Gazawar Gwamna Matawalle ta fara bayyana a Zamfara – Yari

Tsohon gwamna Abdulaziz Yari na Zamfara
Bayanan hoto, Abdulaziz Yari

Bangaren tsohon gwamnan jihar Zamfara AbdulAzizi Yari Abubakar ya maida martani game da zargin haddasa tashin hankali da gwamna mai ci a jihar Bello Matawalle ya yi masa.

Martanin ya fito ne daga bakin Ibrahim Dan malikin Gidan Goga, wanda daya ne daga cikin mamboban kwamitin hulda da 'yan jarida na jami'iyyar APC a jihar ta Zamfara.

A taron manema labarai, Ibrahim Dan Maliki ya bayyana zarge zargen da gwamnan ya yi a hirarsa da sashin Hausa na BBC a matsayin marasa tushe, kuma a cewarsa gwamnan kame-kame ne yake yi saboda gazawa.

A ranar Juma'a ne gwamnan jihar Bello Muhammad Matawalle ya zargi tsohon gwamnan da hada baki da 'yan ta'adda don yi wa shirin zaman lafiyar da ya samar zagon kasa.

To sai dai bangaren tsohon gwamnan ya kalubalanci gwamna Matawalle da ya fadi daya daga cikin hare-haren da aka kitsa a lokacin da AbdulAziz Yari ke cikin jihar.

Kwamitin ya ce tsohon gwamnan bai taba zuwa wata karamar hukuma ba a jihar in ban da mahaifarsa Talatar Mafara tun bayan saukarsa daga mulki.

Haka ma ya ce rashin amsa gayyatar da kwamitin bincike kan matsalar tsaro ya yi wa tsohon gwamnan na da nasaba da jan kunnen da Gwamna Matawalle ya yi masa na ya cire hannunsa kan duk wani abu da ya shafi tsaro a jihar.