''Matasan yanzu ba su damu da karanta jarida ba''
''Matasan yanzu ba su damu da karanta jarida ba''
Dahiru Musa wani mazaunin birnin Kano ya ce ya fara harkar sayar da jarida shekara kusan 35 da suka wuce
Ya ce cinikin jarida a yanzu ya yi rauni, idan aka kwatanta da baya, yana mai cewa a baya yana ɗauko jarida kofi 500, kuma ta ƙare sakamakon rububin sayenta da mutane ke yi, amma yanzu ya ce bai fi ya sayar da kofi 10 ba.
Ya ci gaba da cewa matasan yanzu ba su damu da karanta jarida ba, kamar mutanen da 'yan boko.



