Kotun Duniya: Me ya sa take sauraron zargin Isra'ila da kisan ƙare-dangi?

Palestinian boys are seen in the rubble of a building destroyed by an Israeli attack in Rafah, Gaza on 3 January 2024

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Mafi yawa matada ƙananan yara ne suka fi mutuwa a hare-haren da Isra'ila ke kaiwa Gaza tun bayan fara samamen soji a yankin
    • Marubuci, Aine Gallagher
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC World Service

Lamarin ya kasance shari'ar kotu da ba taɓa gani ba a tsawon ƙarni. A ranar 11 da 12 ga watan Janairu ne, lauyoyi da ke wakiltar Afirka ta Kudu da Isra'ila za su shiga zauren kotun domin ci gaba da ƙarar da al'ummar duniya za ta kalla.

Shin Isra'ila ta aikata laifin kisan kiyashi a kan al'ummar Falasɗinawa? Afirka ta Kudu ta ce ta shigar da ƙara gaban kotun duniya da ke birnin Hague ranar 29 ga watan Disamban 2023.

Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya ce ƙasarsa na fama da suka kan yaƙin da take yi a Gaza, yayin da mai magana da yawun gwamnatin ƙasar ya alaƙanta ƙarar Afirka ta Kudun da ''zubar da jini'' a wani zargin ƙarya da aka ce Yahudawa sun yi wa Kiristoci domin amfani da jininsu a lokacin daɗaɗɗun al'adun tsafin da suka gabata.

Mece ce ƙarar Afirka ta Kudu?

A takardun ƙarar mai shafi 84, Afirka ta Kudu ta ce ayyukan isra'ila ''Kiyasin kiyashi ne idan aka yi la'akari da yanayinsu, saboda ta yi ne da nufin wargaza mafi yawan yankin Falasɗinawan da ke zaune a Gaza.

Ta ce zargin kisan ƙare dangi da ake yi wa Isra'ila sun haɗar da kisan Falasdinawa, da jefa su cikin tsananin damuwa da raunuka a jikinsu.

''Sannan ta sanya mutanen yankin cikin wani yanayi na ƙunci da lalata musu yanki''. Kuma ta ce kalaman da jami'an Isra'ila ke furtawa suna nuna aniyar kisan ƙare dangi.

Juliette McIntyre, malamar fannin sharia a ce a a jami'ar Kudancin Australiya, ta kuma ce ƙarar da Afirka ta Kudun ta shigar Cikakkiya ce kuma an ''tsarata yadda ya kamata''.

"Ta buƙaci mayar da martani kan duk wani iƙirari da Isra'ila ta yi... sannan ta mayar da martani kan duk wani ikirari na cewa kotun ba ta da hurumin ƙarar,'' kamar yadda ta shaida wa BBC.

"Afirka ta Kudu ta ce ta tattauna batun da Isra'ila ne ta hanyoyi da dama kafin ta shigar da ƙarar.''

Chairs sit beside piles of burned debris sifted to find human remains, as Israeli residents of the Nir Oz kibbutz grapple with being overrun by Palestinian Hamas militants from the nearby Gaza Strip on 6 December 2023

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Mayaƙan Hamas sun kai hari garin kibbutz na Nir Oz a Isra'ila da ke kusa da kan iyakar Gaza ranar 7 ga watan Oktoba

Mene ne martanin Isra'ila?

Mai magana da yawun gwamnatin Isra'ila Eylon Levy ya Isra'ilar za ta mayar da martani kan ƙarar. Ya kuma ce Hamas ce ta haddasa faruwar wannan yaƙin.

Mene ne kisan ƙare-dangi?

