Waiwaye: Fashewar nakiya a Ibadan da nasarar Najeriya a Afcon

Wannan maƙala ce da ke kawo muku muhimman batutuwan da suka faru a Najeriya cikin makon da muke bankwana da shi.

Fashewar wani abu ya janyo ruɗani a Ibadan

Da maraicen ranar Talata ne kuma wata fashewa ta auku a birnin Ibadan na jihar Oyo wadda kuma ta janyo ruɗani.

Fashewar ta yi sanadin ta ruguza gine-gine da dama saboda mummunar jijjiga.

Kafofin yaɗa labarai a Najeriya sun ruwaito cewa motoci da gidaje sun tarwatse a yankunan Awolowo, Bodija, Akobo da kuma sauran yankuna.

Rahotonni sun ce fashewar ta faru ne sakamakon kayan haƙar ma'adinai.

Gwamnan jihar, Seyi Makinde ya tabbatar da mutuwar mutum biyu, yayin da wasu mutum 77 suka jikkata.

Buhari bai taɓa min katsalandan ba - Tinubu

A cikin makon da muke bankwanan da shi ne Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya bayyana cewa wanda ya gada tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari bai taɓa yi masa katsalanda a gwamnatinsa ba tun bayan barin mulki.

A lokacin taron ƙaddamar da wani littafi da aka rubuta kan rayuwar tsohon shugaban ƙasar, shugaba Tinubu ya ce bayan miƙa masa mulki da Buhari ya yi, tsohon shugaban ƙasar ya koma mahaifarsa Daura, inda ya ce ya yi hakan ne don guje wa yin katsalandan ga sabon shugaban ƙasar

Tinubu ya ce maimakon katsalanda, Buhari ya haɗa gwiwa da shi don ganin dimkraɗiyya ya wanzu a ƙasar.

Tinubu ya gana da manyan hafsoshin tsaro

A cikin makon ne kuma Shugaba Bola Tinubu na Najeriya ya gana da manyan hafsoshin tsaron ƙasar da kuma wasu shugabannin hukumomin tsaro a fadarsa da ke Abuja.

Hafsoshin tsaron da suka halarci ganawar sun haɗa da babban hafsan tsaro, Janar Christopher Musa, shugaban rundunar sojin ƙasa, Laftanar-Janar Taoreed Lagbaja, shugaban sojin sama, Air Marshal Hassan Abubakar, da kuma shugaban sojojin ruwa, Vice Admiral Emmanuel Ogalla.

Shi ma mai taimaka wa shugaban ƙasa kan harkokin tsaro, Malam Nuhu Ribadu na cikin waɗanda suka halarci taron.

Ganawar na zuwa ne a daidai lokacin da batun tsaro ke ƙara taɓarɓarewa a ƙasar, musamman babban birnin ƙasar Abuja, inda ake samun ƙaruwar yawaitar ayyukan masu garkuwa da mutane.

Tawagar Najeriya ta ci wasanta na biyu a gasar Afcon

A ranar Alhamis ne kuma tawagar Super Eagles ta Najeriya ta ci wasanta na biyu a gasar Afcon da ke gudana a ƙasar Ivory Coast.

Najeriya ta samu nasara da ci 1-0 a kan ƙasar Ivory Coast mai masaukin baƙi a gasar. wasan farko da ƙungiyar ta buga ƙarshen makon da ya gabata ta tashi 1-1 da ƙasar Equatorial Guinea.

A yanzu Super Eagles na mataki na biyu cikin rukunin A da maki 4 iri ɗaya da na Equatorial Guinea da ke mataki na ɗaya.

'Yan sanda a Kaduna sun kuɓutar da mutumin da aka yi garkuwa da shi a Abuja

A cikin makon ne kuma rundunar 'yan sandan jihar Kaduna ta kuɓutar da wani mutum da masu garkuwa da mutane suka kama a Abuja suka kuma nufi jihar da shi.

Cikin wata sanarwa da rundunar ta fitar ta ce ta kuɓutar da mutumin wanda aka yi garkuwa da shi a Abuja babban birnin ƙasar ranar Laraba da maraice.

Rundunar ta ce a ranar Alhamis 18 ga watan Janairu ta samu rahoton yin garkuwa da wani mutum a Abuja, inda aka yi zargin masu garkuwar sun tafi da mutumin da suka sacen zuwa jihar Kaduna.

Daga nan ne rundunar ta ce jami'anta suka riƙa sanya idanu kan zirga-zirgar motocin da ke shiga jihar daga birnin na Abuja.