Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Rikicin Tigray zai yi wa Sudan illa - UNHCR
Gwamnatin yankin Tigray a arewacin kasar Habasha ta fitar da wata doka da ke umartar dukkan al'ummar yankin da su daura dammarar yaki.
Tashar talabijin mallaki gwamnati ta ce hukumomin yankin sun ba al'uma umarnin daukan dukkan wani mataki na kare kansu daga abin ta kira keta haddi da gwamnatin tarayyar kasar ke yi.
Rahotannin da BBC ke samu daga yankin na Tigray na cewa daruruwan mayaka daga bangarorin biyu ne suka rasa rayukansu a gumurzun da dakarun yankin ke yi da sojojin gwamnatin tarayyar kasar Habasha.
Juliet Stevenson ma'aikaciyar hukumar kula da 'yan gudun hijira ta MDD ce wato UNHCR a Habasha. Ta ce dubban 'yan yankin na tserewa daga Tigray amma abin damuwar shi ne rashin hanyoyin da za a iya kai wa ga al'umomin da rikicin ya rutsa da su domin kai mu su kayayyakin agaji:
"Babu jiragen sama da ka iya sauka a yankin, kuma tun ranar 4 ga watan Nuwamba aka ayyana dokar hana shiga sararin samaniyar kasar - wannan na nufin babu hanyar shigar mutane da kaya cikin yankin."
Ta kuma ce, "Muna bukatar wannan damar domin mu iya kai taimakon gaggawa ga mutanen yankin amma a halin yanzu babu wannan damar."
Sudan na fuskantar barazana daga rikicin Tigray
A wani bangaren, wannan rikicin ya tilastawa 'yan Habasha a kalla 11,000 tsere wa zuwa Sudan mai makwabtaka da yankin.
Jami'an gwamnatin Sudan sun ce suna sa ran dubban mutane za su ci gaba da kwarara zuwa Sudan cikin kwanaki masu zuwa.
Tun kafin wannan rikicin ya kazance haka, kusan mutum miliyan daya ne ke dogara da taimakon da hukumar UNHCR ke samarwa a yankin Tigray, kma idan rikicin ya ci gaba na wani lokaci mai tsawo, 'yan gudun hijira 10,000 da ke yankin na iya rubanyawa sau biyar kafin karshen wannan shekarar - matakin da ka iya sa Sudan ma cikin wani mawuyacin hali.