Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ranar June 12: Jawabin Buhari ya bar baya da kura
Ana ci gaba da mayar da martani game da jawabin ranar dimokradiyya da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi, inda wata gamayyar kungiyoyin arewacin kasar ta Coalition of Northern Groups ta fito ta soki ikirarin da shugaban ya yi na samun nasara musamman a bangaren tsaro.
Shugaban kwamitin amintattu na kungiyar Ashiru Shariff, ya shaida wa BBC cewa halin tabarbarewar tsaro da yankin arewacin Najeriya ya tsinci kansa a ciki shine mafi muni da aka taba gani.
Ya ce matsalolin da yankin yake fama da su na da nasaba da rashin shugabanci nagari tunda "Dalilin da ya sa aka kawo gwamnatin nan ta APC (a) 2015 don ta yaki rashin tsaro a arewacin Najeriya ne, amma sai gashi harkar tsaron an kasa komai a kanta kullum sai gaba take tana tabarbarewa,"
"Da 'yan Boko Haram ne kawai, yanzu an samu karin masu kwacen shanu da dabbobin mutane, 'yan bindiga masu kashe mutane sannan ga masu satar mutane duka a arewacin Najeriya."In ji Ashiru.
Ashiru Shariff ya kara da cewa ko a gwamnatocin baya, ba a fuskanci irin wannan lalacewar al'amura ba ta fuskar tsaro dama tattalin arzikin kasa wanda ya ce shi ne dalilin da ya sa suke ganin nasu tsarin ya fi na sauran gwamnatoci lalacewa.
Ya ce bai ga dalilin da zai sa shugaba Buhari ya fito ya yi jawabi ga 'yan kasa da sunan murnar ranar dimokradiyya ba saboda yadda mutane da dama suka rasa rayukansu sanadin hare-haren da 'yan bindiga suka kai yankin na arewa a baya-bayan nan.
A cewarsa hanyar da ya kamata a bi wajen kawo maslaha shi ne mutane su jajirce su "Nemawa kansu 'yanci domin wannan gwamnatin ba ta da niyya ko kwarewar da zata kawo musu karshen wannan abun tun da yau shekara nawa ana abu guda."
Ya ce, "Mene amfanin dimokradiyyar da za a kawo ta ba kwanciyar hankali, babu nutsuwa a wajen mutane, babu walwala ta tattalin arziki a cikin kasa kuzo kuce kuna murnar dimokradiyya?."
A ganinsa, kamata ya yi shugaba Buhari ya fito ya ce "Ba bu maganar murna, muna yin jaje da ta'aziyyar mutane da aka rasa rayukansu a wannan sati kadai a Najeriya."
Ya ce lokaci ya yi da mutane ya kamata su nemi gwamnati ta kawo karshen matsalolin sannan su yi kira ga shugaban "Idan har shi shugaban kasar nan ya san ba zai iya wannan aikin ba ya kamata ya dena wahalar da mu yana wahalar da kasarnan,"
"Amma wannan tsarin da ya dauka ba zai yiwu ba, tunda shi a lokacin Jonathan abin da ya yi kenan da kansa ya fito ya ce Jonathan ya yi (murabus) tun da ya kasa kawo tsaro, toh shi yanzu ya gwada a kansa ya tabbatar da cewa shi abin da ya fada a baya da gaske yake." kamar yadda Ashiru Shariff ya fada.