Ƙarƙashin dokar kisan ƙare-dangi ta Majalisar Dinkin Duniya ta 1984, shi ne aikata wani abu da nufin lalata ko kawar da gaba ɗaya ko wani ɓangare na ƙasa ko ƙabila ko wata ƙungiyar addini da suka haɗar da:

  • Kisan mambobin ƙungiyar
  • Haifar da damuwa da raunuka ga mambobin ƙungiyar
  • Jefa mutane cikin wani ayuwacin hali na rayuwa ta hanyar illata wasu sassan jikinsu
  • Ƙaƙaba wasu dokoki da nufin hana su haihuwa
  • Tursasa mayar da ƙananan yaran kungiyar zuwa ga wata ƙungiyar

Kisan ƙare-dangi na ɗaya daga cikin manyan laifukan da ke da wahalar tabbatarwa

A general view on the Peace Palace prior to a public hearing in Ukraine against Russia at the International Court of Justice, the Hague, the Netherlands on 6 June 2023

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Kotun Duniyar na da mazauni a fadar 'Peace Palace' da ke birnin Hague na ƙasar Netherlands

Wa za a zarga da kisan ƙare-dangi?

Za a iya zargin wani mutum ko wata ƙasa da aikata kisan ƙare-dangi.

Michael Becker, malamin shari'a a jami'ar Dublin, ya ce akwai bambanci tsakanin yadda za a samu ƙasa da karya dokar kisan ƙare-dangi da yadda za a samu wani mutum da aikata laifin.

"Wannan bambanci na da sarƙaƙiya kuma na haifar da ruɗani,'' in ji shi.

Wacce rawa kotun ke takawa?

Kotun ta kasance babbar kotun Majalisar Dinkin duniya wadda ke sauraron ƙararraki tsakanin ƙasashe. Duka ƙasashen da ke ƙarƙashin Majalisar Dinkin Duniya mambobi ne na kotun.

Ƙasa na damar shigar da ƙara a gaban kotun, wadda ke da alƙalai 15 da babban zauren MDD da kwamitin tsaro na Majalisar ke zaɓa domin aikin wa'adin shekara tara.

Daya daga cikin manyan dalilan kafa kotun shi ne sauraron batutuwan kisan ƙare-dangi da aka aikata a shekarar 1984.

Yahudawa miliyan shida ne ƙungiyar Nazi ta kashe a Turai lokacin Yakin Duniya na Biyu daga shekarar 1939 zuwa 1945.

Bayan ƙarewar yaƙin ne shugabannin duniya suka yi nazarin kafa kotun da nufin hana faruwar hakan a nan gaba.

Isra'ila da Afirka ta Kudu Myanmar da Rasha da Amurka na daga cikin ƙasashe 153 da suka sanya hannu a kafuwar kotun.

An exterior view of the International Criminal Court in the Hague, Netherlands on 31 March 2021

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Ita ma kotun hukunta manyan laifuka, na da matsuguni a birnin Hague, sai dai ita ɗaiɗaikun mutane take tuhuma

Mene ne aikin Kotun Manyan Laifuka ta Duniya?

An kafa kotun hukunta manyan laifuka ta duniya (ICC) a shekarar 2002, kuma tana da matsuguni a birnin Hague. Ta kasance kotun ƙarshe da ake kai ƙara idan kotunan ƙasa suka kasa warware wata matsala.

Kuma Amurka da Rasha da Isra'ila ba sa cikin mambobin kotun.

Kotun ICC na sauraron ƙararraki tare da yankewa mutuane hukunci kan aikata laifukan yaƙi, da muzgunawa bil'adama da kare-dangi.

Duka kotunan biyu na da mabambantan ma'anoni da dalilan kafa su a doka.

Mai shigar da ƙara a kotun ICC ne zai iya fara ko buɗe shari'a.

Wa aka samu da laifin kisan ƙare-dangi?

Mutum na farko da aka fara samu da aikata laifin kisan kiyashi shi ne Hutu Jean-Paul Akayesu na ƙasar Rwanda a shekarar 1998, a wata kotun da MDD ta kafa domin sauraron zarge-zargen da ake yi masa a kisan kiyashin da aka yi wa 'yan ƙabilar Tutsi kimanin 800,000 a shekarar 1994.

A shekarar 2017 kotun duniya ta musamman ka manyan laifuka da aka kafa kan tsohuwar Yugoslavia ta samu tsohon kwamandan Bosnian Serb Ratko Mladic da laifin kisan ƙare-dangi a kisan kiyashin Srebrenica, inda sojojinsa suka kashe musulmai 8,000 ciki har da ƙananan yara.

