Tsarin USSD: Mene ne USSD, me ya sa bankuna ke caji akansa?

Asalin hoton, Getty Images
Tsarin lambobin da ake amfani da su wurin tura ƙudi a banki a wayoyin salula wato USSD ya ja hankali a Najeriya.
A ranar Talata ne Babban Bankin Najeriya da Ma'aikatar sadarwa a ƙasar suka ɓullo da sabon tsarin haraji ga masu amfani da USSD a cikin wata sanarwa ta haɗin guiwa da suka fitar.
Sanarwar ta ce daga ranar 16 ga watan Maris za a dinga cire N6.98 kan duk mu'amular banki da aka yi ta hanyar tsarin tura lambobin USSD a wayoyin salula.
Wannan na nufin gwamnati ta rage yawan kuɗaɗen da ake cajin kwastamomin banki da suka tura kuɗi ta hanyar lambobin USSD.
Kafin saɓon tsarin, duk kuɗin da mutum ya tura a banki ana cire masa harajin naira N20 zuwa sama.
Mene ne USSD?
USSD tsari ne na mu'amula ta hanyar amfani da wasu lambobi a wayoyin salula.
Kuma USSD lambobin ne da ake amfani da su wurin mu'amula da kamfanin sadarwa ko banki a wayar salula ba tare da wani shamaki ba.
Ko wane banki yana da lambobinsa na USSD da ke ƙarewa da # kuma yawanci lambobin ba su wuce uku ba da ake farawa da * da bankuna suke ba kwastamomi tare haɗin guiwar kamfanonin sadarwa.
Me sanarwar CBN da NCC ta ƙunsa?
Sanarwar ta ce kamfanonin salula da bankuna sun ɗaɗe suna samun saɓani game da tsarin USSD wajen mu'amular kuɗi. Wannan kuma ya haifar da barazanar kamfanonin sadarwa suka yi na janye wa daga tsarin.
USSD hanya ce mai matuƙar muhimmanci wajen mu'amular kuɗi. Don warware taƙaddamar da kuma tabbatar da ingancin tsarin ga kwastamomi, ministan ma'aikatar sadarwa ya jagoranci tattaunawa tsakanin masu ruwa da tsaki domin neman mafiya saboda amfanin jama'a.
Daga ranar 16 ga watan Maris duk mu'amular kuɗi da aka yi ta hanyar USSD a bankuna da CBN - za a caje su kuɗi N6.98, wanda shi ne tsari mai rahusa ga kwastamomi a hada-hadar kuɗi.
Tsarin zai kasance a bayyane kuma zai kasance iri ɗaya ba tare da la'akari da yawan mu'amular da aka yi ba.
Don tabbatar da adalci a tsarin, bankuna ne za su cire kuɗaɗen kai tsaye daga asusun kwastamominsu. Kuma bankuna kada su ɗora wasu ƙarin kuɗaɗe ga kwastamominsu a tsarin na amfani da lambobin USSD.
Bisa wannan matsaya da aka cimma, ba za a toshe wa bankuna tsarin na USSD ba.
Sanarwar ta ce ya kamata jama'a su sani cewa amfani da tsarin USSD zaɓi ne, domin akwai hanytoyi da dama kamar manhajar bankuna a wayoyin salula da kuma injunan cirar kuɗi na ATM da za a iya mu'amular kuɗi.
Me ƴan Najeriya ke cewa?
Sabon tsarin ya haifar da ruɗani a Najeriya. Yawanci ƴan Najeriya ba su fahimci sabon tsarin ba inda suke ta caccakar hukumomin ƙasar.
Da dama sun yi tunanin wani ƙarin haraji ne aka ɓullo da shi baya ga kuɗaɗen da bankuna ke tatsa.
A cewar @Hitee_ Sabon tsarin na CBN kyakkyawar manufa ce ga talakawa amma mutanenmu ba su karatu.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 1
@nifemioluboyede ya ce: Ba kwastamomi ba ne za su biya, bankuna ya kamata su biya kuma bayan sun kasa biya hukumar NCC ta yi barazanar daina amfani da tsarin USSD saboda bashin naira biliyan 42, don ci gaba da tsarin ne ya sa Babban Bankin Najeriya ya ce mutane ne yanzu za su biya.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 2
@victor__okonkwo ya ce: harajin N7 ga USSD, kamar gwamnati na fito na fito ne da yan Najeriya.
@Megamendhie ya ce: Waɗanda suka ƙirƙiro da tsarin ba zai shafe su ba sosai. Gwamnan Babban Bankin Najeriya da ma'aikata da wuya su yi amfani da USSD.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 3
Masana tattalin arziki da hada-hadar kuɗi kamar Yusha'u Aliyu na ganin mataki ne mai kyau gwamnati ta ɗauka saboda yadda tsarin USSD ya samu karɓuwa a Najeriya.
Kuma idan an caji mutane kuɗi domin biyan buƙatar mutane ba wani abu ba ne amma idan za a bambance ta la'akari da yawan kuɗaden da aka tura
Sai dai a cewarsa yawancin ƴan Najeriya ba su fahimci tsarin ba saboda hukumomi ba su yi cikakken bayani ba kan tsarin aiwatar da shi.
Za a ci gaba da cire naira 20 na kwamisho da bankuna ke cire wa a duk kuɗin da aka tura? Ba batun kyauta kenan ga wanda ya tura kuɗi zuwa ga wani mai amfani da bankinsa?











