Ku San Malamanku tare da Limamin Masallacin Juma'a na Gandun Albasa
Ku San Malamanku tare da Limamin Masallacin Juma'a na Gandun Albasa
Shirin Ku San Malamanku na wannan makon ya yi hira ne da Sheikh Ahmad Muhammad Badayi, limamin masallacin Juma'a na Gandun Albasa.
Ya ce shi tun yana yaro ya taso cikin karatu a hannun kakansa, wanda malamin makarantar allo ne.
Daga baya ya koma yin karatun hannun mahaifinsa da na Kur'ani da sauran littattafai.
Shehin malamin ya ce ya taa karatun zamani amma shi ma mai alaƙa da karatun Arabi ne duk a cikin birnin Kano.
Ku kalli bidiyon don jin cikakken tarihin malamin.