A woman is seen near a family grave at the Memorial centre Potocari near Srebrenica, Bosnia and Herzegovina on 20 March 2019

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Kisan kiyashin Srebrenica ya faru ne a watan Yulin 1995 a lokacin yakin tsohuwar Yugoslavia

To sai dai kotun duniya ta yi watsi da ikirarin Bosniya na cewa Sebiya, ko kuma tsohuwar Yugoslavia, kai-tsaye ta aikata kisan ƙare-dangi a Srebrenica.

A maimakon haka, kotun ta ce Sabiya ta kasa hana kisan ƙare-dangin sannan ta aike wa manyan janar-janar.

Mista Becker, wanda ke aiki a matsayin lauya a kotun, ya ce kotun na da tagawar manyan lauyoyin da za su bincike batun kisan ƙare-dangi da aka zargi wata kasa da aikatawa.

Mene ne yaƙin Isra'ila da Gaza?

Rikicin ya faro ne ranar 7 ga watan Oktoban 2023, a lokacin da mayaƙan ƙungiyar Hamas suka kutsa cikin Israila tare da ƙaddamar da hare-hare tare da kashe Israilawa 1,200, da kuma yin garkuwa da fiye da 200.

tun daga lokacin ne, Isra'ila ta ci gaba da kai hare-hare ta sama, tare da ƙaddamar da samame ta ƙasa da kuma umartar Falasɗinawa da su fice daga yankin arewacin Gaza zua kudanci.

Sannan kuma ta hana shigar da abinci da man fetur zuwa yankin.

Ma'aikatar lafiyar Hamas da ke Gaza ta ce fiye da mutum 22,000 ne aka kashe kawo yanzu mafi yawansu mata da ƙananan yara.

Isra'ila da Birtaniya da Amurka da sauran ƙasashen Yamma sun ayyana Hamas a matsayin ƙungiyar ta'addanci.

Israeli army humvees and vehicles move along a dirt road in the Gaza Strip near a position along the border with southern Israel on 4 January 2024

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Isra'ila ta ce manufar yaƙin da take yi shi ne kawar da ƙungiyar Hamas, da sakin mutanenta da kungiyar ke garkuwa da su, tare da tabbatar da cewa Gaza ba ta zama barazana a gareta ba a nan gaba

Me zai faru ranekun 11 da 12 ga Janairun 2024?

Afirka ta Kudu ta shigar da ƙara a gaban kotun inda take neman kotun ta ɗauki matakan umartar Isra'ila ta dakatar da sojojinta daga kai hare-hare a Gaza. Wannan ce hanyar gaggauta fara sauraron ƙarar.

"Wannan ba zai kai ga gano laifukan kisan ƙare-dangi ba a wanan mataki," in ji Ms McIntyre.

Afirka ta Kudu na cewa akwai ''yiyuwar hatsarin faruwar kisan ƙare-dangi'', kamar yadda Ms mcIntyre ta bayyana.

Ƙasar Ukraine ta shigar da makamancin wanna ƙara a lokacin da Rasha ta mamayeta ranar 24 ga watan Fabrairun 2022, inda kotun ta umarci Rash da ta dakatar da ayyukan sojinta a Ukraine makon bayan shigar da ƙarar, matakin da Moscow ta yi watsi da shi.

Wounded people, including children, are brought to Al-Aqsa Martyrs Hospital for treatment following Israeli attacks in Deir al-Balah, Gaza on 4 January 2024

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, MDD ta ce Gaza na da asibitoci 13 ne kawai da ke aiki sama-sama, sai kuma wasu guda biyu da kaɗan-kaɗan, sai kuma 21 da suka daina aiki.

Misis McIntyre na sa ran cewa kotun ta ICJ za ta yanke hukunci kan batun zuwa ƙarshen watan Janairu.

"Wannna mataki zai sanya matsin lamba kan Isra'ila.'' in ji Ms McIntyre, amma ta ƙara da cewa ba shi ne ƙarshe ba, kuma kotun ba za ta iya tilasta wa Isra'ila aiki da hukuncin da za ta yanke ba.

"Kotun za ta iya samun ba a aikata kisan ƙare-dangi ba, idan ta duba hujjojin wanda ake ƙara.''

