EFCC ta mayar wa CBN kudi sama da naira biliyan 19 da aka boye

Asalin hoton, BBC HAUSA
Hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC ta ce ta mayar da kudaden ceto tattalin arziki na naira biliyan 19.3 ga babban bankin Najeriya wanda ake zargin gwamnatin jihar Kogi ta boye .
Tun farko hukumar ta bayyana cewa gwamnatin Yahaya Bello ta boye kudin a asusun wani banki.
Gwamnatin jihar Kogin ta musanta zargi kuma ta zargi EFCC da kokarin shafa mata kashin kaji.
Sai dai a wata sanarwa a ranar Juma'a ,kakakin hukumar, Wilson Uwujaren, ya ce an tura da kudaden zuwa babban bankin.
"Babban bankin Najeriya ,CBN, ya amince da karbar kudi, naira 19,333,333,333.36 wanda EFCC ta kwato daga asusun ajiyar kudi na bankin Sterling kan tallafin da aka bata domin biyan albashi. Wannan ya kawo karshen bayannan karya da zargin da gwamnati jihar Kogi ta rika musantawa a kan cewa ba a gano kudi a cikin asusunta na gudun bacin rana ba".in ji hukumar ta EFCC
A cikin wata wasika da babban bankin Najeriyar ya rubutawa shugaban hukumar ta EFCC, Abdulrasheen Bawa ya ce kudaden sun shiga hanunsu.
Hukumar ta ce ta mayar da kudaden zuwa ga babban bankin Najeriya sakamakon umarnin da wata babbar kotu a Lagos ta bayar inda ta umarci bude asusun ajiyar kudi na albashi na gwamnatin jihar Kogi domin bankin Sterling ya saka kudin a cikin asusun babban bankin Najeriya. Alkalin kotun , mai sharia, Chukwujekwu Aneke ne ya hukucin bayan da EFCC ta gabatar da kara a kotun.
"Hukumar ta EFCC ta fadawa kotun cewa babban daraktan bankin ya amince da cewa akwai kudi da yawansu ya zarce naira biliyan 19 ajiye a bankin".
Ta kuma ce banakin ya amince da cewa zai mayarwa babban bankin Najeriya da kudin
Hukumar ta kuma kara da cewa ''Kudaden da aka mayar ya kawo karshen duk wani ce-ce ku-ce a a kan asalin kudi da kuma mamallakin kudin kuma ya hana karkatar da kudaden''
A ranar 31 ga watan Agusta wata kotu ta bada umarnin dakatar da asusun bayan da hukumar EFCC ta shigar da kara gabanta.










