Marcelo ya yi ritaya daga taka leda

Asalin hoton, Getty Images
Ɗan bayan Brazil, kuma tsohon ɗan wasan Reald Madrid, Marcelo, ya sanar da yin ritaya daga wasan ƙwallon ƙafa yana da shekara 36.
Ɗan bayan da ke taka leda a ɓangaren hagu, wanda ya kasance ɗaya daga cikin 'yan wasan da suka fi cin kofuna a tarihin ƙwallon ƙafa ya yi wa Brazil wasa sau 58.
An haifi Marcelo Vieira da Silva Júnior, a birnin Rio de Janeiro, na Brazil, ranar 12 da watan Mayu na 1988.
Bayan da ya fito daga ƙungiyar Fluminense, ta Brazil yana matashi, Marcelo tafi Real Madrid a 2007 yana shekara 18 da haihuwa.
Ya ɗauki manyan kofuna 25 a cikin shekara 15 da ya yi a Bernabeu, ciki har da Kofin Zakarun Turai ( Champions League) biyar da kuma na gasar Sifaniya ta La Liga shida.
A wani hoton bidiyo da ya sanya a shafinsa na sada zumunta da muhawara, ya bayyana cewa : "Ina shekara 18, Real Madrid ta zo ta ƙwanƙwasa min ƙofa, kuma na zo nan. Yanzu zan iya alfahari da cewa ni cikakke ɗan birnin Madrod ne.''
Ya ce, ''tafiyata a matsayin ɗanwasa a nan ta ƙare, to amma har yanzu ina da gudummawa da yawa da zan bai wa ƙwallon ƙafa. Na gode muku a kan komai."
A shekara ta 2021 ne aka naɗa Marcelo, kyaftin ɗin ƙungiyar, inda ya zama kyaftin ɗin ƙungiyar na farko wanda ba ɗan Sifaniya ba a cikin shekara 117.
Shugaban Real Madrid Florentino Perez ya ce: "Marcelo na ɗaya daga cikin manyan 'yan bayan a tarihin Real Madrid da wasan ƙwallon ƙafa a duniya, kuma mun samu damar cin moriyarsa tsawon lokaci.
"Yana ɗaya daga cikin manyan tsofaffin taurarinmu kuma har kullum Real Madrid za ta ci gaba da kasancewa gidansa."
Marcelo ya bar Madrid a ƙarshen kakar 2021-22 inda ya tafi ƙungiyar Olympiacos, ta Girka, amma kuma ya kawo ƙarshen kwantiraginsa bayan wata biyar kawai a ƙungiyar.
Ɗanwasan ya sake komawa ƙungiyar da ya taso a cikinta yana yaro wato Fluminense a 2023 inda ya yi kaka biyu, ya yi mata wasa 68.
A watan Nuwamba da ya gabata suka raba gari da ƙungiyar bayan da suka yi sa-in-sa a bainar jama'a da kociyan ƙungiyar Mano Menezes.