Mista Becker ya ce hukuncin kotun ICJ na hana Rasha mamayar soji kan Ukraine ya zama tamkar na je-ka-na-yi-ka.

"Ina da shakku idan kotun za ta iya tilasta wa Isra'ila dakatar da yaƙin,'' in ji shi, ya ce abin da yake tunani shi ne kotun ta tailasta wa Isra'ila ''rage'' hare-harenta a Gaza.

"Abin da hakan ke nufi shi ne dole Isra'ila ta bi dokokin duniya kan ka'idoji sharia'a da take da su," in ji shi.

Yaya ake sauraron ƙarar kisan ƙare-dangi a kotun?

Misis McIntyre ta ce ƙarar da za a iya kwatanta wannan da ita, ita ce ƙarar kisan ƙare-dangi da Gambiya ke zargin ƙasar Myanmar da yi wa al'ummar Rohingya.

Falasɗinawa a Gaza da 'yan ƙabilar Rohingya a aMyanmar ba su da damar zuwa kotun ta ICJ, saboda su ba ƙasashe ba ne, don haka wasu ƙasashen ke shigar da ƙara a madadinsu.

A Rohingya Muslim woman reacts while holding her child, as they are relocated from their temporary shelter in Banda Aceh, Indonesia following protests on 27 December 2023

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Kusan 'yan ƙabilar Rohingya miliyan ɗaya ne suka fice daga Myanmar a 2017 inda a yanzu wasu daga cikinsu ke jefa rayukansu cikin hatsari wajen yin tafiya a jiragen ruwa domin zuwa Indonsiya

Gambiya ta shigar da ƙara a madadin ƙasashen musulmai, inda take zargin Myanmar da aikata kisan ƙare-dangi kan 'yan ƙabilar Rohingya bayan kusan 'yan ƙabilar miliyan guda sun fice daga ƙasar zuwa Bangladesh mai maƙabtaka a 2017.

A ƙarshen shekarar 2023 ne Birtaniya da denmar da Faransa da Jamus da kuma Netherlands tare da Canada suka nuna sha'awar shiga cikin ƙarar, ma'ana za su nuna adawa da ƙarar.

"Alama ce ga duniya cewa kotun za ta goyi bayan abin da suke so,'' in Misis McIntyre.

Ƙasashen Yamma sun nuna makamancin wannan mataki inda suka goyi bayan Ukraine a kotun.

Amma Misis McIntyre na ganin ƙasashen Yamma da dama za su goyi bayan watsi da ƙarar.

"Ba na tunanin ƙasashen Yamma za su goyi bayan Afirka ta Kudu,'' in ji ta.

"Abin tambayar a nan shi ne, ko ƙasashen Larabawa za su mara wa Afirka ta Kudun baya."

Palestinian citizens carrying their belongings leave their homes in Al-Maghazi refugee camp to seek safer places in the city as Israeli attacks continue in Deir al-Balah, Gaza on 4 January 2024.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, MDD ta ce kusan kashi 85 na mutanen da ke zaune a Gaza sun rasa muhallansu, inda wasu suka rasa muhallan a lokuta da dama

Yaushe ake sa ran yanke hukunci?

Gambiya ta shigar da ƙararta a watan Nuwamban 2019, to amma har yanzu ba a kai ga sauraron shari'ar ba. Don haka hukuncin ƙarshen zai iya ɗaukar shekaru masu yawa.

Idan kotun ICJ ta samu Isra'ila da laifin aikata kisan ƙare-dangi a Gaza, Misis McIntyre ta ce daga baya za a iya amfani da shi a matsayin hujja kan wani duk wata ƙara da aka shigar da wani mutum a kotun hukunta manyan laifuka ta ICC.

Masana sharia'r biyu sun amince cewa hukunta Isra'ila a wannan shari'a ka iya zama darasi ga sauran ƙasashe musamman magoya bayan Isra'ila wajen sake nazarin alaƙarsu da ita.

Haka kuma Amurka ta riga ta fito ƙarar ta soki Afirka ta Kudu kan matakin, inda kakakin ma'aikatar tsaro ta fadar White House John Kirby ya ce ƙarar ba ta da ''makama'' kuma gaba-ɗaya ''ba ta da tushe balle makama''.