Biden ya sha alwashin kawo ƙarshen 'baƙin mulkin Trump'

Former U.S. Vice President Joe Biden accepts the 2020 Democratic presidential nomination during a speech

Asalin hoton, Reuters

Dan takarar mukamain shugaban kasa a karkashin jam'iyyar Democrat, Joe Biden ya bayyana matakan da zai dauka idan Amurkawa suka zabe shi a watan Nuwamba mai zuwa.

Mista Biden ya bayyana haka ne a rana ta ƙarshe yayin babban taron jam'iyyar, kuma cikin jawabin da yayi daga garinsu na Wilmington, a jihar Delaware, ya ce abokin hamayyarsa Shugaba Trump ya shuka fushi da tsoro da rarrabwar kawuan a tsakanin 'yan kasar.

Mista Biden ya kuma ce Shugaba Trump ya "saka Amurka cikin baƙin duhu na lokaci mai tsawo."

Saura kwana 75 a kada kuri'ar kuma Mista Biden ne ke kan gaban Mista Trump a kuri'ar raba gardama, kamar yadda za kuji cikin rahoton da Sani Aliyu ya hada mana.

Yayin da yake jawabinsa a rana ta karshe na babban taron Jam'iyyar Democrat, dan takarar ya bayyana wasu daga cikin matakan da zai dauka idan Amurkawa suka zabe shi a watan Nuwamba mai zuwa, musamman ya soki yadda Shugaba Trump ya ke tafiyar da aikin dakile annobar korona kuma ya bayyana matakan da shi zai dauka domin kawo karshen annobar:

Mu ke kan gaba a yawan wadanda suka kamu da cutar korona, mu ke kan gaba a yawan wadanda suka mutu. Tattalin arzikinmu ya yi kaca-kaca, ga Amurkawa da suka kasance bakar fata da latino da 'yan Asiya da 'yan Amurka na asali wadanda su ne suka fi shan wahala.

Ya kara da cewa: "Kuma bayan wannan lokaci, shugaban kasar nan ya kasance ba shi da wani shirin magance matsalar. To ni a shirye na ke."

Democratic presidential candidate and former Vice President Joe Biden, his wife Jill Biden, U.S. Senator and Democratic candidate for Vice President Kamala Harris and her husband Douglas Emhoff celebrate after Joe Biden accepted the 2020 Democratic presidential nomination

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Mista Biden tare da matarsa Jill da mataimakiyarsa Kamala Harris da mijinta Doug Emhoff

Ya yi alkawari kamar haka: "Idan na zama shugabanku, daga ranar farko za mu aiwatar da wani shiri a fadin kasar nan, shirin da tun watan Maris nake shimfidawa. Za mu fara gwaje-gwaje cikin hanzari, kuma mu samar da sakamako cikin hanzari."

"Za mu samar da kayan aiki da magunguna da kasarmu ke bukata, inda za mu hada su a nan Amurka domin kada mu kara zama ba mu da mafita sai yadda China ta yi da mu ko sai yaddda sauran kasashe suka yi da mu domin kare lafiyar mutanenmu," inji Mista Biden.

Mista Biden ya kuma ce "Shugabanmu mai ci ya gaza a wannan aiki da kasarmu ta damka ma sa amana. Ya gaza kare mu, ya gaza kare Amurka, kuma wannan ba abu ne da za a iya yafe wa ba ya ku 'yan uwanan Amurkawa. Idan na zama shugabanku, zan sha alwashi guda. Zan kare Amurka, zan kare mu daga ko wane irin hari, bayannanen hari ko boyayye, kuma a ko yaushe, ba tare da zabi ba, a ko yaushe."

Mista Biden ya kuma taba wasu batutuwa masu yawa, ciki har da na hadin kai tsakanin Amurka da kawayenta.

Ya ce zai kuma nuna wa magautan Amurka cewa Amurka ba za ta sake rungumar shugabannin da ke take hakkin 'yan kasarsu ba.

Musamman ya bayyana abin da ya ce Amurka ba za ta sake kyale Rasha ta rika farautar sojojinta kamar yadda ta ke yi a yanzu ba. Ya kuma ce ba zai kyale wasu kasashe su ci gaba da yin katsalandan a zabukan kasar ba.