Ciwon dementia: 'Ƴan Najeriya na cikin wadanda suka fi fama da ciwon mantuwa a duniya’

Wani bincike ya nuna cewa ƴan Najeriya na cikin waɗanda suka fi fama da ciwon mantuwa a duniya.

Ciwon mantuwa da ake kira 'dementia' na ɗaya daga cikin cututukan da ke barazana ga lafiyar bil'adama.

Kungiyar da ta gudanar da binciken mai suna Alzheimer's Disease International ta ce sama da mutum miliyan 40 ke fama da cutar a duniya ba tare da sun sani ba.

Binciken ya kiyasta cewa kashi 75 cikin 100 na ɗauke da cutar ba tare da sun sani ba, kuma wadanan alkaluma sun fi yawa a kasashen Najeriya da Indiya da kashi 90 cikin 100.

Rahoton ya ƙunshi kundin nazari daga manyan masana 50 a faɗin duniya game da cutar.

Shugabar kungiyar, Paolo Barbarino ta ce tsangwama da rashin wayewa da rashin bincike sun taka rawa wajen samun karuwar masu ɗauke da cutar.

Hukumar Lafiya ta WHO ta kiyasta cewa adadin mutanen da ke dauke da cutar a duniya za su haura miliyan 130 kafin shekara ta 2050.

Matsalar rashin gwaji

Binciken ya ce rashin gwajin cutar shi ne babban ƙalubalen da ake fuskanta, inda aka bayyana cewa ya kai kusan kashi 90 cikin 100.

Rahoton ya ce gwaji domin gano cutar na da muhimmanci, tare da ba masu dauke da cutar damar samun kulawar da dace da magani, wanda sun fi tasiri kafin cutar ta yi karfi.

"Labaran boge daga bangaren lafiya, da kuma rashin samun horo a fannin kwararu da karancin kayan aikin gwaje-gwaje, sun taka rawa wajen karuwar da ake samu na gaza iya gano masu dauke da cutar," a cewar Barbarino, wacce ke cikin manyan mambobi a kungiyar da ke taimakawa masu dauke da cutar ta Dementia.

Tsananin yanayi

Barbarino ta ce babban abin damuwarta shi ne yadda gwamnatoci har yanzu ba su shirya shawo kan hasashen da ake yi na karuwar cutar a nan gaba ba. "Babu shaka, ana fuskantar tafiyar hawainiya wajen shawo kan cutar," a cewarta.

Farfesa Serge Gauthier, kwararen likitan kwakwalwa kuma malami a Jami'ar McGill, ya ce yana dakon karban bukatu kan gano cutar", yanayin da zai kasance matsi ga fanin lafiya.

A lokacin mayar da martani kan Rahoton, Richard Oakley, shugaban sashen bincike na kungiyar Alzheimer, ya ce gazawar gano masu dauke da cutar ya bar mutane cikin matsanancin hali da rashin samun goyon-bayan da suke bukata da taimako.

Ya ce: "Karancin bincike domin gano mutum na dauke da cutar babbar matsala ce a duniya, sai dai waɗanan alkalumma na nuna girman matsalolin. Ga wadanda ba a yi bincike domin gano cutar ba, wannan na haifar da gajiyarwa, birkicewa da jefa su cikin yanayi na galabaita wadanda kan kasance sakamakon yanayin da yake ciki.

"Sai dai, a yanzu binciken na da tsada, kuma ba kasafai ake samun inda ake gwajin ba, sannan har yanzu akwai tsangwama kan ambato mutum na dauke da ciwon mantuwa na dementia."

Gwaji cikin dakika biyu

Bincike ya bijiro da wani gwajin kamfuta na dakika biyu da zai iya taimakawa wajen gano ko zaka iya kamuwa da cutar nan da shekaru biyar gaba.

Wannan zai ba mutane damar soma daukan matakai da shan magunguna a kan lokaci.

"Gwajin ya taimaka wajen gano mutanen da ake tunanin za su iya kamuwa da ciwon a shekarun 20 na farkon rayuwarsu, ma'ana akwai manyan damammaki da ka iya taimakawa mutum," a cewar Dr George Stothart, na jami'ar Bath, wanda ya jagoranci binciken.

Alamominta

  • Manta abubuwan da suka faru a baya
  • Wahala wajen mayar da hankali
  • Birkicewa
  • Wahala wajen bin zance
  • Rashin gane lokaci ko wuri
  • Sauye-sauye yanayin mu'amala