Wane ne gwamnan Filato Simon Lalong?

Asalin hoton, @SIMONLALONG
A karo na farko tun bayan da aka gudanar da zaben gwamna na ranar 9 ga watan Maris din bara a Jihar Filato, Simon Bako Lalong zai ji kamar an sakar masa mara.
A lokacin zaben dai Hukumar Zabe ta Kasa a Najeriya ta bayyana cewa ba a san wanda ya yi nasara ba tsakaninsa da babban mai adawa da shi, Jeremiah Useni na Jam'iyyar PDP.
Bayan gudanar da zabe a wasu rumfunan zabe na jihar, an ayyana shi a matsayin wanda ya yi nasara, amma da karamin rinjaye, kuma kafin ya numfasa abokin hamayyar tasa ya garzaya Kotun Sauraron Kararrakin Zabe.
Sai dai mai yiwuwa a matsayin shi na lauya fadi-tashin da ya yi daga wannan kotu, zuwa Kotun Daukaka Kara, har zuwa Kotun Koli ba bakon abu ba ne a wurin shi.
Aikin Lauya
Mista Lalong dai ya fara aikin lauya ne a 1992, shekara guda bayan ya kammala karatu a Makarantar Koyon Aikin Lauya ta Nigeria da ke Legas, da kuma Jami'ar Ahmadu ta Zaria (inda ya yi digirinsa na farko a aikin lauya), wacce ya kammala a 1990.
Ya kuma yi karatun digiri na biyu, shi ma a aikin na lauya, a Jami'ar Jos, wacce ya gama a 1996.
Kafin ya tsunduma harkar siyasa a 1998 dai ya yi aiki a ofisoshin lauyoyi daban-daban, ciki har da wanda ya hada gwiwa don kafawa, wato Simon B. Lalong and Co.

Asalin hoton, Makut Simon Macham
Harkar Siyasa
A daidai wannan lokaci da Najeriya ke komawa kan turbar dimokuradiyya bayan shekara da shekaru na mulkin soji, Mista Lalong ya yi takara ya kuma yi nasarar lashe zabe don wakiltar mazabarsa ta Shendam a Majalisar Dokoki ta Jihar Filato a karakshin tutar jam'iyyar PDP.
A shekarar 2000 kuma ya karbi shugabancin majalisar bayan wata turka-turka da ta yi awon gaba da rawanin shugabanta mai ci a wancan lokacin; ya kuma rike mukamin har zuwa 2006.
Yayin da zabukan 2015 suka karato, Mista Lalong ya shiga sahun masu sha'awar maye gurbin Gwamna Jonah David Jang, amma ganin cewa ba zai cimma wannan muradi a karkashin jam'iyyarsa ta PDP ba, ya sauya sheka zuwa jam'iyyar APC.

Asalin hoton, Getty Images
Wa'adi na Farko
A ranar 29 ga watan Mayun 2015 aka rantsar da shi a matsayin gwamnan jihar Filato a karo na farko.
Masu suka dai sun sha zargin Gwamna Lalong da gazawa wajen samar da romon dimokuradiyya ga al'ummar Jihar Filato, da ma kasa cika alkawuran da ya dauka a lokacin yakin neman zabe.
Musamman, tawagar yakin neman zaben babban abokin hamayyarsa a 2019, Janar Useni mai ritaya, ta zargi Mista Lalong da gazawa wajen kawo karshen kashe-kashe da hare-haren da aka rika kaiwa a kan wasu al'ummun jihar—hare-haren da ake zargin makiyaya da kaiwa.
Sai dai magoya bayan Gwamna Lalong sun nuna cewa a shekara fiye da goma ba a samu zaman lafiya a jihar kamar yadda aka samu a zamaninsa ba.
Sun kuma bayyana cewa salon mulkin Mista Lalong na tabbatar da adalci da kuma tafiya da kowa ya taimaka wajen samar da zaman lafiyar.
Ra'ayin Masana
Masu sharhi a kan al'amuran yau da kullum a Jihar ta Filato dai na ganin wannan nasara da Mista Lalong ya yi a Kotun Koli dama ce ta dawo da dawwamammen zaman lafiya.
A cewar Muhammad Lawal Is'haq, wani lauya mai zaman kansa a Jos, babban birnin Jihar, "A yanzu ba shi da sauran dalilin jan kafa a yunkurinsa na dawo da martabar Jihar Filato a matsayinta na cibiyar zaman lafiya da yawon bude ido.
"Ga shi kuma an dora masa karin nauyin tabbatar da hadin kan Arewa a matsayinsa na Shugaban Kungiyar Gwamnonin Jihohin Arewa, saboda a yanzu ne aka fi bukatar hadin kan al'ummomin Arewa fiye da ko wanne lokaci, bisa la'akari da dimbin kalubalen tsaro da yankin ke fuskanta".











