Ƴansanda sun hana hawan sallah a Kano

...

Asalin hoton, Sani Maikatanga

Lokacin karatu: Minti 1

Rundunar ƴansandan Najeriya a jihar Kano ta sanar da haramcin yin hawan sallah a lokacin bukukuwan ƙaramar sallah da ke tafe.

Kwamishinan ƴansanda a jihar, Ibrahim Adamu Bakori, ne ya bayyana haka lokacin da ya yi taron manema labarai a shalkwatar rundunar da ke birnin Kano.

Kwamishinan ya ce sun ɗauki matakin ne saboda bayanan sirri da suka samu game da yunƙurin tayar da fitina.

"Wannan mataki ya zama dole bayan tattaunawa da hukumomin da suka dace saboda bayanan sirri da ke nuna cewa wasu da aka ɗauka haya da masu gidansu za su fake da hawan sallar domin tayar da fitina," in ji kwamashinan.

Matakin rundunar ta 'yansanda ya saɓa da aniyar da gwamnan jihar na Kano ya nuna na yin hawan, inda ya nemi dukkan masarautun Kano huɗu ƙarƙashin jagorancin Sarki Muhammadu Sanusi II da su shirya aiwatar da hawan.

Kazalika, shi ma Sarki Sanusi ya aika wa hukumomin tsaron jihar wasiƙa yana mai sanar da su shirinsa na gudanar da bikin al'adar da aka saba yi duk shekara.

Zuwa yanzu gwamnatin jihar ta jam'iyyar NNPP mai adawa a Najeriya da masarautar Kano ba su ce komai ba game da batun.

Sanarwar haramcin na zuwa ne kwana ɗaya bayan Sarkin Kano na 15 Aminu Ado Bayero ya sanar da soke shirinsa na yin hawan kamar yadda ya tsara tun farko, yayin da yake ci gaba da bayyana kansa a matsayin sarki duk da matakin gwamnatin Kano na sauke shi.

Cikin wani jawabi da aka wallafa a shafukan sada zumunta, Aminu Ado ya ce sun yanke hukuncin dakatar da hawan ne saboda "shawarwarin da malamai da iyaye da 'yanmajalisa" suka bayar.

"Muna tabbatar muku cewa mu a wajenmu hawan sallah ba abu ne na ko a mutu ko a yi rai ba, idan har zai zama sanadiyyar kawo tashin hankali da hargitsi lallai ya zama wajbi mu haƙura," a cewarsa.