Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
An bai wa mata 20 manyan muƙamai na Masallacin Harami a Saudiyya
A wani mataki na sake ƙarfafawa mata gwiwa a Saudiyya, hukumar kula da Masallatai Biyu Masu Daraja ta sanar da naɗin mata 20 a manyan muƙamai na jagoranci.
Mata da ke ɗauke da digiri na biyu da na uku ana ganin wannan wata dama ce da za ta sake nuna daraja da ƙarfafa musu gwiwa wajen kawo sauyi kan harkokin hukumar.
Muƙaman da aka ba su sun haɗa da mataimakiya ga shugabancin hukumar, sakatariyar da mataimakan sakatarori a ɓangarori daban-daban na hukumar.
Shugaban hukumar Sheikh Abdul Rahman Al-Sudais ya ce za a taimaka wa mata wajen sanin makaman aiki da nasara wajen sauke nauyin da ya rayata a wuyansu.
Sheikh Al-Sudais ya umarci a ƙirƙiri sashen da zai ke taimakawa mata ƙarƙashin hukumar a wani ɓangare na tsare-tsaren da ake bijirowa da su na karfafa gwiwar mata a masallatan biyu.
Limamin ya ce matan da aka yi wa wanann naɗin sun nuna bajinta a kowanne ɓangare da aka ba su muƙamai da jagoranci.
Sannan ya ce wannan tsari zai ci gaba da ba da gagarumar gudunmowa a sabbin sauyin da ake fatan ganin ya tabbata a fanin Hajji da Umrah kafin shekara ta 2030.
Waɗannan sabbin sauye-sauye da Saudiyya ke bijirowa da su a kullum yaumin na daga cikin muradan Yarima Salman mai jiran gado wajen zamanartar nda sake ɗaga darajar mata a ƙasar.
A shekarun baya-bayan nan mata na sake samun yanci a fannoni daban-daban wanda babu shaka ke nuna irin sassauci da rangwame da ake musu a wannan zamani.
Ga irin ci gaban da mata suka samu a Saudiyya a shekarun baya-baya nan.=
1. Naɗin mata Jakadu
A watan Afrilun 2021 aka naɗa Bint Ahmed Al-Shahwan a gaban Yarima mai jiran gado Muhammad Bin Salman, a matsayin sabuwar jakadiyar ƙasar a Sweden.
Al-Shahwan ce mace ta uku a cikin matan Saudiyya da aka taɓa naɗawa a matsayin jakadu.
Naɗin nata ya biyo bayan na Gimbiya Reema Bint Bandar Bin Sultan da kuma Amal Bint Yahya Al-Moallimi.
Nade-naden wani bangare ne na shirin Vision 2030 na Masarautar Saudia, da ya ƙunshi ƙarfafa wa matan Saudiyya gwiwa.
2. Shiga aikin soja
A watan Fabarairun wannan shekara ta 2021 aka buɗe wa mata damar shiga aikin soja a Kwalejin Tsaro ta King Fahd da ke Riyadh a Saudiyya.
Jaridar Saudi Gazette ta ƙasar ta ce za a fara karɓar takardun mata masu son shiga aikin soja daga 13 ga Fabrairu zuwa 18 ga Fabrairun wannan shekarar, kamar yadda hukumar da ke kula da harkokin soja ƙarƙashi ma'aikatar harkokin cikin gida ta sanar.
Kwalejin Tsaro ta King Fahd makaranta ce ta koyon aikin soja da ke babban birnin Saudiyya, Riyadh.
Ɗaliban da suka kammala karatu a wannan makaranta na iya samun aiki a bangarorin tsaro da dama na ƙasar.
3. Ɗage haramcin tuƙi ga mata
A watan Satumbar 2018 gwamnatin Saudiyya ta sanar da ɗage haramcin tuki ga mata, kuma tuni aka fara bai wa matan lasisin tukin.
Kafin dage haramcin Saudiyya ta kasance kasa ta karshe a duniya da mata ba su da izinin yin tuƙi.
4. Bikin kafa Saudiyya da ya kawo gwamutsa mata da maza
A karon farko an ba mata damar shiga wani filin wasanni don bikin zagayowar ranar 'yancin kan masarautar Saudiyya.
A watan Satumbar 2017 ne filin wasa na Sarki Fahad a Riyadh babban birnin ƙasar, ya maƙare da ɗaruruwan matan da suka yi ɗango don cin wannan gajiya.
An ga mata a wasu lokuta ma cakuɗe da maza a kan kujeru suna karkaɗa tutocin Saudiyya albarkacin murnar ranar kafa Saudiyya.
5. Kallon 'yan kokawa na Amurka
A karon farko a watan Afrilun 2018 an bai wa mata da maza damar shiga kallon wasan kokawa na Turawan Amurka wato wrestling.
An gudanar da damben kokawar na (WWE) a birnin Jiddah, kuma maza da mata ne suka shiga kallo wanda kafar telebijin din kasar ta nuna kai tsaye.
Maza zalla ne suka fafata a kokawar a Saudiya yayin da aka haramta damben mata a kasar.
6. Shigar mata wajen kallon kwallo
A yanzu ana barin iyalan mutum da suka hada da mata da yara su rinka halartar filayen wasanni da ke manyan biranen kasar uku, wato na Riyadh da Jedda da kuma Dammam.
Wannan sabon mataki dai ya fara aiki ne daga farkon shekarar 2018.
Hakan dai wata 'yar dama ce a masauratar da ake killace mata a gidaje, domin a kara fito da su don shiga a dama da su a cikin al'umma.
7. Tseren keken mata zalla
A watan Afrilun 2018 ne kuma aka gudanar da tseren keken mata na farko a kasar Saudiyya, inda suka bai wa mutane da yawa mamaki a kasar ta masu ra'ayin mazan-jiya, musamman a shafukan sada zumunta.
Karin haske
Kasar Saudiyya dai kasa ce da ta ginu kan al'amuran addini, kuma wadannan sauye-sauyen suna alamta yadda kasar ke sauya wa cikin sauri zuwa ga rayuwar da ake yayi a kasashen Turai.
Sai dai wadannan sauye-sauyen da Yarima mai jiran gado Mohammed bin Salman yake bullowa da su a kasar, na sanya mutane cikin rudani da jawo ce-ce-ku-ce ba a Saudiyyar ba har ma a sauran kasashen musulmi na duniya.
Ana kallon Saudiyya a matsayin wata jagora ta addinin musulunci, shi ya sa a duk lokacin da ta bullo da wani abu da ba a saba gani ba yake darsa shakku a zukatan wasu.