Abu uku da zan mayar da hankali kansu idan na zama shugaban ƙasa - Sowore

Bayanan bidiyo, Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyon
Abu uku da zan mayar da hankali kansu idan na zama shugaban ƙasa - Sowore

Ɗan takarar shugabancin Najeriya ƙarƙashin jam'iyyar AAC, Omoyele Sowore, ya ce zai mayar da hankali kan abu uku idan ya samu nasarar zama shugaban ƙasar a babban zabe na 2023.

Mista Sowore ya ce dalilin da ya sa yake takarar shi ne don ya ci zaɓen shugaban ƙasar kuma ya yi wa 'yan Najeriya abin da ya dace.

Ya ci gaba da cewa dalilin da ya sa ƙasar ke cikin matsaloli shi ne ana zaɓar 'yan takarar da ba su da wani abin da za su iya bayarwa ga Najeriya.

''Ina ganin ya dace lokacin zaɓe mutane su faɗi duk abin da suke so game da 'yan takara, wadanda suka tsaya takara'', in ji mista Sawore.