Hukumar Leƙen Asiri ta CIA, da tsofaffin jami'an sojoji. Za a dai ce wani gungu ne na jami'an sojoji da suka tsara aiki da ɓangare ɗaya, wato Dakarun Tsaron Isra'ila".

"Ba zai yuwu mu samu ɓangaren da a yaƙi shi zai tsara inda da kuma waɗanda za a ba tallafi ba," in ji shi.

Hamas ta gargaɗi Falasɗinawa da kada ta yarda da manufofin GHF inda suke cewa, "za su kawo hargitsi da shigo da manufofin da za su haifar da yunwa g al'ummar Falasɗinawa, tare da yin amfai da yunwa a matsayin makami a lokacin yaƙi.

Isra'ila ta ce dama akwai buƙatar fito da wata hanya da daban da za ta hana Hamas sace kayan agajin da ake samarwa, duk da yake ƙungiyar ta musanta wani abu mai kama da haka.

Wani kuma da ya ƙara jefa shakku akan ayukan GHF shi ne ganin yadda daraktanta Jake Wood ya bayar da sanarwar sauka daga muƙamin a daren ranar Lahadi sakamakon tsarin da hukumar ke amfani da shi.

Wane ne Jake Wood kuma saboda me ya sauka da muƙaminsa?

Wood wanda tsohon sojan ruwan Amurka ne, ya ce an nemi ya jagoranci GHF watanni biyu kawai da ya taɓa jagorantar ƙungiyar bayar da agaji. Amma daga baya ya bayyana saukarsa daga matsayin daraktan GHF akan abin da ya kira rashin jin daɗain yadda Isra'ila ke da wata manufa game da shirin.

A cikin takardarsa ta ajiye aiki ya bayyana cewa, "Kamar sauran al'ummar duniya, ni ma na ji shakku da fargaba akan irin tsananin yunwar da ake fama da ita a Gaza, sannan, a matsayina na shugaban ƙungiyar bayar da agaji, na yi rantsuwar yin duk abin da zai yuwu domin in fitar da masu fama da wahala halin da suke ciki".

Ya ce "yana alfahari da aikin da ya yi, ciki har da samar da tsare-tsaren yadda za a ciyar da masu fama da yunwa, da samar da tsaro na kuma yaba ƙoƙari na ayukkan ƙungiyoyin agaji masu zaman kansu na tsawon shekaru a Gaza."

Sai dai ya ce ba zai taɓa yabon wannan ƙiƙirarriyar ƙungiya ba "wadda a zahiri ba abu ne me yuwa ka fito da wannan shirin alhali an saɓawa tsarin bayar da agajin jinƙai da kamar rashin nuna ɓangaranci, da adalci da kuma 'yanci waɗanda abubuwa ne da ba zan watsar da su ba."

Daga bisani aka maye gurbinsa da tsohon babban manajan Hukumar bayar da agajin ta Amurka - John Acree.

Ya munin yadda yanayin ya ke a yanzu?

Isra'ila ta hana shigar da kayan agajin jinƙai zuwa Gaza tun daga ranar 2 ga watan Maris, ta kuma ci gaba da mamaya makonni biyu da suka gabata, abin da ya kawo ƙarshen yarjejeniyar tsagaita wuta tsakaninta da Hamas bayan tsagaitawar wata biyu da aka samu.

Ta ce matakin na da zimmar matsawa ƙungiyar mai ɗauke da makamai ta saki mutum 58 da ta ke garkuwa da su a Gaza waɗanada aka yi amannanr har yanzu 23 na raye.

A ranar 19 ga watan Mayu sojojin Isra'ila sun ƙara faɗaɗa mamayar da Firaminta Benjamin Natanyahu ya ce suna neman "dakarun sojojin sun karɓe iko da daukan yankunan" Gaza. Shirin na da manufar kore mazauna arewacin Gaza inda za a kora su zuwa kudancin birnin.

Natanyahu ya kuma ce Isra'ila za ta buɗe ƙofa na ɗan lokaci domin shigar da "muhimman" kayan agaji misali abinci zuwa Gaza domin hana ƙaruwar yunwa, amma duk wannan ya faru bayan fuskantar matsain lamba daga wajen Is'raila.

Tun daga lokacin, hukumomin Isra'ila suka ce sun buɗewa motocin ɗaukara kaya 665 da ke ɗauke da kayan agaji da suka ƙumshi garin fulawa da abincin jarirai da magungunna.

Har ila yau, a ranar Lahadi shugaban Shirin Samar da Abinici na MDD ya ce kayan agajin "wani ɗan yanki" ne kawai na abin da ake buƙata a lardin idan ana son a kawar da yunwar da dubban jama'a ke fama da ita, wanda hakan ya ƙara tsashin farashin kayan abinci.

A cewar wani shirin da ke yaƙi da yunwa mai samun talafi daga Majalisar Ɗinkin Duniya kimanin mutum rabin miliyan ne za su fuskantar tsananin yunwa nan da watanni masu zuwa.

Isra'ila ta ƙaddamar da farmakin soji a Gaza a matsayin martani kan wani harin da ƙungiyar Hamas ta kai a ranar 7 ga watan Oktoban 2023, wanda kimanin mutum 1,200 suka mutu kana aka yi garkuwa da wasu 251.

Ma'akatar Lafiya da Hamas ke tafiyarwa ta bayyana cewa aƙalla mutum 54,056 aka kashe a Gaza tun daga lokacin somawar rikicin, da suka haɗa da fiye da ƙarin wasu 3,901 a cikin makonni 10 da suka gabata.