Boko Haram: Mu muka kai harin Maiduguri - Shekau

Shekau

Asalin hoton, AFP

Kungiyar Boko Haram ta ɗauki alhakin harin da aka kai Maiduguri babbaan jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya da yammacin ranar Talata.

A wani bidiyo da BBC ta gani, wani mutum da ke iƙirarin shi ne shugaban ƙungiyar Abubakar Shekau ya nuna jin dadinsa game da kai harin da ya ce sun samu nasara.

Ba a ga fuskar Abubakar Shekau a zahiri yana magana a cikin bidiyon na minti biyar ba, amma ana iya jin muryar da ke ikirarin shi ne a karkashin bidiyon wasu mutane da ke harba rokoki a cikin wani yanki.

Mai maganar ya nanata irin kyamar da kungiyar ke yi wa ga tsarin ƙasashen yammacin duniya, sannan ya sha alwashin kafa daular musulunci.

A farkon wannan makon wasu makamai suka dira a wata unguwa da ke da yawan jama'a a babban birnin Maiduguri tare da tafka mummunan ta;adi.

Harin ya kasance ɗaya daga cikin munanan hare-hare da aka kai wa birnin a cikin shekara guda.

Jami'ai sun ce mutane goma sun mutu sannan da dama sun samu rauni, amma majiyoyin yankin sun ce adadin wadanda suka mutu yanzu ya kai goma sha shida.

Wannan harin na zuwa ne wata guda bayan da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada sabbin shugabannin tsaro, biyo bayan sukar da gwamnatinsa ke sha game da rashin tsaro.

Hankalin sojojin Najeriya ya rabu

Sojojin Najeriya

Asalin hoton, NDHQ

Yayin da sojojin sama da na ƙasa da wasu dakarun haɗin gwiwa ke ƙoƙarin ƙarasa fatattakar ɓurɓushin 'yan Boko Haram a arewa maso gabashin ƙasar, sai aka fara samun matsalar tsaro a jihar Zamfara inda aka yi ta ba-ta-kashi tsakanin ƴan bindiga da jami'an tsaro.

Ga kuma rikicin ƙabilanci da na makiyaya da manoma a jihar Benue inda hankalin sojoji ya sake karkata a can.

Ba a gama wannan rikici na Zamfara da Benue ba matsalar garkuwa da mutane a arewa maso yammacin ƙasar ta ƙara ƙamari inda masu garkuwa da mutane suka ci gaba da cin karensu babu babbaka a hanyar Kaduna zuwa Abuja da kuma hanyar Birnin Gwari a Kaduna da Kudancin Kaduna da dai sauran wurare na arewa maso yammacin ƙasar.

Ana cikin haka kuma sai jihar Katsina ta ɗauka inda can ma 'yan bindiga da ɓarayin shanu suka addabi sassan jihar wanda yanzu haka ana ci gaba da samun irin wannan matsala a jihar nan da can.

Ta irin waɗannan rikice-rikicen ne ya sa aka raba hankalin sojojin ƙasar musamman na sama da na ƙasa inda ake ta kafa rundunonin haɗin gwiwa da ke aiki a dazuka daban-daban na ƙasar.