Hafsat Ganduje: EFCC 'ta yi wa matar Ganduje tambayoyi' kan zargin rashawa

Goggon Ganduje

Asalin hoton, KNSG

Lokacin karatu: Minti 2

Hukumar EFCC da ke yaƙi da cin hanci da rashawa a Najeriya ta kama Hajiya Hafsat uwargidan gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje, kan tuhuwar rashawa da zambar fili da ɗanta ya kai kararta.

Wata majiya daga fadar gwamnatin jihar da ta buƙaci a sakaya sunanta ta tabbatar wa BBC lamarin.

Majiyar ta ce jami'an hukumar EFCC ne suka je har Kano suka kuma tafi da "Goggo" kamar yadda ake kiran ta, zuwa Abuja, don amsa tambayoyi.

Amma ya ce tuni aka kammala kuma har ta koma gida.

Tuhumar da aka yi wa matar Ganduje na zuwa ne makonni bayan ƙin amsa gayyatar hukumar ta EFCC da rahotanni a Njeriya suka ce ta yi.

Jaridun ƙasar sun ce ɗan Hafsat Ganduje Abdualzeez Ganduje ne ya kai karar mahaifiyarsa gaban EFCC.

BBC ta tuntuɓi hukumar EFCC ta bakin mai magana da yawunta Wilson Uwajeren, amma sai ya bai wa wakilinmu Chris Eworkor gajeriyar amsa cikin cunkusasshiyar murya cewa "ba ni da labari."

Sannan da safiyar Talata ɗin wani babban mai taimaka wa gwamnan Kano kan shafukan sada zumunta Abubakar Aminu Ibrahim, ya wallafa wasu hotuna da ke nuna Hajiya Hafsat Ganduje tana saukowa daga jirgi bayan komawarta gida daga Abuja.

Kauce wa Facebook

Babu karin bayanai

Ci gaba da duba FacebookBBC ba za ta dauki alhakin abubuwan da wasu shafukan daban suka wallafa ba.

Karshen labarin da aka sa a Facebook

Goggon Ganduje

Asalin hoton, Abubakar Aminu Ibrahim

Me gwamnatin jihar Kano ta ce?

Kwamishinan yaɗa labarai na jihar Kano Muhammad Garba ya ce wa BBC labarin ba gaskiya ba ne don ko da safiyar Litinin ɗinnan ma ya ga uwargidan gwamnan.

Da aka tambaye shi kan ko ya ganta ne bayan komawarta daga Abujan, sai ya ce "babu yadda za a yi irin wannan abu ya faru a ce bai fito fili ba.

"Ni dai a sanina tana Kano kuma babu wanda ya kama ta," in ji shi.

Ya kara da cewa ko a ranar Talata din ma akwai wani taro da za ta halarta a Kanon kuma za a gan ta.

Garba ya yi kira ga al'umma da su yi watsi da labarin.

Amma hotunan da mai taimaka wa Gwamna Ganduje kan yada labarai ya wallafa a Facebook da ke nuna Hajiya Hafsat ta koma daga Abuja sun kara sa kokwanto kan al'amuran biyu, wato batun kwamishinan cewa "Goggon" ba ta je Abuja ba da kuma hotunan da ke nuna komawar ta Kano.