APC bangaren Ganduje a Kano ta ce shan kaye a kotu ba zai sa su karaya ba

Asalin hoton, SALIHU TANKO YAKASAI
Jam'iyar APC bangaren gwamnatin jihar Kano a Najeriya ta ce har yanzu ba ta karaya ba, duk da cewa kotun daukaka kara a Abuja ta kara tabbatar da hukuncin da wata kotu ta yi a baya, na sahihancin zaben shugabannin jam'iyyar bangaren tsohon gwamna Sanata Ibrahim Shekarau.
Tunda farko kotu ta halatta jagorancin ɓangaren Shekarau, wanda ya ƙalubalanci cewa ɓangaren Gwamna Abdullahi Umar Ganduje bai gudanar da zaɓukan mazaɓu ba.
To amma nan take ɓangaren Ganduje ya nemi a dakatar da ci gaba da shari'a saboda akwai giɓi, a cewarsa.
Sai dai kuma a zaman na ranar Juma'a kotun daukaka kara ta tabbatar da sahihancin zaɓukan da ɓangaren Shekarau ya gudanar a daukaka karar da bangaren gwamnatin ya yi.
Hakan ya nuna cewa kotun ta rusa shugabancin APC na Abdullahi Abbas wato ɓangaren Gwamna Ganduje kenan.
Bugu da kari alƙalin kotun mai shari'a Hamza Mu'azu ya kuma buƙaci ɓangaren Gwamna Ganduje (wanda shi ne ya shigar da kara) ya biya tarar naira miliyan ɗaya, kamar yadda Sha'aban Sharada ɗan majalisar tarayya daga jihar Kanon, kuma dan bangaren Ahmadu Haruna Zago ya shaida wa BBC.
Toh amma BBC ta tuntubi Kwamishinan Yada Labarai na jihar Kano, Malam Muhammad Garba, wanda ya bayyana cewa tabbas hukuncin kotun bai musu dadi ba, sai dai kuma hakan ba yana nufin sun karaya ba.
" Ai indai cikakken dan siyasa ne kai ba maganar gwuiwarka ta yi sanyi, magana ce ta gwagwarmaya," in ji shi.
Ya kara da cewa, " Na tabbatar da cewa tun da magana ce ta gida daya daga nan zuwa wani lokaci za a samu daidaituwa, za a zauna kuma abubuwa za su daidaita."
Duk da Kwamishinan ya ce ba zai yanke hukuncin mataki na gaba ba don ba huruminsa ba ne, amma ya tabbatar da cewa " idan uwar jam'iyya ta ga cewa za a tafi har Kotun Koli to ka ga ai ba za a iya cewa a'a ba."
A kan haka ya ce a yanzu za su jira matakin shugabancin jam'iyar na kasa da tuni ya fara nazari, kuma idan sun kammala nazari za su tuntube su don jin matakin na gaba.
Sai dai kuma ya ce tuni manyan masu fada a ji a jam'iyyar APC suka fara shiga tsakani, don ganin an dinke barakar tsakanin bangarorin biyu.











